Babi Na Ashirin Da Biyar

3.8K 324 99
                                    

Diib, wuta ta dauke ma ta na dakika biyu. Ta ji kamar da wani harshe Yusuf ya ke ma ta magana. “Maree? ‘Yar uwata Mariya?”

Ta san dai ba zai ma ta wasa a kan hakan ba. Sannan ba zai taba fada mat aba idan har bai tabbatar da abin da yak e fad aba. Shi yasa wata kila wancan karon bai sanar da ita a kan an gan ta a Jos ba.

Ta kura ma sa idanu, zuciyar ta na bugu, ta na son jin ya maimaita furucin na sa. Wata kila zagin kunne ne tun farko.

“Eh, ita.”

Ba ya taimakawa da amsar nan da ya bayar. So ta ke yi a muntsine ta, ko wani ya cije ta ko za a samu a cikin mafarki ta ke ba, ba zahiri ba. Ta dade da son jin wannan labarin da a yau kuma ba ta tabbatar da yadda ta ke ji ba da ta samu.

Hakan ya na nasaba ne da cewar ta fidda ran ta a kan bullowar Mareen ne. ko kuma zuwan da ta yi kwatsam a yau ya jijjiga ta ne ta yadda tunanin ta ya birkice.

“A ina a ka same ta? Yaushe kuma? Ta na cikin koshin lafiya?”

Ba fata ba ne, amma wannan tunanin za a iya samun Maree cikin halin rashin lafiya ko tagayyara ya gifta cikin tunanin ta lokaci-lokaci.

Ya dan yi murmushi, “Ai kya bari na amsa daya bayan daya dai ko.”

Ta gagara yin ko da murmushin don muddin ba ta ji amsar ta ba, ba za ta sake ba. Wayyo Dada, yau wane irin hali za ta kasance a ciki? Addu’o’in su sun samu karbuwa a wajen Allah.

“A Kaduna a ka same ta. Ta na kuma cikin koshin lafiya.”

“Alhamdulillah! Allah mun gode maka.” Ta furta, ta re da zukar numfashi ta fitar. Idanunta suka ciko da kwalla, ba ta san ko na me ye ba ne. A yau kusan shekara guda ke nan da bace mu su, ko waiwayen sub a ta yi ba. Sau nawa ta sha tunanin Maree cikin wani mummunar yanayi, cikin fargaba da zullumi.

Sai ga shi a lokacin da ba ta tsammani ba zato, an samu ‘yar uwar ta, mahaifiyar Amatullah. Amma mece ce matsalar da ya ce an samu?

“Amma me ye matsalar dazun?”har a lokacin gani take yi za ta farka daga mafarkin da ba ta kwanta barcin sa ba.

Ya sake nisawa, idanun sa na bayyana bacin rai, da bakin ciki. Ya ce, “Ina son ki san cewa duk abin da ya samu bawa, to daga Allah ne. Sai ki yi hakuri, domin Yafendo ta dawo. A yanzu haka tan a falo.”

“Yafendo? Me Yafendo za ta iya yi, musamman a yanzu ma da a ka samu Mariya?”

Ya yi ma ta kallon ba ta fahimce shi ba, ya amsa, “Yafendo ta zo ne tare da Mariya. Ya lura da gwalo idanun da ta yi, sannan ya sauke muryar sa sosai.

“Mariya ta na bukatar a ba ta Amatullah, diyar ta.”

Iya abin da ta iya ji ke nan. Bayan nan sai karar bugun zuciyar ta, wadda ta yi rugu-rugu...

                      *             *             *

Wuri ya yi tsit, ko ina ya yi shiru. Wurin da ke cike da hayaniyar jama’a a dazu ya zama tamkar makabarta, in an dauke karar iyakwandishan, da wasu na’urorin lantarki na sanyaya rayuwar dan Adam.

Asiya ta kura wa ‘yar uwar ta Mariya idanu cike da kwalla. Shekara guda ke nan da idanun su ba su hadu ba. Ya dace a ce sun rugumi juna ne cikin farin ciki da tsalle. Amma kuma in ban da kwalla, babu abin da ke gudana cikin idanun Asiya.

Kusan za a ce ba ta gane ta ba, domin Mariya ta rame. Ta kara bakin fata, har cikin idanun ta na bayyana kunci da wahala, da ma rashin abinci mai inganci. Atamfa ce ke jikin ta, irin roba-robar nan, dinkin riga da siket. Wuyan dinkin rigar sai faduwa ta ke yi daga kafadar ta. Wani irin tsami ke bayyana rashin samun kula jiki ta bangaren ta.

KudiriWhere stories live. Discover now