BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS.

593 39 4
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*












*Na Xarah~B~B.*












*{NWA}.*







www.zahrabb.blogspot.com





*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*





      _As i promise here is ur gift *Ummi _25*. Tabbas amsar da kika ba da dai-dai take, i really appreciate the way u luv nd care. Wad'anda suka yi k'ok'arin bada amsa ba su samu dai-dai ba koma ina godiya da kulawar ku i love you all. #one luv._






    *BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS.*





      Sanye suke cikin uniform d'in islamiyyah ta sowar su kenan, tafe suke suna firar su ta duniya cike da nishad'i.

"Yauwa Maryam wai ni na tambaye ki?" Waliyya ta fad'a tana k'ok'arin gyara jakarta da ke neman fad'uwa.

    "Allah yasa na sa ni" Maryam ta bata amsa a tak'aice.

"Dan Allah dan son Annabi ki fad'an gaskiyar abin da ke ranki"

   "Uhm! Ina jinki"

"Meyasa bakya son kula samari?"

   "Waliyya kenan! Daman wannan tamabayar ce za ki yi man?"

"Eh, ita ce" Cewar Waliyya.

   Murmushi Maryam tayi kafin ta ce

"Haka kawai"

    "Ban yarda ba"

"Meyasa za ki ce baki yarda ba Waliyya? Bayan kin san bazan maki k'arya ba"

    "Yau kina son ki fara yi man ita Maryam. Ashe a duniya akwai abin da za ki iya 6oye man? Haba Maryam!"

"Bahaka bane Waliyya"

    "To yane?"

"Kiyi hak'uri kin ga yanzu mun iso gida amma gobe ma yi zancen Insha Allah"

   "OK Allah ya kaimu"

"Ameen Ya rabbi" Maryam ta amsa mata da shi.

    Sallama suka yi kowanan su ya nufi gidan su.


******

*_08:00am._*

 
  Zaune suke akan dinning table suna yin breakfast, kallon sa Abba ya maida gare shi ya ce

   "Zaid sai yaushe za kayi aure ne? Ko so kake sai ka tsofa ba kayi aure ba?"

Sosa kansa Zaid ya yi alamar jin kunya kana ya furta

    "Shekara ashirin da tara(29years)na keda fa Abba"

"Au! Me kake son ka fad'a kenan? 29years wasane? Nan da wata shekara(next year)talatin fa za kayi ai kuwa ka tsofa, gaskiya Zaid ka daina ganin mun saka maka ido idan har lokacin da muka d'ibar maka ya yi baka fitar da matar aure ba Allah zan nemota da kaina kuma wannan karon kayi kad'an ka ce bata yi maka ba" Ummi ta fad'a tana kallon sa.

   "Ayi hak'uri Ummi Insha Allah zan nema"

"Da dai ya fi maka" Cewar Abba.

   Daga haka kuma suka cigaba da yin breakfast d'in su cikin walwala da farin ciki.


******

"Jabeer ango, ni fa har na fara jin kana k'amshin angwaye" Yasir ya fad'a yana dariya.

    "Au! Kai sai yanzu ka fara jin yana wannan k'amshin? Ai ni tuni na ji shi" Cewar Sadiq.

"Kunga ni fa ba na son wannan zolayar" Jabeer ya ce da su yana murmushi.

    "Aradu ba wata zolaya JJ" Sadiq ya furta yana kallon shi cike da farin ciki.

"Gaskiyar kenan na Jawaheer" Yasir ya ce da shi.

     Haka dai suka cigaba da firar su cike da k'aunar junan su had'e da farin cikin abokin su zai aure wadda yake so.

******

"Ruky Wallahi bakida kirki, wato idan bani na neme ki ba ke sam bakya nemana"

   "Kiyi hak'uri Zuby wallahi bahaka bane, kwana biyu banida lafiya kuma wayana fad'uwa tayi jiya-jiyan nan nayi welcome back sa'annan yanzu nan na gama zancen gobe zan zo gidanku ta yadda zan samu number d'in ki. Kiyi hak'uri please Zuby na"

"Ayyah sannu Allah ya ba ki lafiya, ban san ba ki da lafiya ba ai da na zo dubin ki, dan kuwa ni ina nan ina faman fushi da ke ashe ba ki da lafiya, sannu"

   "Bakomai Zubyna, na ji sauki sosai Alhamdulillah!"

"Masha Allah! Allah ya k'ara sauki yasa kaffara ce"

   "Ameen Zuby"

"Goben za ki shigo ko?"

   "Eh, zan shigo Insha Allah" Ruky ta amsa mata da shi.

"OK ina zuba ido sai na ganki"

   "To na gode" Ruky ta furta tana murmushi.

Sallama suka yi game da tsinke wayar.

   Washegari kamar yadda Ruky ta fad'a hakan kuwa tayi dan ranar gidan su Zuby ta wuni sai bayan sallar magrib sa'annan ta wuce gida.




    Please don't forget to vote and comment on Wattpad @Zarah_bb

Ur vote nd comment count alot.



     Muje zuwa..........









*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ