BABI NA GOMA (Ƙarshe)

1K 38 3
                                    

😜 SAUDALA 🥴
❣❣❣❣❣❣❣


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼





*STORY & WRITTEN*
            *BY*
   *NEAT LADY*✍🏻


*Dedicated to my blood sisters*❤





*Bismillahir rahmanir rahim*






81&82




Cikin b'acin rai yake bud'e takardar , tsayawa yayi yana karantawa yana huci ,  wular da takardar yayi ya juyo yana kallan ta cikin b'acin rai.


Saudala kuwa ja da baya take tana fad'in, "ka tsaya kayi binkice wallahi babu Wanda ya kawo ni , "

Cikin tsawa yace "ki rife min baki !, in ba shi ya kawo kiba waye ya dawo dake ?,"

Girgiza kai Saudala take tana hawaye tana fad'in, "na rantse da Allah babu Wanda ya kawo ni , nasan dai drop na hau tunda ina ta jiran drivern bai zo ba shine kawai na hau drop na dawo, kuma kaje makarantar ka tambaya nasan za'a fad'a maka wallahi babu Wanda ya kawo ni ," ta fad'a tana fashewa da kuka.



Juyawa yayi ya kalli Hady da take ta murna, cikin tsawa yace,

"Kinga Wanda ya kawo tan da idon ki ?" , nan da nan jikin Hady ya fara rawa kamar mazari , tana tunanin Allah yasa kar ya gane k'arya take.

Katse mata tunani yayi da fad'in , "zaki fad'a min ko saina ci uban ki,"

Cikin rawar murya Hady tace "na......g....an....sh......, "

Kafin ta k'arasa ya d'auke ta da mari yana fad'in , "karya kike kenan , "

Ihu Hady tayi Dan Marin ya shige ta tace , "sai dai indai mutumin kuskure yayi yazo gidan nan." Ta fad'a jikin ta na rawa.

Yace "kuskuren uban ki , daman k'arya kike kenan , daman sharri zaki had'a mata kenan?"


Girgiza kai tayi alamun A'a,

Yace "to meye , wallahi in baki fad'a min ba saina lahira yafi ki jin dad'i."

Ja da baya Hady take tana girgiza mai kai , ganin ya juya yasa ta fice a 360 ,


Saudala kuwa tuni ya gudu d'aki ta kulle kanta tana haki , a fili tace, "tayi min sharri tana so a dake ni gashi nan dukan ya koma kanta , daman hausawa sun ce *IN ZAKA GINA RAMIN MUGUNTA* ka gina shi dai-dai kai da wata rana zaka iya fad'awa, yanzu da tuni nI yake ta jibja ."

Ajiyar zuciya tayi tace "Allah ya cece ni",

Abdul kuwa safa da marwa yake a parlourn , yana son sanin wace mai gaskiya a cikin su , in kuma da gaske ne fa?, cikin sauri ya juya ya kuma d'aukar takardar yana karantawa,

_Gaskiya naji dad'in kasancewar mu tare yau , ina fata gobe ma mu kuma mu kasance tare,  really miss u my dear_.

Sake maimaitawa ta karantawa yake yana jin zafi a cikin zuciyar sa.

Tunani yake a ransa to ai wan'nan  a waya ya dace a turo ba a rubuta a paper ba , to idan kuma salon Soyayyar tasu ce haka fa, da k'arfi ya buga table yana fad'in , " bazai yu ba , zanyi binkice duk mai Mara gaskiya a cikin su ya shiga uku". Ya fad'a yana fitowa harabar gidan.



You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 23, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SAUDALAWhere stories live. Discover now