Babi Na Talatin Da Daya

3.5K 268 38
                                    

Ya durkusa a kan gwiwowin sa duka biyu a gaban ta, idanun sa da rauni, muryar sa dauke da nadama. Nan take zuciyar ta ta shiga zogi da tsananin rudani.

“Asiya, na rantse da Mahallicin mu, babu abin da ya taba shiga tsakanina da Mariya ‘yar uwar ki. Wallahi, ban taba kallon ta ta wannan sigar ba. Ban taba cin amanar auren mu ba. Amma duk da haka, na amince, na karbi hukuncin da ki ka yi min, wanda ya kasance mai tsauri matuka. Na yi hakan ne, don ki samu sanyi cikin ranki, tare fatan cewa idan har hakan ya samu, za ki huce har ma ki saurare ni.”

Ya ja tafin hannun ta ya rungume cikin na sa, ya kara sauke muryar sa, “Asiya, ki tausaya wa rayuwa ta, kar ki jefa ni cikin ukuba bayan kin dandana min dadi tun farko.

Tun faruwar wannan abu, gidan nan ya zama tamkar daji a gare ni; babu haske, babu tsaro. Kin kaurace wa yi min murmushi balle dariya. Na bar ganin kauna cikin kwayar idanun ki. Don haka na ke neman gafarar ki. Please ki yafe min, ki bar azabtar da zuciyata haka nan.”

Asiya ta fadi kasa tare da baje hannayen ta, ta rungumi mijin ta cikin kuka mai ratsa zuciya, “Na shiga uku, na saka mijina kuka tare da cusa ma sa bakin ciki.”

Shi ma ya kara rungumar ta ga-gam, sai ajiyar zuciya kawai yake yi. Ta ci gaba da cewa, “Ka yafe min mijina, ko zan yi dace da rahamar Allah. Idan na tarar da Ubangiji na cikin wannan hali, kaicona!”

Da gaske ta ke jin ta shige su. Zuciyar ta ta matukar sosuwa, ganin yadda ya saukar da kan sa, ya amsa laifin da bai aikata ba, don kawai su yi sulhu.

Yadda Yusuf ya rufa ma ta asiri, ita da ‘yar uwar ta da iyayen ta bai dace a ce ya shiga kunci ta hanyar su ba. Ta taba jin an ce mutum ya fi bata rai wa wanda ya fi son shi. Ma’ana dai, kishin sa ne ya rufe idanun ta, har ya kai su ga halin da ta jefa su ciki.

Ba taba soyayya ba sai a kan sa. Don haka ba ta san yadda za ta shawo zuciyar ta a kan kishin da ta taso gare ta ba a kan sa. Garin neman bayani, ta soki zuciyar sa, ta so tarwatsa ginin rayuwar da suka fara shimfidawa.

Yusuf ya ja daga jikinta, sannan ya shiga share hawayen ta da hannun sa. “Ki bar kuka my dear, domin har ga Allah, na yafe mi ki duniya da lahira. Ban karaya ba, daga rahamar Allah. Kamar yadda Ya mallaka min ke cikin ta, Ya kuma bani tagwaye. Hakika, na yi alkawarin rike ku tsakani na da Shi duk wuya duk rintsi.”

Hawaye ya ci gaba da zuba daga idanun ta. Ya y aba za ta yi kuka ba? ta na ji da gani ta saka kafa ta na neman fatali da farin cikin ta, hanyar aljannar ta? Ta tausaya wa kan ta, da ma shi gaba daya. Dole ta gyara, tun ba ta shiga bone ba.

Ya ci gaba da share hawayen ta, “Kukan ki masifa ce gareni, ki daure ki tsagaita haka don Allah.”

Ta kai na ta hannun ita ma, ta na goge fuskar ta sa cikin tsananin jimami da nadama, “Na bar kukan. Ka yafe min, ba zan sake yarda shakka ta shiga tsakanin mu ba. Wata kila na makara da furtawa, amma so nake na kara jadadda cewa na yarda da kai, dari bisa dari.”

Ya dan sumbace ta, gaba daya jijiyoyin jikin ta suka mace, ya saki murmushi, “No, ba ki makara ba. So na ke na ji wadannan kalamai daga gare ki. Sun fi min komai a duniya.”

Ya ja ta a hankali ya sake rungume ta. Iska mai ni’ima, wadda suka dade ba su ji irin ta ba ta gewaye su. Karar bugun zuciyar sa take ji, wadda ta yi daidai da yadda tata zuciyar ke yi. Ta lumshe idanun ta, ta ji ajiyar zuciya.

Wannan mutum, wanda ya dandana ma ta farin ciki ya na rike da ita a lokacin da ta kawo ma sa bacin rai ta dalilin da baya da tushe. Mariya ce ‘yar uwar ta, amma ba ta taba haddasa ma ta komai ba sai bakin ciki.

Ta yi nadamar wautar ta, da yarintar ta. Don me ta bari har Mariya ta ci galaba a kan ta? Me yasa, duk da sanin halayen ta, ta bar ta tayi tasiri a kan ta?

KudiriWhere stories live. Discover now