Babi Na Goma

4.7K 327 87
                                    

Asiya ta fito daga bandakin, fuskar ta cike da rudani, ta ce wa Dada, "Ashe ba ta ciki?"

Dada ta shiga jijjiga jaririyar, ta na kallon Asiya kamar wata sabuwar tababbiya, "Kamar ya ya ba ta ciki? Ba tun dazu kin ce ita ki ke jira ba?"

"Eh, na dauka ta na ciki ne. bari na je na duba waje ko nan ta yi."

Ba tare da bata lokaci ba ta bude kofar dakin ta fita, zuciyar ta na tsalle don fargaba, kan ta na juyi.kai tsaye ta nufi bakin wajen ma su karbar baki, wato reception, ta tambayi Nas din ko Allah Ya sa ta ga Maree?

"Na dan yi barci kam gaskiya tun wajen sha daya na dare, kasancewar ayyukan sun ragu. To amma kofofin nan duka a kulle su ke. Ba na tsammanin akwai wadan da za su shiga, ko fit aba tare da sani na ba."

Asiya ba ta san ko godiya za ta yi ba, ko nuna jin dadi. Ko ma ta shiga kwala kira wa Maree ba. Idan ko ina a rufe ne, to ina ta shiga ke nan? Dakuna goma ne a jere, biyar suna fuskantar biyra, kuma kowanne da lamba a saman sa. dan bakin kofar dakunan bay a da fadi sosai, sai dai tsawo har ya kai zuwa wajen karbar bakin. Ta gangara daga farko har karshen sa, ta na dube dube.

A wannan lokaci ne wata mai tallafa wa Nas a asibitin, wato attendant mai suna Binta ta shiga farfagiyar, ta na mitar sake barin kofar fita ta baya, don yawan fadar da shuwagabannin su suke yi kan hakan. Musamman cikin dare, saboda tsaro. Nas ta tabbatar wa Binta cewar da hannun ta ta rufe kofar kafin ta kwanta.

"Watakila sister Sala ce ta bude daga baya ta fita, na san ita ke yawan yin hakan idan tana aiki."

Sister Sala ta yi motsi a cikin barcin da take yi a kan katifar da ke shimfide a kasa. Sai a lokacin Asiya ta lura da ita tuntuni. "Eh na fita dazu, bayan na dawo daga dakunan marasa lafiya. Lokacin da zan dawo ciki na hadu da wannan mai jegon da ke daki mai lamba na shida, ta ce min shanyar ta zata kwaso daga waje. Na ce mata idan ta shigo ta rufe kofar."

Gaban Asiya ya kara faduwa. Me hakan ke nufi ke nan? Ina Maree ta shiga ne? shanya?

"Shanya? Wacce shanyar? Ba mu bar shanyar komai a waje ba."

A lokacin sister Sala ta mike, idanun ta da nauyin barci, amma bai boye damuwar yanayin da suka samu kan su ciki. "Ni dai abin da ta ce min ke nan. So ina sauri a lokacin shiya sa ban tsaya dogon binckie ba."

"Yanzu to ga shi ba mu gan ta."

"Kai anya?! Ku dai duba da kyau. Ta na dai wani waje ne."

Zuciyar ta cikin bakin ta ta shiga aikin dubawa. Cikin wani lokaci ta leka dukkan dakunan, wanda mutane ke ciki da wanda ba kowa. Ta ji kamar ta shiga rusa ihu. Me ya samu Maree? Ina ta shiga? Ko dai ta shiga wani yanayi ne mai wahala?

Wannan tunani shi ke rura ma ta wutar neman 'yar uwar ta ta, cikin lambu, bakin get, dakin janareto...ko ina. Wasu wuraren ma ta san zai yi wuya ta same ta. To amma dole ta duba, saboda idan rakumin ka ya bata, a cikin duma ma za ka neme shi.

Tare da zuciya mai nauyin gaske ta nufi dakin na su, ta tarar da Muhibbat tana jijjiga baby, ita kuwa ta na ta rusa kuka. Nan take hankalin Asiya ya kara tashi, ta ji ita ma kwallar ta ciko mata. Tashin hankali, wai gobarar gemu. A cikin ranta ta so a ce ta samu Maree a dakin, a ce kawai komai ya faru ne cikin mafarki.

Da ganin ta Muhibbat ta ce, "Ki duba fa Minde, yarinyar nan an bata ruwan dumi ta sha. Amma ta ki barin kukan nan, sai karuwa yake yi. Ina Mareen?"

Ita ma tambayar da ta ke yi wa kanta ke nan amma ta kasa furtawa, gudun kar su kara jefa su cikin yanayin da ya fi wanda suke ciki. Ta hadiye yawu da kyar, lokacin da Dada ta fito daga alwala a bandakin ta kura mata ido.

"Ba ki same ta bane?" dada ta tambaye ta.

Yanzu kam abin da take tsoro ya tabbata. Amma, anya, Mariya za ta iya yi musu hakan kuwa? Za ta iya guduwa ta bar su cikin wannan halin tashin hankalin? Wayyo Allah!

KudiriWhere stories live. Discover now