BABI NA TALATIN DA BIYAR.

558 45 0
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*









*Na Xarah~B~B.*






*{NWA}.*





www.zahrabb.blogspot.com




*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*




   *BABI NA TALATIN DA BIYAR.*




    Da murmushi kwance a fuskarta ta shiga gidan su Ruky, zaune ta sa me ta a tsakar gida tana latsar wayarta. Ganin Zuby yasa ta mik'e tsaye tana yi mata oyoyo.

"Gwaggo fa?" Zuby ta tambaya.

   "Yanzun nan ta fita" Ruky ta fad'a game da jan hannun Zuby zuwa cikin d'akin ta.

Ruwa da lemo Ruky ta kawo wa Zuby. Kad'an ta sha ta ajiye.

   "Zuby y'ar duniya, ya kike ya mutan gidan?"

"Lafiya k'alau suke"

   "Ke naga yau sai wani nishad'i kike yi meye sirrin?"

"Kai Ruky ba ki da dama wallahi, To kuka kike son nayi?"

   "A'a amma dai da gani kin sa mu sa'ar wani ne"

"Zan dai sa mu"

   "Magana ta dai-dai take kenan" Cewar Ruky.

"Sosai ma kuwa" Zuby ta ce da ita.

   "Hhhhhh! Bani labari in sha" Ruky ta furta tana kallon Zuby.

Zamanta Zuby ta gyara game da cewa

   "Wani ne na had'u da shi duka-duka yanzu ina jin satin mu uku da shi. To shi yana son bariki amma baya iya fitar da kud'i, d'azu ba ki gani ba da na ce masa ina son dubu d'ari wallahi da k'yar na tsayar da dariyata harda wani uban gumi ya rink'a keto masa."

Dariya Ruky ta rink'a yi harda dafe ciki. Sai da tayi mai isarta kana ta ce

   "Wallahi Zuby ba ki da dama, To yanzu ya ku ka yi? Ya ba ki kud'in?"

"Cewa yayi ba kud'i hannun shi yanzu amma na bari zuwa yamma zai ba ni ko da 50k ne daga baya zai ban sauran, shi ne fa na ce ya kawo ni nan gidan da yamma ya zo ya d'auke ni"

   "Ki ce yau yini zungur za'a yi man"

"Sosai kuwa"

     Suna tsaka da firar su sai ga Gwaggo mahaifiyar Ruky ta dawo, gaishe ta suka yi sa'annan suka cigaba da firar su ta duniya.

******

A 6angaren Fahad kuwa yana gama yin parking ya fito daga cikin motar sa, wani babban shago naga ya dosa ina d'aga kaina sama naga an rubuta *RAZ MALL* yana shiga shagon kai tsaye office d'in manajan wajen ya nufa, a hankali ya tura k'ofar office d'in tare da shiga ciki bakin shi d'auke da sallama. Amsa sallamar mazaunin office d'in yayi fuskar sa d'auke da murmushi.

Guri Fahad ya samu ya zauna, bayan sun gaisa da abokin na sa sannan ya d'ora da cewa

   "Isma'il kud'i nake son ka ara man har zuwa jibi insha Allah zan baka"

"A'a Fahad nasan halin ka da rashin son biyan bashi kuma kaga nima wajen nan ba nawa bane"

   "Cikin kud'in ka za ka araman ba cikin kud'in mutane ba"

"Ai matsalar ba ka biyan bashi sai ankai ruwa rana."

   "Allah wannan karon zan ba ka, ka dai san inada kud'i ko?"

"Shin nawa ne ka ke so kuma me za ka yi da su?"

    "Dubu hamsin ne nake so. Ba abin da ya dame ka da abun da zan yi da su"

"Wallahi Fahad ka ji tsoron Allah, nasan bazai wuce wata mace ce zaka bawa ba, shiyasa duk sana'ar da kake yi ba cigaba a cikinta"

   "Ka ga ni ba wa'azi na zo kayi man ba, idan zaka ban ka ban idan kuma bazaka bayar ba sai ka fad'an ba sai ka tsaya yi man surutu ba"

"Da ace wani abun arziki za ka yi da su da ko nawa kake so zan ba ka kyauta ba ma aro ba, amma nikam yanzu bazan ara maka kud'ina ba ka je ka kaiwa mace. Kuma wallahi idan baka daina neman matan nan ba sai na sanar da Alhaji(Mahaifin Fahad kenan)."

"Ka da ka fad'awa Alhaji ka fad'awa Hajiya" Fahad ya fad'a game da barin office d'in a hasale.

   Murmushin takaici Isma'il yayi, duniya ya tsane halin abokin sa kullun cikin yi masa nasiha yake amma kamar yana zuga shi, ga shi ba wani kud'in azo agani ne da shi ba amma sai neman mata kamar bunsuru duk nan yake halaka abin da ya mallaka. Ya sha arawa Fahad kud'i amma baya biyan sa wani lokacin ma na wasu zai ara but k'arshen ta shi zai biya.

Isma'il da Fahad abokanin juna ne tun yarintar su kuma unguwar su d'aya amma suna da banbancin halaye shiyasa basa rabuwa da yin fad'a dukda da sunyi suke shiryawa.

Sosai Fahad ya wahala kafin ya je ya yiwa wani abokin sa k'aryar cewa akwai wasu kayan sa da za su zo dan Allah ya ara masa kud'i da kayan sun zo sai kawo masa, cikin sa'a kuwa ya samu abokin na sa ya ara masa kud'in.

*_06:30pm._*

   Dai-dai lokacin Fahad ya iso k'ofar gidan su Ruky, number Zuby yayi dialing sai da kusa tsinkewa sa'annan aka d'aga.

"Ki fito gani a k'ofar gidan na iso"

    "OK gani nan fitowa" Aka amsa masa a d'ayan 6angaren.

Ya shafe fiye da minti goma yana jiran ta sa'annan ta fito. Cike da rausaya ta iso inda yayi parking, sosai Zuby ke ba shi sha'awa saboda ta cika mace iya mace komai ta had'a, wasu yawu ya had'iye sannan ya ce

"Sannu da fitowa Zuby na"

   "Yauwa" Ta amsa atak'aice.

"Ga k'awata nan ku gaisa" Ta ce da shi a yangace.

   Cikin fara'a Fahad da Ruky suka gaisa. Sallama Zuby tayi da Ruky sannan suka wuce.







*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Where stories live. Discover now