BABI NA TARA

936 25 3
                                    

🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
      🌴🌴🌴🌴
          🌳🌳
            🎄

  😜 SAUDALA 🥴
❣❣❣❣❣❣❣

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*STORY & WRITTEN*
           *BY*
  *NEAT LADY*✍🏻

*Dedicated to my blood sisters*❤

*Bismillahir rahmanir rahim*

69&70

Shikuwa Abdul part d'in Mama shiga babu ko kuna mutanen da suka parlourn yayi shigewar sa d'akin Mama.

Ita da Fadila ne a d'akin da ya shiga da sallama.

Amsawa Mama tayi tare da fad'in , "Abdul kuna tare da Saudat ne.?"

Abdul yace "eh Mama bata dad'e da dawowa ba , wai lesson suka tsaya yi a makarantar."

Ajiyar xuciya Mama tayi tace "maza kira min ita ga mutane tun d'azu suke son ganin ta."

Yace "to bara na kira ta, Fadila zo in aike ki." Ya fad'a yana fita daga d'akin.

Bin yaban sa Fadila tayi tace "gani ".

Had'e rai yayi san'nan yace , " ki shiga d'aki ki d'auko min kayan da Saudat zata saka yanzu ina jiran ki a part d'in na." Yana gama fad'ar hakan ya juya ya bar wajan.

Da kallo Fadila ta bishi tana tunanin yaushe suka fara shiri da Saudat har haka , d'aki ta shiga ta d'auko kayan ta fito.

Da Iya suka had'u tazo zata shiga d'akin Fadilan , tana ganin ta tace , "yauwa Fadila maza ga bak'i can kije ki kai musu abinci."

Fadila tace "to Iya, Amma bara na kai wan'nan sak'on ko."

Kallan abin hannun ta Iya tayi san'nan tace "ina kuma zakije da kaya a hannun ki.?"

Fadila tace "kayan Saudat ne Yaya Abdul ne yace na ka masa part d'in sa." Ta k'arasa maganar tana barin wajan .

Rik'e baki Iya tayi tace "toh lallai mai k'atan kai ya cika Mara kunya."

Bayan Abdul ya fita daga part d'in Mama nasa ya koma , a inda ya barta anan ya dawo ya same ta .

Zama yayi baice komai ba itama kuma haka.

Fadila ce ta shigo d'akin da sallama , kallan inda Saudala take tayi san'nan tace ,

"Yaya Abdul gashi." Ta fad'a tana mik'a masa kayan .

Karb'a yayi ya ajiye a kusa dashi ya kalli Fadila Yace, "zaki iya tafiya."

Fadila tace "Amma bro zafa ayi mata make up , sai dai na kira mai make up d'in nan in yaso tayi mata anan d'in."

Yace "naji ki kira Dan bazata fita da wan'nan munafukin siket d'in ba kamar wata wacce zata tsallake wuta."

Murmushi Fadila tayi tace "idan ta gama shirya a sai kayi min waya muzo da mai make up d'in." Ta fad'a tana barin parlourn.

Kallan Saudala yayi yace "tashi kije ki saka kayan ." ya ce yana mik'o mata .

Karb'a tayi san'nan tace  "zan shiga wanka kar ka shigo d'akin har sai na gama." Ta fad'a tana murgud'a baki.

Sakin baki yayi yana kallan ta yayi murmushi yace,  "d'aki nane inda ikon da zan shigo lokacin da naga dama."

Ba tace komai ba ta shiga d'akin ta saka key .

SAUDALAWhere stories live. Discover now