BABI NA GOMA SHA TAKWAS.

664 58 2
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*





*Na Xarah~B~B.*




*{NWA}.*




www.zahrabb.blogspot.com


*Vote me on Wattpad @Zarah_bb*



  *_Wannan shafin naku ne aminnai na kuma y'an uwa na, baki ba zai iya fad'in matsayin ku ko muhimmancin ku a gareni ba sai dai a koda yaushe ina rok'on Allah ya k'ara mana so da k'aunar junan mu. I luv u so so very much my proudly RAZ @{Rabi'atu Sk mashi and Amrah Auwal mashi}. #one luv._*



*BABI NA GOMA SHA TAKWAS.*

   K'arfe takwas da minti ashirin dai-dai na dare Jabeer ya isa gidan Baba Al'ameen. A falo ya same Aunty Fati kamar yadda yake kiranta tare da yara suna kallo, bayan yayi sallama suka amsa ya gaishe da Aunty Fati tare da zama d'aya daga cikin kujerun dake falon, gaishe da shi yaran suka yi cikin fara'a ya amsa masu. Cikin sakin fuska Aunty Fati ta ce

"Ai ni nayi fushi da kai Jabeer"
   "A'a Auntyna ayi hak'uri dan Allah kar kiyi fushi da ni in shiga uku"

Dariya tayi sa'annan ta furta "Ka ganka ko Jabeer"
    Shima dariyar yayi kana ya ce "Me nayi kuma Auntyna?"

"Hmmm! Ba kayi komai ba"
   Haka dai suka yi ta barkwancin su shi da auntynsa dan Jabeer akwai fara'a da son mutane. Sai can daga bisani ya ce

"Aunty Baba na nan kuwa?"
   "Eh yana nan"

"Dan Allah ina son magana da shi"
   "To bara na fad'a masa" Ta ce da shi game da ta shi ta nufi hanyar da zata sadata da 6angaren mai gidan na ta.

Jabeer ji yake ina ma ace ana canjen iyaye da tuni yayi, lokota da dama yana tunanin meyasa halayen mahaifinsa suka sha ban-ban dana Baba Al'ameen kuma ga su uwa d'aya uba d'aya.
   "Saboda kowa da yadda Allah ya halicce shi, dan haka kama daina la'akari da iyayen su d'aya" Wani 6angare na zuciyar shi ya ba shi amsa.

Ajiyar zuciya ya sauke kana ya ce "Ina ma halayyar Mummy zata dawo irin ta Aunty Fati, da sai nafi kowa farin ciki da jin dad'i. Sosai *ZAMANTAKEWAr* su Baba Al'ameen da Aunty Fati ke burge shi komai na su cikin tsari suke yin shi." Yana tsaka da zancen zucin shi ya ji Aunty Fati na cewa
   "Jabeer ya ce ka same shi a d'aki"

"To Auntyna" Ya fad'a yana k'ok'arin ta shi.

   Da sallama k'unshe a bakin shi ya tura k'ofar d'akin, amsa sallamar Baba Al'ameen yayi. K'asan kujerar da Baba Al'ameen yake zaune Jabeer ya zauna, cike da ladabi ya gaishe da Baban na shi.

Fuskar sa cike da annuri ya amsa gaisuwar had'e da tambayar sa ya mutanan gidan.
   "Lafiya k'alau suke" Jabeer ya ba shi amsa.

"Fatima ta ce kana son magana da ni"
    "Eh Baba"
"Hope dai lafiya?"
     "Da sauk'i za'a ce"

"Meya faru ne Jabeer?"
    "Wallahi Baba Mummy ce"

"Me tayi?"
    Duk'ar da kansa yayi k'asa sa'annan ya zanyanewa Baba Al'ameen duk abunda ke faruwa bai 6oye masa komai ba.

Shiru Baba Al'ameen yayi zuciyar shi cike da mamakin halayen matar Yayansa. Ni sawa yayi kana ya fara magana

   "Amma gaskiya Hajiya bata kyauta ba, sam bai dace ta guje talaka ba idan har tayi la'akari da wasu abubuwan, amma bakomai ka cigaba da hak'uri kuma ka dage da addu'ar duk abinda yafi zama alkhairi. Insha Allah zan je inga ko Allah zai sa ta fahimce ni"

"To Baba nagode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi"
   "Ameen Ameen. Yaya yana gari?"

"Eh! Yana nan"
     "Yaushe ake samun sa a gida?"

"Da safe ko bayan sallar isha"
    "OK insha Allah ina nan zuwa da yardar Allah"

"To Baba Allah ya bada iko"
    "Ameen" Baba ya furta game da mik'owa Jabeer kud'i wanda ni kaina bansan ko nawa bane.

K'in kar6a Jabeer yayi har sai da Baba ya matsa masa sannan ya kar6a game da yi masa godiya. Sallama yayi da shi ya fice daga d'akin.

  A parlour ya same Aunty Fati wannan karon ita kad'ai ce yaran duk sun tafi d'akunan su dan su kwanta kasancewar tara harda y'an mintuna na dare.

Nan ma sallama yayi da Aunty Fati kana ya wuce.

******

   Zaune take a harabar gidan tana d'ura zo6o a goruna. Mama ce ta fito fuskar ta d'auke da murmushi ta k'araso wajen da y'arta take zaune.

"Maryam ba ki gama ba ashe?"
    "Eh Mama amma saura kad'an insha Allah"

"To bara na tayaki"
     "A'a Mama dan Allah ki barshi yanzun nan zan k'arasa"

"To Maryam Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a da rabo"

    "Ameen ya rabbi Mamata"

Murmushi Mama tayi ta juya zata shiga cikin falo, jin anyi sallama yasa ta tsayawa tare da jiyowa ta amsa sallamar.

   "A bada zo6o da kunun aya" Yaron ya fad'a.

"To kawo" Maryam ta ce da shi tana k'ok'arin ta shi ta ba shi.

    "A'a kiyi zaman ki bari na ba shi"

"To Mama nagode"
      Wajen da Frizer take ajiye Mama ta dosa tare da d'aukowa yaron abunda ya zo saya ta mik'a masa.

"Ga kud'in Maryam"
    "Ki shiga da su ciki Mama"

"To" kawai Mama ta ce da ita had'e da shigewa ciki.





*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Where stories live. Discover now