Babi Na Shida

4.1K 342 97
                                    

“Yauwa, gwara da Allah Ya san a gan ku tare. Angwayen ne suka zo tare da matan da zasu dauki amarya. Duk da dai Azare za a kai ta, sun bukaci a yi komai da wuri a kan lokaci. Na yi bayani wa Gwaggonku Tambaya, yadda za a bayar da garar bikin.”

Asiya ta gyada kan ta, alamar ta fahimta. Ta fi kowa sanin yadda Dada ta sha wahalar tara garar Maree. A hidimar wannan biki kadai sai da ta sayar da shanun ta biyu hade da gonar da ta ke sa a noma mata gero da damina. Ta yi hakan ne don kar a ga gazawar su. Duk da ma Mudassir ya hana a sayi kayan daki. A cewar sa , ya tanada ma ta komai na kece raini.

Ku san duk matan garin a nan kowacce za ta ci ta gyatse sannan ta kai wa bataliyan ta gida idan ta tashi komawa. Haka al’adar garin su ya ke idan a na biki. Asiya abin haushi ya ke bata. A yi ta wahalar daurawa a sauke ba kakkautawa. Da a ce tana da iko, da lokacin auren ta in ya zo babu wani tuwon da za a yi.

Kawai garin za a kukkula da kuka, a raba wa kowacce mata, idan ta je gidan ta girka. Muhibbat ta sha dariyar wannan ra’ayi na ta. Oho dai. Allah Ya gani, da gaske ta ke yi idan za ta samu halin yin hakan.

Haka ta fita ta shiga shirin tara kan kawayen su da ma wadan da za su kai amaryar dakin ta. Ba ta kaunar ta sake bata wa Dada ran ta.

Motoci hudu ne kanana, hade da bus-bus manya guda biyu suka je diban jama’a. Mata kuwa suka cika tab don kuwa babu wacce ta ke son a bata labari. An gama bikin gidan su amarya, sauran na gidan ango.

An bar garin a na wake-wake cikin jerin gwano:
A yau rana na hazo,
A yau rana na hazo
A yau rana na durum durum
Rana na hazo
A yau Maree ta na fushi, Mudassir sai murna ya ke mata
Rana na hazo

Sun isa garin Azare misalin karfe bakwai na dare. Kasancewar an takura cikin motar, kowa sai hamdala take yi, don za su samu su huta. An kai su kofar wani gida a ka tsayar da su, ko kofar ba a bude ba.

Mata suka rika alla-alla a bude su shiga don akwai ma su laluri, wasu kuma yaran sun a ta fitina a motar. Abin da a ka fara da wake ya koma damuwa.

Wahalar dai bata kare ba, don sai a ka sake daukar kan motocin, a ka kuma nausawa wa ta unguwar, bayan abokan angon sun fita sun yi magana a tsakanin su. Sun koma dai suka rika ba da hakuri, kan cewa sun yi batan kai ne.

Wasa gaske, a ka rika yawo da su a gari, a na kewayawa, amma ba su kai wannan gida ba har suka kai misalin karfe tara.

“Kai, wai abokin ango, wannan wacce irin wahala ce da ukuba? Wannan gida kamar ya bace mu ku a doron kasa? Sai ka ce za mu kai ta karshen Nijeriya?”

Direban da ke tuka motar da suke cikin ta, wanda ita ma Maree ke ciki tare da Asiya, ya yi murmushi cikin neman afuwa, ya ce, “Ki yi hakuri Baba. Gidan Angon ne na nan garin ba mu san shi sosai ba. mun fi sanin gidan sa na Bauchi, shi yasa kika ga muna yawo.”

“Yo wannan ai da ma Bauchin kawai ku ka kai mu, mu san mun kwashi hanya. Amma yawon nan har jiri ya fara saka min da ciwon kai.” 

Direban ya ce, “Ki kara hakuri dai Baba. Gidan Bauchin ne ba a gama ginawa ba, gefe daya ne ya gyara sauran ukun bai karasa gyarawa ba. To yadda bikin ya zo ma sa cikin gaggawa ya sa shi yanke shawarar ya zauna a nan din kawai. To kun ga dare ya yi, ga shi ba mu san garin sosai ba. Angon ne fa da kan sa ya ke ma na kwatancen gidan da kan sa a waya.”

Rufe bakin sa ke da wuya, wayar sa ta dauki kara. Sau takwas ke nan, Asiya ta na kirgawa. Ya sake tsayar da motar sannan ya fita daga cikin ta don ya amsa. Gwaggo kuwaa ta ci gaba da sababi, wai bai amsawa a gaban su sai ka ce munafiki?

Sauran direbobin ma suka fita suka tarar da shi. Suka koma gefe suna Magana kasa-kasa. Ai kuwa Gwaggo Tambai ta fita ta same su cikin masifa, “Anya, kun kulla gaskiyaa kuwa? Tun dazu kuke ta yawo damu harm un haddace hanyoyin garin ma. Sannan motsi kadan sai ku tsaya mitin sai ka ce ma’aikatan gwamnati. Ko dai ku din ‘yan yankan kai ne?”

KudiriWhere stories live. Discover now