BABI NA SABA'IN DA BIYAR.

1.1K 53 15
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*







*Na Xarah~B~B.*






*{NWA}.*



www.zahrabb.blogspot.com

*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*

     _Shafin k'arshe na bada shi kyauta ga duk wasu masoya masu son junan su domin Allah. Ina rok'on Allah ya had'a mu da masoyanmu na gaskiya masu sonmu tsananinsu da Allah Ameen._

             *BABI NA SABA'IN DA BIYAR.*

*K'ARSHE!.*

                  
   K'aramin pillow ne rik'e a hannunsu sai faman wasa suke yi wannan ya jefawa wannan, wannan ya karb'a ya jefawa d'an uwansa da haka Jabeer ya shammace ta ya bugamata pillow a cinyarta ya tashi yana dariya sai zagaye d'akin yake yi cikin gudu-gudu sauri-sauri, binsa ta rink'a yi itama tana dariyar sun jima a haka amma bata samu nasarar kamashi ba.

"Allah ni ka tsaya na rama" Jawaheer ta fad'a cikin shagwab'a pillow rik'e a hannunta.

    Gwalo ya yi mata sannan ya ce "Ank'i"

"Uhm! Uhm!" Ta rink'a fad'i tana bubbuga k'afarta ita a dole sangarta idan ka ganta bazaka tab'a cewa ta ajiye y'ay'a uku ba.

     Ganin bayada niyyar tsayawa d'in yasa ta rik'e k'afarta tana fad'in "Wash! Wash! K'afata."

Da hanzari ya iso wajenta yana cewa "Me ya same k'afar?"

    Shiru tayi masa, yana duk'awa wajen k'afar sai ta rik'e shi tana fad'in "Na kamaka" Ta idar da maganar tana dariya.

Dariyar shima ya yi "Wayau kika yi man kenan."

   D'aukarta ya yi suka koma kan gado suka zauna cike da so da k'auna yake kallonta, cikin muryar shi mai sanyi ya ce

"Ina mutuk'ar alfahari dake uwar y'ay'ana, wallahi Jawaheer ji nake nafi kowa sa'ar mata a duniya ke d'in ta daban ce ko acikin mata duk namijin da ya same ki a matsayin matarsa dole ya godewa Allah, shiyasa bana gajiya da yin hamdala ga Allah da ya azurtani da ke a matsayin matata. Allah ya yi maki albarka, tabbas ba k'aramin dace nayi ba da na samu mace wadda ta iya *ZAMANTAKEWA*."

    "Duk abin da kake ji nafi ka jinshi hubby, kaine jigonmu kuma kaine ka inganta *ZAMANTAKEWAR* mu."

Wani murmushi ya yi game da janyota jikinsa ya lumshe ido sun jima a haka suna shak'ar k'amshin junan su kafin ya ce

    "Allah ya k'ara mana son junan mu Allah ya barmu tare har k'arshen rayuwar mu, ina rok'on Allah ya k'ara sanya alkhairi da albarka a cikin *ZAMANTAKEWAR* mu."

"Ameen Ya rabbi Abban Mahmud."

     Hannunsu mak'ale da juna suka fito falo. Mahmud da Mansur suna zaune suna yin assignment inda Fatima ke ta faman wasarta da bebin roba da sauran kayan wasarta.

Kan three seater(Kujerar zaman mutum uku) Jabeer da Jawaheer suka zauna, nan  yaran suka zo wajen su suna gaishe su. Ka mosu dukan su Jabeer ya yi ya rungume wani farin ciki marar misiltuwa na bin duk ilahirin jikinshi, a ransa sosai yake yiwa Allah godiya. Wayar sa ya d'auko ya ce

   "Ku gyara nayi maku hoto."

Jawaheer zaune ta rungumo duka yaranta Jabeer ya dauk'e su hoto, shima ya zauna tayi masu hoton hakama suka had'a kan yaransu su uku suka yi masu daga k'arshe suka zauna dukan su akan three seater Mahmud ya zauna gefen Jabeer inda Mansur ya zauna gefen Jawaheer suka saka Fatima a tsaka. Jabeer ne ya saita camerar wayarsa ya rink'a yi masu selfie sosai hotonan suka yi kyau gwanin sha'awa nima dake lab'e bayan labule na fito a hankali da wayata na d'auke su hoto, na jima ina kallon hoton na su sunyi kyau ainun.

    "I love you Abbana" Abin da na ji Mahmud ya fad'a. Shima Mansur ya fad'a cikin muryarta ta yara itama Fatima ta ce kamar yadda ta ji y'an uwanta sun furta.

"Love you more yarana" Jabeer ya fad'a game da rungumosu dukan su har Jawaheer sai dariya suke yi cike da k'aunar junan su.

    Nima dai dariyar nayi game da ficewa daga gidan ina mai rok'on Allah ya dauwamar da zaman lafiya da farin ciki mai d'orewa a rayuwar wad'annan bayin Allah'n masu son junan su saboda Allah da su da dukan musulmi baki d'aya Ameen.

*ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!!.*

    Ni *Zarah B~B* anan na kawo k'arshe wannan littafen nawa mai suna *ZAMANTAKEWA* kuskuren dake ciki Allah ka yafe man inda kuma nayi dai-dai Allah yasa mu amfana da shi. Allah yasa sak'on danake son isarwa ya isa ga dubban jama'a kuma Allah ya basu ikon amfani da shi Ameen summa Ameen.

      Gaisuwa ta musamman ga *MAhAIFIYATA* abun tink'ahuna Allah ya k'ara maki lafiya da nisan kwana masu albarka Ameen.

Allah ya gafartawa *MAHAIFINA* yasa aljanna ce makumar sa. Allah ya kai haske k'abarin shi da sauran musulmi baki d'aya. Allah ya kyautata tamu in tazo Ameen.

    Wannan littafen *TUKUICINE* ga duk *MASOYA* wad'anda suka jure game da jajircewa wajen karantun wannan dogon labarin nawa mai taken *ZAMANTAKEWA* tun daga farkonsa har zuwa k'arshensa fatan zamu yi amfani da darasin dake ciki. Kuma ina fatan ya fad'akar ya wa'azantar game da nishad'antar daku.

  Na *SADAUKAR* da wannan littafen nawa ga aminiyata kuma y'ar uwata *FATIMA MUH'D HASSAN(KAUSAR LUV.)* na gode sosai da k'aunar ki a gare ni Allah ya baki lafiya ya kuma dauwamar da zaman lafiya da farin ciki mai d'orewa a tsakaninki da mijinki, Allah ya barmu tare har abada Ameen.

Ku kan na daban ne a rayuwata matsayinku ya wuce duk wani tunanin mai tunani, ni ta kuce ku nawa ne Allah ya barmu tare har jikokin jikokinmu Allah ya k'ara sanya alkhairi da albarka a *ZAMANTAKEWAR* mu Allah ya k'ara karemu daga sharrin masu sharri Allah ka nisantamu da sharrin mak'iya da mahassada alfarmar annabi da alqur'ani, bakina ya yi kad'an ya bayyana tsantsar k'aunarku a zuciyata fatana Allah ya barmu tare cikin yarda da amincinsa Ameen *@RAZ*{Rabi'atu SK Mashi and Amrah Auwal Mashi.}

    Jinjina da bangirma gare ku k'ungiya mai albarka mai son y'ay'anta *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* Allah ya k'ara had'a kanmu ya kuma k'ara mana son junan mu domin sa Ameen.

Gaisuwa ta musamman ga duk masoyana na nesa dana kusa maza da mata, ku sani ina sonku da k'aunarku kuma ina alfahari da ku, ku saka a ranku Zarah BB ta kuce har abada.

       Na gaishe ku y'an group d'in *RAZ NOVELLA* da *MU SHA KARATU NA RAZ* da duk wani group da neke ciki ina gaishe ku sosai.

Banida bakin yi maku godiya sai dai akuda yaushe ina yi maku fatan alkhairi a rayuwar ku @ Abdul'aziz Arzika Jega(AAJ), Dr Aliyu Muhammad Sarki, Ahmad Bauchi(MR360), My Jidda Aliyu, Aunty Maijidda Musa thanks alot once again.

 
   *DODON JATAU* ya mayar da ita *MARAINIYA* tamkar Attahir a cikin *MASARAUTARMU* wanda da addu'a ya samu *SAUYIN YANAYI* a rayuwarsa.

Amrah da Zarah *AMINNAN JUNA* ne wanda kowa ya sansu tare, amma sai da Farouk ya shiga tsakaninsu har suka zama mak'iya tamkar *HAYDAR DA HAYBAR.*  A kowane lokaci kuka Amrah ta ke tana ambatar "Hak'ik'a wannan *K'ADDARATA CE!"* Sai daga baya Amrah ta furta *"NAYI DA NA SANI* na son zuciyata da na yi, *ZAMANTAKEWA* wata aba ce wacce ya kamata mutum ya san darajarta amma ni ban yi la'akari da wannan ba na butulcewa aminiyata."
     Littafan *MARUBUCIYAR* a tak'aice. *SAUYIN YANAYI* Na nan zuwa nan ba da jimawa ba insha Allahu.

Ni Zarah B~B nake cewa ma'ssalam ku huta lafiya sai mun had'u a littafena na gaba.😘

*For comments only 👇🏻.*
   08144410022.


*LOVE YOU ALL😘.*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 19, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ZAMANTAKEWA!.Where stories live. Discover now