BABI NA GOMA SHA SHIDA.

743 57 2
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*








*Na Xarah~B~B.*





*{NWA}.*



www.zahrabb.blogspot.com


   *Vote me on Wattpad @Zarah_bb*


_Mafi hankalin mutane su ne wad'anda suka bar duniya kafin ta barsu, suka gyara k'abarinsu kafin su shige shi, suyi sallah a cikin jama'a kafin a sallace su, sannan suyiwa kansu hisabi kafin a gurfanar da su a ranar hisabi._




    *BABI NA GOMA SHA SHIDA.*



    K'wafa tayi game da shigewa gidan a ranta sai fad'i take "Watau Yaya bai daina kula y'ar matsiyatan nan ba ko? Aradu yau sai na fad'a ma Mummy, wani murmushin mugunta tayi"

Zaune ta same Mummy a parlour tana kallon Zee world ga ba d'aya ta maida hankalinta ga film d'in da suke yi, har Juwairiyya ta shigo bata sa ni ba sai da ta d'ora kanta akan cinyarta sannan ta maida dubanta gareta tare da cewa

   "Yaushe kika dawo ne y'ar lelena?"

"Kina can kina kallo ya za'ayi kisan na dawo" Juwairiyya ta ce da ita cike da sangarta.

    "Sorry sha lelena film d'in ne da kyau wallahi. Ya hanya hope ba wata matsala"

"Hanya Alhamdulillah Mummy"
   "Masha Allah"

"Mummy!"
    "Na'am Juwairiyya"

"Mummy ashe daman Yaya bai daina kula y'ar talakawan nan ba?"
   "Wane Yayan kuma Juwairiyya?"

"Yaya Jabeer mana"
    Ido Mummy ta zaro kana ta ce "Ba dai tare da Jawaheer kika ganshi ba?"

"Wallahi Mummy tare na gansu ya ajiye ta a mota harda wata k'atuwar leda naga ta fito da ita ta nufe gidan su"

   "Hmmmm! Lallai Son ya rainani, ni zaiyi wa wayau? Watau bai ji maganata ba, zan ko yi maganin su gaba d'aya dan wallahi duk wanda ya ci tuwo dani miya ya sha"

K'ara zugata Juwairiyya ta rink'a yi ita kuwa sai hawa take.

*_09:30pm._*

Mummy ce zaune akan (Three seater) kujerar zaman mutum uku sai Juwairiyya a gefenta fira suke suna ta faman dariya kamar wasu sa'anni, da sallama k'unshe a bakin shi ya shigo falon had'e da gaishe da Mummy'n sa, tamau ta d'aure fuska kamar ba ita bace ke dariya yanzun nan ba, can ciki ta amsa masa gaisuwar sa.

   Kujerar dake gefen Mummy ya zauna kana ya ce "Mummy lafiya kuwa naga yanayin ki ya canza?"

"Me ya dameka da yanayina tun da ka nuna mini ban isa da kai ba"
    "Subhanallah! Mummy me nayi?"

"Uhm! Ni ban san lokacin da ka rainani har haka ba"

   Ganin ya rasa gane kan Mummy'n ta sa yasa ya maida duban shi ga Juwairiyya ya ce "To Hajiya ai sai ki bamu guri muyi magana ko"

"Ba inda zata je" Mummy ta furta.
    Kallon da Jabeer ya watsawa Juwairiyya ya sakata fad'in "Mummy bara na je daman akwai abin da nake son nayi a d'aki idan nagama zan dawo"

"Bana son k'arya fad'a mani gaskiya"
    Marairaice fuska tayi sa'annan ta furta "Allah Mummy da gaske nake"

"To shikenan je ki sai kin fito"
   "Yauwa Mummyna" Ta fad'a game da barin falon ta nufi hanyar da zata sadata da d'ankinta.

Zaman sa ya gyara cike da girmamawa ya fara magana
    "Mummy kiyi hak'uri dan Allah ki fad'a mani laifin da nayi maki"

"Ka fi kowa sanin abin da kayi, ko so kake ka maida ni wata iri ne?"
    Shiru yayi dan ya ma rasa abin da zai ce mata.

"Ohhh! Bazaka yi magana bane?"
    "Mummy kiyi hak'uri ki fad'a mani laifina"

"Duk da nasan kasan laifin ka kawai dai bazaka fad'a ba to ni bari na fad'a maka"
    Bai ce komai ba illah k'ara natsuwa da yayi game da bata duk hankalin shi.

"Wato Son in nuna maka banida ra'ayin ka aure y'ar matsiyatan nan ka nuna mani ban isa ba ko? So kake kaga iyakata ko Son?"

   Sai yanzu ya gano inda fa d'an Mummy'n ta shi ya dosa. "To waya kawo mata wannan gulmar?" amsar da ya kasa bawa kansa" Mummy ta katse masa tunani ta hanyar cewa

"Ka bani amsar tambaya ta"
   "Mummy ni fa tun lokacin da kika ce in rabo da ita na shareta. Me aka ce maki ne?"

"Hmmm! Yaushe ka iya k'arya Son? D'azun nan fa da idona naga ka ajiye yarinyar nan a mota harda yi mata sayayya"

    Ido ya zaro da k'arfi cike da mamakin kalaman mahaifiyar shi ya ce

"Ni! Mummy"
    "K'arya zanyi maka ne?"

"A'a" Ya fad'a yana sosar kai.

    "To bara ka ji in fad'a maka, daga yau daga rana mai kama da ta yau na sake ji ko ganin ka da wannan yarinyar wallahi Son sai na matuk'ar sa6a maka sha-sha-sha kawai wanda bai san ciwon kansa ba" Tana gama fad'ar haka ba tare da ta tsaya jin komai daga gare shi ba ta ta shi ta nufi side d'inta.

Duk'ar da kansa Jabeer yayi game da dafe su da duka hannayen sa idon shi yayi jajir kamar gauta, duk sanyin A.C dake falon bai hana Jabeer yin gumi ba(Zufa). Tunani yake yi wace irin uwace Allah ya ba shi? A iya sanin shi duk uwa tana son taga d'anta cikin farin ciki da walwala, To meyasa Mummy'n sa ke k'ok'arin tarwatsa masa farin cikin sa. A daddafe ya tashi ya tafi 6angaren shi, da shigarsa d'aki ya kwanta kan gado tare da yin lamo kamar mai bacci har k'arfe d'aya da minti arba'in bacci ya k'i ya zo ma Jabeer sai faman tunani yake ya sak'a wannan ya warware wancan ganin har k'arfe biyu ta buga ba alamun bacci a idon shi yasa ya tashi ya shiga (Toilet) ban d'aki dan d'oro alwala, nafilfili ya shiga yi game da rok'on mafita awajen mahaliccin shi sai da yayi sallar asuba ya kwanta shima bai jima ba ya tashi ya shirya tsaf ya fice daga gidan ba tare da kowa ya sa ni ba.....






*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Onde histórias criam vida. Descubra agora