BABI NA BIYU

1.2K 38 1
                                    

🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
           🌴🌴🌴🌴
                🌳🌳
                   🎄

     😜  SAUDALA 🥴
   ❣❣❣❣❣❣❣


®🇳🇬
_*ABORIGINAL WRITERS ASSOCIATION*_📚✍🏻
[❄Dance above the surface of the, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

*STORY & WRITTEN*
             *BY*
NEAT LADY✍🏻

_Last page din nayi mistake zan saka page 5&6 nasa 4&6 , dafatan kun gane_.

*Dedicated to humairah (innahoro)*😘😘 

*Kiyi yadda kike so dashi my horo*😜  


*Bismillahir rahmanir rahim.*

7&8

*CIGABAN LABARI.*

Iya ce zaune ta rafka uban tagumi tana tunanin aljana.

Saudala ta fito daga d'aki ta zauna kusa da Iya tace.

"Iya da zakaji shawara ta kar kije Abujan nan , dan yasin na tsani zuwa birnin nan yawan cinsu duk 'yan iska ne , kuma duk inda kika je sai aljanar ta biyo ki , gwara ma kiyi zaman ki anan"

Iya tayi shiru tana sauraran Saudala har ta kai aya sannan Iya tace,

"Babu abinda zaisa na zauna a garin nan karkari na zuwa gobe "

Tana gama fad'ar hakan ta tashi ta shiga d'aki.

Saudala kam murna ce ta kamata aranta take cewa ahh to ai da sauƙi tinda zama ki kai goben.

Bayan sallar magariba Saudala da 'kawayenta suka nufi dandali.

Tunda suka isa sukaga samari da 'yan mata ana zance, wani saurayi da take jin haushinsa ta gani yana kwasar love abinsa.

Murmushi Saudala tayi dan har ta shirya muguntar da zatayi musu.

Gefe suka koma wajan da babu haske sosai , Saudala ta had'a musu plan d'in da zasuyi.

wani kare Saudala ta tsokano ai kam ya biyosu da gudu,
Dije da Talatu suna ganin haka suka nufi cikin dandalin Suna ihun "kura jama'a"

mutane na juyowa suka ga Saudala tana gudu abu yana binta a baya sai kowa yayi ta kansa.

Cikin gudu wani saurayi ya fad'a cikin kwata wandon sa ya cire amma bai tsaya gyara wando ba ya cigaba da gudu abinsa.😂

Me saida kifi kam tuni kifinsa ya zube cikin kwata 🤣.

haba me Saudala zatayi in ba dariya ba , ta dinga dariya kamar mahaukaciya sabowar kamu harda riƙe ciki.

Ihu ta fara tana cewa,

"Hoooooooooo ba kura bace kare ne kuma nina tsokano shi kuyi yadda zakuyi dani"

ta fad'a tana kwasa a guje ,
Aikam suka rufa mata baya tana gudu suna binta har ta 'karasa gida.

Da gudu ta shige gida tana faman hakki.

Tunda Baba yaganta yasan tayi halin nata ns tsokana barima daya jiyo hayaniyar mutane a waje.

Ko kallanta baiyi ba ya tashi ya fita wajen,
Dayake kowa na ganin mutuncinsa a unguwa sai suka hakura suka koma.

A tsakar gida ya tadda su Baaba ya kalli Saudala yace,

" Wai yaushe zakiyi hankali ne Saude? Ace ke kullum cikin tsokanar mutane kike , yaushe zakiyi hankali ne ?"

Iya ta kar'be zancen da fad'in,

SAUDALAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن