Babi Na Sha Shida

4.1K 333 36
                                    

Assalamu alaikum. Oh, am I glad to meet here again. Okay, I haven’t really been myself, so the last two updates were not as I wanted them. There were blunders and typo errors all over.

But for your love and understanding, you all overlooked them, thank you so much for the overwhelming support and love. May Allah reward you.

Gaban Asiya ya fadi. Wace ce kuma wannan matar? Wace ce jikanyar ta ta? Me ye gamin ta da Yusuf, ko kuma shi din da wata jikanyarta?

“Ina yini Yafendo.” Yusuf ya furta ga wannan mata cikin muryar da ke nuna ya na kokarin danne zuciyar sa.

Ta katse shi tare da daga ma sa hannu, idanunta na ci da wuta, ta ce, “Ba gaisuwar ka na ke bukata ba Dan-auta, so nake ka bani jika ta. Domin Khalid ba mutuwa yayi ba da ransa. Kuma ni ce na dace na yi renon ‘yar sa, ba kai ba. Don haka ka bani ita yanzu na yi tafiya ta, idan kana son a zauna lafiya. In kuwa ba haka ba, to lallai za ka ga abin da zai ba ka mamaki, har tashin duniya.”

Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un! Me Asiya ke ji kuma? Wai da ma wannan din ta zo ne a bata Amatullah? Ya salam! Amatullah? Rana tsaka? Zuciyar ta ta kara bugawa, ta kalli Yusuf. Bai kale ta ba. Idanun sa a kan wacce ya kira da Yafendo ne, fuskar sa a natse. Ko dai ba a dakin da suke ciki yak e ba, ko kuma yak ware wajen boye sirri.

Cikin natsuwa, ya ce, “Ba zan iya bayarwa ba. Ba na kuma tsoron abin da za ki yi.”

Ba ta nuna alamar amsar sa ta girgiza ta, ko ta ba ta mamaki ba. Daure fuskar ta ta kara yi, sannan ta ce, “Oh, haka ka ce ko? To duk duniya ba bu wurin da a ka taba rikon diya na dole, muddin da dangin ta na kusa.”

Ta kalli saurayin da suke tare, ta ci gaba da cewa, “Kai da na dauko ka don ka karbi ‘yarka ka tsaya ka na ji na kamar rediyo?”

Ta dan ingiza Khalid gaba zuwa wajen da Yusuf din ke tsaye, “Ga Khalid, a ba shi diyarsa, mu tafi.” Furucin umarni ne.

Bai ce komai ba har a lokacin. Ta sako shi gaba kamar wani yaro dan shekara goma, ko kuma wanda a ka buga a makaranta mahaifiyar sa ta je kwatar ma sa fada. Ta kalli Yusuf, Idanun Asiya su ka tsaya kan saurayin nan, Khalid.

Ta kura ma sa idanu, ta ji wani irin bacin rai ya shige ta, duk da rudanin da suka samu kan su ciki. Wannan shi ne ya jefa Mariya cikin ukuba, wanda ya yaudare ta, har ma yayi sanadin bata wa gidan su suna. Wannan shine azzalumi, maci amana. Shin ina ya shiga ne tun tsawon lokacin nan?

Yusuf ya kalli Asiya, karo na farko ta ga ya nuna ma ta alama a cikin kwayar idanun sa. So ya ke yi ta yarda da shi, ta nuna ma sa fahimta. Ta ji zuciyar ta ta yi zogi.

Ta san auren su ba mai dadewa ba ne, amma ta fara samun gargadar da tilas zai bukaci ta tsaya tare da shi don su fuskanta tare. Balle ma, wannan barazana ce ga Amatullah, wacce dukan su biyun suka yi alwashin tsarewa da karfin ikon da Allah Ya ba su.

Nan take ta ji bukatar ta kasance tare da Aman, don ta rungume ta a jikin ta. Kafin ta motsa, ta ji Yusuf ya ce da Yafendo, “Kamar yadda na ce ne, ba zan bayar da Amatullah ba. Ba na kuma tsoron abin da za ki yi, tun da ba zai yi tasiri a kanmu ba da ikon Allah.”

Idanun Yafendo suka canja kala, muryar ta na amon wuta, ta ce, “Ka yi furucin a hankali Dan-auta, don da sannu zan sa ka zuba su a kwano, ka cinye su daya bayan daya.”

Ya yi murmushi, “Tun da na kira Allah to na gama komai.’’

“To ka sani cewa zan dawo ko ka na so, ko ba ka so dole ka mallaka mini ita. Ka sanar da uwar taka, cewa na fi karfin ta. Ta fita daga hanya ta, ko kuwa na gama da ita. Don kuwa ba ta kare ba tsakanin mu.’’

Bai kara ce da ita komai ba, ya juya zuwa ga bakin su, “Don Allah ku koma ku zauna ma na. Ku yi hakuri…”

Yafendo ta sake katse shi, “Lallai Dan auta, an ce yaro bai san wuta ba sai ya taka. Da sannu zan gwada mu ku cewa masallacin kura ko da kudi ne, kare ba zai shiga ba!”

KudiriWhere stories live. Discover now