BABI NA TAKWAS

668 26 3
                                    

🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
       🌴🌴🌴🌴
            🌳🌳
              🎄

   😜 SAUDALA 🥴
❣❣❣❣❣❣❣




®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼








*STORY & WRITTEN*
            *BY*
   *NEAT LADY*✍🏻





_*kai gaskiya jiya nayi mutuk'ar jin dad'in comment d'inku my fan's, Allah ya bar mu tare.*_😁😁😁






*Bismillahir rahmanir rahim*




61&62




"Kutumelecy ni Hadiza mai zan gani , yanzu Abdul daman cin amatana kake.?" Hadiza ta fad'a cikin b'acin rai.

Jin muryar mutum yasa Saudala saurin mik'ewa daga jikin Abdul tana hararar sa.

Dak'yar Abdul ya mik'e yana kallan cike da mamaki.

Cikin dashewar murya yace "My hady yaushe kika zo?".

Cikin d'aga murya tace " ban sani ba!, Ashe daman duk abinda ka fad'a min yaudara ta kake , wai a tak'aice ma wace wan'nan .?" Ta fad'a tana nuna Saudala.


Juyawa yayi ya kalli Saudala da take auki hararar sa yace , "K'anwata ce ."

"Daman kana da wata k'anwa ne bayan Fadila, kada kace min wan'nan ce Saudat d'in ."

Saudala tace "nice Saudat a ina kika sanni ? , Dan nidai nasan kaf dangin mu babu mace kamar skeleton."

Cikin hargagi Hadiza tace "ni kike kira skeleton ?".

Murgud'a baki tayi tace " ai da hakan kika dace , aba kamar muciya."

Da sauri ta k'araso da niyar Marin Saudala Abdul ya rik'eta yana fad'in , "wai meye haka my life , wan'nan fa ba girman ki bane."

A fusace ta juyo tace "ina so ka fad'a min da bakin ka wan'nan itace matar ka Saudat.?"

Gyad'a Kai Abdul yayi alamun eh.

Sai kuwa ta fashe da kuka tace "Ashe baza iya cika alk'awarin da ka d'auka ba , kace min wani Abu bazai tab'a shiga tsakanin ku ba , Ashe duka dad'in baki kake mun." Ta k'arasa maganar tana kuka.

Rik'e hannun ta yayi suka zauna akan kujera yace "haba my life yanzu idan akace wani Abu ya shiga tsakanina da wan'nan yarinya zaki yarda?, me take dashi har da ja hankalina na kula ta nida ba sonta nake ba,  ki k'wantar da hankalin ki yanzun ma ba wani abu bane kinji."

Hadiza ta share hawayen ta tace "shikenan na yarda , Amma ina jin tsoro kar wata rana a kula Yarinyar nan dan ina da kishi sosai zan iya kashe ta."

Abdul yace "ki kwantar da hankalin ki babu komai."

Saudala kuwa tana tsaye tana kallansa, har cikin ranta taji wani iri da yace baya sonta amma sai ta dake tace , "ai sai yanzu na gane wan'nan ce Hadiza taka , tab Amma gaskiya mai hancin karas Sam baka iya zab'e ba , ka rasa wacce zaka zab'a sai wan'nan abar , Aradu da shigo na zata namiji ne wai ashe macece , tab wan'nan ko a cikin mazan ai irin su ne masu k'wantai ." ta fad'a tana dariya.

Juyawa tayi ta kalli Abdul da yake kallan ta dan shi gabad'aya ya manta tana d'akin ya zata ta fita, tace "Maza guda biyu a zaune ." tana gama fad'ar hakan ta fice daga parlourn.

SAUDALAWhere stories live. Discover now