BABIN FARKO

2.7K 85 4
                                    

https://www.Facebook.com/Romantic-Writers-Association-415799935882006/

💥 *ROMANTIC WRITERS ASS...*💥

*We are the star's keep shining always*💥

    🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
            🌲🌲🌲
               🌴🌴
                  🌳

     😜 SAUDALA 🥴

Story & written
        By
NEAT LADY
✍🏻✍🏻

Dedicated to SAUDALA fan's group, kuyi yadda kuke so dashi😘😘😘


Bismillahir rahmanir rahim

3&4

Wata dariya ce ta kusa kufcewa saudala , amma sai ta danne ta cigaba da cewa

" karki sake ki fito tsakar gida yanzu, ki bari sai da safe in ba haka ba anan zaki kame har sai wani daren ,

Iya da take kwance cikin kashi kai kawai ta daga jikin ta na rawa,

Tace "in kika fadawa wani wannan abinda ya faru shikenan sunan ki gawa ,

Cikin rawar baki iya tace " kwarankwasi bazan fada ba ,

Saudala cikin tsawa tace " rife idon ki

Tsawar  da tayi yasa iya kuma sakin wani kashin😂 , cikin sauri ta rife idon ,

Mikewa saudala tayi ta wata tafiya kamar aljanar gaske tana bude hannu kamar tattabara ,

Tana zuwa daki ta dinga dariya kamar mahaukaciya ,

Tace " zaki gane kuran ki iya , badai ni kika zaga ba ,

In sane nace karta fito sai da safe yadda zan kuma cin dariya 😂😂

Tashi tayi ta wanke fuskar ta ta cire kayan jikin ta ta kwanta,

Tunda saudala ta fita iya take kuka tana fadin

" shikenan karshe na yazo  aljanu sun fara bibiyata , kai dole gobe nabar gidan nan dan bazan iya zama wannan aljanar ta kashe ni ba ,

Haka iya ta kwana bata rintsa ba  , tana ji ana kiran sallah amma babu damar fita tunda aljana tace sai da safe ,

Karfe shida na safe saudala nata tsakar gida a zaune umman ta kuma ta fara hura huta dan daura abinci,

Iya ce ta fito kashi yana bin kafar ta duk ta bata wajan ,

Ai saudala tana ganin ta ta mike, amma sai tayi kamar bata ganta ba , kawai sai tayi wajan umman ta

Iya da bata kula da kowa ba cikin sanda take tafiya duk dan kar saudala ta ganta da kashi🤣🤣

Sai da ta bari iya ta fito sosai yadda babu damar komawa sannan tace

" kai umma warin kashi fa nake ji ,

Umma tace " nima haka saude warin ya isheni ,

Sai kam saudala ta juyo ,

Tace " lah yanzu iya kashi kikayi a kwance sai kace wata saniya ,

Ta fada tana kyalkyalewa da dariya😂😂😂

Iya ta kulu sosai tace " baban ki ne saniya ba ni ba , banxa me kan daddawa,

Saudala tace " kika kuma zagi na ,

Cikin masifa iya tace " an zage kin ko zaki rama ne ,

Saudala tace " ke dai kiji da kashin kwance ki,

SAUDALAWhere stories live. Discover now