BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI.

601 52 2
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*










*Na Xarah~B~B.*




*{NWA}.*




www.zahrabb.blogspot.com



*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*


_Ina miki fatan alkhairi *My Nabeelert Zango (Marubuciyyar Zamani)* Allah ya k'ara kareman ke a duk inda kike Ameen, wannan shafin naki ne. #ILYSVM._



  *BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI.*



       K'wank'wasa(Knocking)k'ofa ta shiga yi a hankali shiru bai bud'e ba kuma bai yi mata izinin shigowa ba. Jin shirun yayi yawa ya sa ta tura k'ofar cikin sa'a kuwa ta bud'e kasancewar bai rufe ta ba. Kwance ta sa me sa akan gado yayi ni sa a tunanin da yake yi. Wajen mintin Juwairiyya biyu a tsaye amma sam bai san da wanzuwarta a d'akin ba, ganin in zata shekara dubu a nan bazai san ta shigo ba yasa a hankali ta kai hannunta kan hannunsa ta bubbuga kad'an had'e da kiran sunan sa a hankali.

Firgigit ya dawo daga duniyar da ya lula, numfashin sa ya sauke tare da mai da duban sa ga Juwairiyya ya ce

    "Ya akayi ne?"

"Mummy ce ta ce a fad'a maka ka yi bak'o a waje"

   "OK gani nan zuwa"

Ba tare da ta ce da shi komai ba ta juya ta fice daga d'akin. Ya fi minti biyar kafin ya ta shi cikin rashin kuzari ya fita.

   Tsaye take a bakin gate ta juya bayanta idonta k'yam akan gate d'in.

Direct wurin Baba mai gadi ya nufa bayan sun gaisa ya furta

    "Ina wanda ke nemana yake Baba?"

Da hannu Baba mai gadi yayi masa nuni da inda take a tsaye. Tun da taji Jabeer ya iso wajen ta saukar da nik'af d'inta k'asa in banda k'wayar idanunta ba abin da ake gani.

   Kallon sa Jabeer ya maida dai-dai inda Baba mai gadi ya nuna masa.

"To ai wannan mace ce Baba"

   "Eh daman ita ce ke neman ka"

"Amma abokina aka ce dani"

    "Ita ta buk'ace ace haka" Cewar Baba mai gadi.

"To!" kawai ya ce da Baba mai gadi sannan ya nufi inda take tsaye.

    "Assalamu Alaikum!" Ya furta dai-dai lokacin da ya iso wajen da take a tsaye.

"Wa'alaikun Salam!" Ta amsa masa ba tare da ta jiyu ba.

    "Ya akayi ne ki ke nemana?"

"Magana nake son muyi da kai" Ta fad'a had'e da jiyuwa sai dai fuskarta rufe take da nik'af.

   "To ai sai ki bud'e fuskar dan na san da wa nake magana"

     Tsaf ta k'are masa kallo, sosai ta tausayawa Jabeer ganin yadda ya koma cikin k'ank'anin lokaci. Jim kad'an tayi kafin daga bi sa ni ta furta,

"Kar ka damu, kai dai ka sa ma mana inda zamu tsaya muyi maganar dan bana son Mummy'n ka ta sa me ni anan"
   "OK! Zo mu je" Ya ce da ita tare da fara tafiya.

Mara masa baya tayi, tafiya kad'an suka yi suka iso wani korido anan suka tsaya, jiyuwa yayi ya kalleta game da cewa

    "Ina jin ki"

"To!" Ta fad'a had'e da d'aga nik'af d'in ta sama nan ta ke fuskarta ta bayyana.
   Ganin ko wacece yasa Jabeer yin murmushin da shi kansa bazai iya tuna yaushe rabon sa da yayi sa ba. Cikin jin dad'in ganinta ya ce

"Wai daman ke ce kika wani yi man basaja?"

   Murmushin itama tayi sannan ta ce

"To ai abubuwan ne sai da basajar"

   "Hakane kam!. To ya kike ya mutan gida?"

"Ni da dama, gida kuwa lafiya k'alau suke"

    "Masha Allah, amma ke me ya faru?"

"Me ye ma bai faru ba Jabeer"

   "To ki fad'an na ji mana"

"Yanzu kuwa" Ta fad'a tana gyara tsayuwar ta kasancewar koridon ba wajen zama.

   "Kiyi hak'uri Na barki a tsaye"

"Noo bakomai" Ta fad'a atak'aice.

"Jabeer!" Ta kira sunan sa cikin natsuwa.

    "Na'am Rashida" ya amsa mata.

"Game da matsalar ku da Jawaheer ne"

    Ta sosowa Jabeer inda ke yi masa k'aik'ayi, cikin rawar murya ya ce "Kin san dalilin da yasa ita da Innah suka shareni?"

"Sosai ma kuwa"

     "Dan Allah Rashida ki fad'a man ko na samu sassauci a zuciya ta" Ya fad'a fuskar sa fal da damuwa.

"Jabeer kayi hak'uri da abin da zan ce"

    Gaban sa ne yayi wata muguwar fad'owa, cike da fargabar abin da zata fad'a ya ce

"Bakomai Rashida ki fad'a kawai ina jin ki"

    "Alal hak'ik'a ba kowa ya haddasa wannan matsalar ba fa ce Mummy"

"What? Wace Mummy'n?"

    "Mummy'n ka Jabeer. Nan ta zayyane masa duk abin da ya faru ba tare da ta rage masa komai ba"

Tuni idanun sa suka canza launi suka yi Ja kamar gauta. Ba abin da yake fad'i fa ce "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Da haka ya samu sauk'in zugi da rad'ad'in da zuciyar sa ke yi masa.

    "Meyasa ba ki sanar da ni ba tun lokacin da abin ya faru?"

"Ita ta ce kar na fad'a maka ko yanzu ba da saninta ba na zo nan"

   "But why bata son nasani?"

"May be tana gudun abin da zai je ya dawo tun da su Mummy sunyi mata gargad'i."

    Shiru yayi dan bai san abunda zai koma cewa ba.

Sun fi minti uku ba wanda ya ce da d'an uwan sa uffan. Rashida ce tayi k'arfin halin katse shirun ta hanyar cewa

    "Ni zan wuce"

"To Rashida nagode sosai Allah ya saka maki da alkhairi."

    "Ameen ya rabbi"

Har bakin gate Jabeer ya rakata kana ya dawo cikin gida da tunani kala-kala aran shi.

******

   "Haba Jawaheer! Kin yiwa Jabeer adalci kuwa? Kin ga kuwa yadda ya zama kamar ba shi ba duk a dalilin ki? Dan Allah ki fad'a man abin da Jabeer yayi maki wanda yasa kike hukunta shi ta wannan hanyar"

Shiru tayi bata ce da shi komai ba in banda kuka ba abunda take yi masa.

    Sosai Mu'azzam ya k'ulu da lamarin Jawaheer dan duk lokacin da ya zo mata da irin wannan maganar ba abin da take ce masa illah ta saka masa kuka.

"Ke! Dallah yi man shiru ba kukan ki nake so ba, wallahi Jawaheer yau sai kin fad'a man abin da Jabeer yayi maki ku na sa6a maki"

    "Wai hayaniyar mecece nake ji haka?" Innah ta tambaya tare da fitowa daga cikin d'aki.

Da gudu Jawaheer ta yo bayan Innah ta 6uya, a hasale ya biyo ta.

    "Kai! Tsaya dan Allah, me tayi maka ne?" Innah ta ce da shi.

"Haba! Innah duba fa ki ga yadda yarinyar nan ke son ta maida mu wasu iri, tun yaushe nake tambayar ta abin da Jabeer yayi mata amma tak'i ta fad'a sai dai ta rink'a yiwa mutane wani kukan munafurci. To wallahi yau sai kin fad'a ko na tattakaki a gidan nan."

    "Ka yi Hak'uri, ba laifinta bane."

A tare suka juyo dan ganin wanda yayi maganar....







*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Onde histórias criam vida. Descubra agora