Babi Na Sha Biyu

4.1K 293 101
                                    

“Assalamu alaikum.”

Wata mace kyakkyawa da ita, fara sol mai kyaun sura da sutura ta shiga dakin. Ta matsa dab da su cikin fara’a. ga ta da kyaun diri, tana ta kamshin dadi. Hakan ya sa Asiya jin kaskanci da karanta.

“Amarsu ta ango, mai dadin tuwo. Lallai na taki sa’ar kasancewar wadda ta fara ganin fuskar ki.”

Asiya tayi murmushi. Irin shigar da wacce ke gaban ta , idan an gan su za a yi zaton it ace amaryar. Irin su ne suka dace da auren maza irin su Dokta. Ba irin ta ba. Komai nata ya na nuni ga ajin ta da kwarjini ba tare da nuna rawan kan ta ba.

“Sunana Sara. Ina fata nan gaba ni da ke zamu saba sosai. A halin yanzu, so nake na ji ko da wani abin da kike bukata?”

Asiya ta amsa, “Babu komai.” Alhali so take yi ta tambaye ta Amatullah. Bakin ta ne ya mata nauyi.

Bai kyautu ta rika nuna wa mutane dalilin amincewa da wannan auren ba. Kawai dai ita ke bukatar tuna wa kanta hakan, musamman idan ta ji rudani ya sauka mata. Ganin Sara ne ya kara ankarar da ita cewa ruwa ba sa’ar Kwando ba ne, linzami kuma ya fi karfin bakin kaza.

“Kin tabbata?” hakorin Makkan ya bayyana cikin jerin fararen hakoranta farare fat, masu kyaun tsari.

Asiya ta gyada kan ta, “Na tabbata.”

Sara ta ce ta na zuwa, sannan ta fita daga dakin. Ta ji Muhibbat ta riga ta furta abin da ke zuciyar ta, “To ita kuma wannan wace ce?”

Ita ma bata da amsa. Tunanin ta, idan har Dokta ya na ganin ire-iren su Sara, to lallai ba zai ma kalle ta a matsayin komai ba. Ta san ya zabe ta ne don ita ce kanwar Maree, uwa daya uba daya. Ba don hakan ba, ko kallo ba za ta ishe shi ba.

Sara ta dawo, ta na tura wani abin ajiye kooler na abinci wanda ta jera wa kuloli manya guda uku, filet filet da kaofuna. Sannan a gefen su kuma da ruwan sha masu kala da bakin ruwa.

Ta ce da Asiya, “Amarsu ta Ango, ga wannan na kawo miki. Na san ba ki wani ci abinci ba dazu. Kar Yayana ya zo ya ce na bar ki da yunwa.”

“Yayan ki?” Muhibbat tambaya.

Sara ta yi murmushi mai fadi, “Ni kanwar ango ce, wacce ya dora wa nauyin kula da ke a wannan lokaci. Ba zan so yaga gazawa ta ba.”

Sanyi ta ji ya sauka Asiya, ba ta san dalili ba. Wato dai ashe kanwar sa ce. To amma bata fayyace yadda suke ba. Uwar su daya uba daya, ko ‘yar kawu da dan gwaggo ne? Shin duk zuri’ar su kamar Sara su ke? Yusuf kyakkyawa ne, haka nan ma Khalid.

Wai ma shin ina Khalid ya ke ne? Bai kamata bane a ce ya bayyana kan sa ko don saboda Amatullah? Me yasa bai taba zuwa ziyartar su a asibiti ko sau daya ba? Hakan ya nu na ba ya son Amatullah ke nan, ko kuma bai san dai ta ba. Hakika tun farkon faruwar al’amarin nan Allah bai sa ta yi ido biyu sa shi ba. Ko me ye dalili?

Bayan Sara ta tafi, Muhibbat ta bude kwano daya, kamshin fefesun kaji ya buso hancin ta. Ta shaka sosai, sannan ta ce, “Oh, garin dadi ya na nesa, ungulu ta leka shadda.”

Ta dauki filet daya, ta fara zuba wa. Ba ta damu da duba sauran abin da ke wadancan kwanukan ba. Asiya ta ce, “Muhi, me ki ke shirin yi? Duk abincin da ki ka ci har ki na da wajen zuba wannan?”

Muhibbat ta finciki cinya, ta ce, “Yarinya, zubi in dai ba na adashen kudi ba ne babu matsala. Balle ma, me ye na ci? Kawai shinkafa ce dafa-duka, sai salak, soyayyen nama da ferfesun kifi. Ban sha ferfesun kaji ba ai.”

Asiya ta rike baki, sannan ta ce, “Tab! Yau a bandaki za ki yi shimfidi ki kwanta. Wannan irin hadin duk a cikin ki ke kadai?”

Muhibbat ta tsotsi kashin cinyar da ta dauka, “Kin san ba zan bari a riga ni ba da labari ba. Don haka komai sai na ci a yau din nan.”

KudiriWhere stories live. Discover now