BABI NA.....BIYU.

1.8K 175 6
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*

*Na Xarah~B~B.*




*{NWA}.*



www.zahrabb.blogspot.com

*Vote me on Wattpad @Zarah_bb*

   *_Na gaishe ki da babbar murya Auntyna ta kaina nagode sosai da kulawar ki game da k'aunar ki a gareni wannan shafin na ki ne Allahu ya barmu tare@Aunty Taufeeqa A Baba kano. Allah ya raya mani Waleedina da Ahmad Allah ya nuna mani auren su in sha biki Ameen. #one love._*


      *BABI NA......BIYU.*


   Zaune suke a soron gidan firar su suke yi cikin walwala da farin ciki kallo d'aya zakayi masu ka tabbatar da suna matuk'ar son junan su.
   "My Jawaheer dan Allah komai rintsi kada ki gujeni kar ki damu da su Mumy da Dady insha Allah komai zai zama normal kinji koh my lady?"

"Insha Allah Yaya zaka sameni mai jajircewa dan kuwa ni kaina zuciya ta bazata barni inyi hakan ba fatana dai Allah ya za6a mana abinda duk yafi zama alkhairi a rayuwar mu baki d'aya"
    "Ameen Ameen nagode sosai Allah yayi maki albarka"

"Ameen ya rabbi my cwt J" Ta fad'a had'e da rufe fuskarta da tafonan hannunta.
  Kai kawai ya girgiza fuskarsa d'auke da murmushi, kunya da natsuwar Jawaheer suna d'aya daga cikin abinda ke k'ara tsunduma shi cikin k'aunar ta.

Sun jima suna fira kafin su kayi sallama ya wuce.

*****

  Tsaye take agaban dressing mirrow sai famar fesa turarukka take tuni d'akin ya d'auki k'amshi sai ka ce kamfanin buga turare ne, sanye take cikin purple t-shirt mai ratsin fari ajiki and black jeans wanda ya kameta sosai abinka da mai jiki cinyoyinta duk sun dame, gashin kanta kuwa tayi parking d'in sa da purple rebon sosai tayi kyau wani d'an ficikin mayafi ta yafa. Wayarta da ke gefen katifarta ta d'au ruri tana neman agaji ganin mai kiranta ya saka ta sakin wani k'ayataccen murmushi sa'annan ta d'aga wayar.

"Hello dear na ya kake?"
  Banji me aka fad'a ba a d'ayan 6angaren sai ji nayi ta amsa da "Ohhh! Am sorry dear gani nan fitowa yanzun nan ka ji" tana gama fad'in haka ta katse wayar, post d'inta ta d'auka da sauran abun amfani ta nufe hanyar fita daga d'akin dai-dai lokacin suka ci karo da k'anwarta mai suna Maryam. Sake da baki Maryam ke kallon irin tsinannar shigar da Yayarta tayi, cikin murya mai laushi Maryam ta fara magana "Haba Aunty Zubaida wannan sam ba girmanki bane dube irin wannan shigar da kika yi kuma a matsayin ki na y'ar musulma bayan nan ma yanzu ina zaki je a cikin darannan karfe tara fa aunty haba! Dan Allah ki ji tsoron Allah ki sani fa wannan duniya ba matabbata ba ce ina jiye maki ranar da zakiyi da na sani a lokacin da bata amfani sa'annan....." Tsawar da Zubaida ta daka mata ce ya saka Maryam yin shiru batare da ta shirya ba cike da jin haushin kalaman  k'anwarta tace "Ke har kin isa ki fad'a mani abinda ya dace nayi? Me ya dameki da rayuwa ta? Ina ruwanki da shigata ko inda zan je? Kinga Maryam ki fita idona ki je can da wa'azin ki bana so"
Wata uwar harara ta watsa mata game da bankad'e ta ta wuce a fusace"

Cikin sa'a bata tarar da Mama a falo ba wata ajiyar zuciya ta sauke dan ta san da ta same Mama too fa sai ta k'ara 6ata mata lokaci wajen wa'azin ta. A k'ofar gida ta same sa yana jiranta cike da rausaya ta isa wajen da yayi parking gefen mai zaman banza ta zauna, sam bai damu da 6ata masa lokacin da tayi ba illah ma yaba kyanta da ya shigayi ita kuwa sai murmushi take tana jin dad'in yabonta da yake yi.

   "Zubyna" Ya kira sunanta cikin wata makirar murya.

"Na'am Muby ya akayi ne?"
   Murmushi yayi kana ya ce "Yau tare nake son mu kwana gaskiya bazaki dawo gida ba sai gobe"

"Uhm Muby kenan idan har zaka iya bani abinda nake so ai wannan ba matsala bace"
   "Hhhhhhhhh Zuby kenan! Kema kinsan kud'i ba matsala ta bace nayi maki alk'awarin babbar kyauta"

"Allah koh Mubyna?"
   "Allah kuwa" Ya bata amsa yana wani malalacin murmushi.

Da haka dai har suka isa hotel d'in da suka saba shashancin su.
   Ni kuwa Zarah nace "Allah ya shirye mu Allah ya k'ara mana wadatar zuciya ya kuma k'ara karemu daga muguwar k'addara Ameen".

  Uhm!.... This is just the beginning



Shower shower shower shower me with your votes and comments.

Wattpad @Zarah_bb



*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Where stories live. Discover now