https://www.Facebook.com/Romantic-Writers-Association-415799935882006/
💥 *ROMANTIC WRITERS ASS...*💥
*We are the star's keep shining always*💥
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲
🌴🌴
🌳😜 SAUDALA 🥴
Story & written
By
NEAT LADY
✍🏻✍🏻Dedicated to SAUDALA fan's group, kuyi yadda kuke so dashi😘😘😘
Bismillahir rahmanir rahim
3&4
Wata dariya ce ta kusa kufcewa saudala , amma sai ta danne ta cigaba da cewa
" karki sake ki fito tsakar gida yanzu, ki bari sai da safe in ba haka ba anan zaki kame har sai wani daren ,
Iya da take kwance cikin kashi kai kawai ta daga jikin ta na rawa,
Tace "in kika fadawa wani wannan abinda ya faru shikenan sunan ki gawa ,
Cikin rawar baki iya tace " kwarankwasi bazan fada ba ,
Saudala cikin tsawa tace " rife idon ki
Tsawar da tayi yasa iya kuma sakin wani kashin😂 , cikin sauri ta rife idon ,
Mikewa saudala tayi ta wata tafiya kamar aljanar gaske tana bude hannu kamar tattabara ,
Tana zuwa daki ta dinga dariya kamar mahaukaciya ,
Tace " zaki gane kuran ki iya , badai ni kika zaga ba ,
In sane nace karta fito sai da safe yadda zan kuma cin dariya 😂😂
Tashi tayi ta wanke fuskar ta ta cire kayan jikin ta ta kwanta,
Tunda saudala ta fita iya take kuka tana fadin
" shikenan karshe na yazo aljanu sun fara bibiyata , kai dole gobe nabar gidan nan dan bazan iya zama wannan aljanar ta kashe ni ba ,
Haka iya ta kwana bata rintsa ba , tana ji ana kiran sallah amma babu damar fita tunda aljana tace sai da safe ,
Karfe shida na safe saudala nata tsakar gida a zaune umman ta kuma ta fara hura huta dan daura abinci,
Iya ce ta fito kashi yana bin kafar ta duk ta bata wajan ,
Ai saudala tana ganin ta ta mike, amma sai tayi kamar bata ganta ba , kawai sai tayi wajan umman ta
Iya da bata kula da kowa ba cikin sanda take tafiya duk dan kar saudala ta ganta da kashi🤣🤣
Sai da ta bari iya ta fito sosai yadda babu damar komawa sannan tace
" kai umma warin kashi fa nake ji ,
Umma tace " nima haka saude warin ya isheni ,
Sai kam saudala ta juyo ,
Tace " lah yanzu iya kashi kikayi a kwance sai kace wata saniya ,
Ta fada tana kyalkyalewa da dariya😂😂😂
Iya ta kulu sosai tace " baban ki ne saniya ba ni ba , banxa me kan daddawa,
Saudala tace " kika kuma zagi na ,
Cikin masifa iya tace " an zage kin ko zaki rama ne ,
Saudala tace " ke dai kiji da kashin kwance ki,
![](https://img.wattpad.com/cover/196379563-288-k986378.jpg)