BABI NA SHIDA

629 24 2
                                    

🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌴🌴🌴🌴
🌳🌳
🎄

😜 SAUDALA 🥴
❣❣❣❣❣❣❣

🇳🇬®
_*ZUMUNCI WRITER'S ASSOCIATION*_📚✍🏻

[ *Zumunci mai d'orewa*🤝🏻]

*STORY & WRITTEN*
*BY*
*NEAT LADY*✍🏻

*Dedicated to my daughter Fatima*😘😘

*Bismillahir rahmanir rahim*

41&42

Inda yake kwance Saudala ta k'arasa tana dariya k'asa-k'asa.

Zama tayi san'nan ta kalle shi tace ,

"Ina ne yake ciwon ?"

Shikam Abdul gaba d'aya ya zuba mata ido gani yake anya kuwa itace? .

Abba ne ya katse masa tunani da fad'in ,

"Abdul ana tambayar ka."

Kallan ta yayi yace "me kika ce? ."

Dan k'aramin tsaki taja san'nan tace ,

"Ina ne yake maka ciwo?"

Kallan ta yayi san'nan ya nuna ma wajan idon sawun sa.

Da k'arfin gaske Saudala ta rik'e wajan ta fara murzawa cikin mugunta.

Abdul bai san lkcn da yace,

"Washhhhh".

Kallan sa tayi san'nan ta juya tace ,

" Abba kaji da girman sa yana cewa wani washh kamar ba soldier ba."

Baba ne yace "Kin san meya yake ji ne?."

Tab'e baki Saudala tayi ta kuma danna wajan da k'arfi.

Abdul ya cije baki dan yana jin zafi kawai daurewa yake.

Abba yace "to nidai bara na koma ciki Allah ya k'ara sauk'i."

Abba ya Mik'e ya fita Baba ma ya bi bayan sa.

Saudala tana ganin sun fita ta kalle shi tace ,

"Nasan zaka yi mamakin ya akayi ka fad'i ko , to nice nan na zuba maka kuka a wajan ramuwar dukan da kayi min kenan."

Kasa magana Abdul yayi ya zuba mata ido dan shi gaba d'aya ma ya manta da wani duka da yayi mata.

Mik'ewa tayi tana fad'in,

" to nidai na gama aiki na sai anjima ".

Har kusa fita ta dawo baya tace ,

" Har yanzu ina nan akan baka ta indai kayi min sai na rama."

Sallama akayi aka shigo d'akin.

Amsawa Abdul yayi yana fad'in ,

"Mubarak shigo mana."

Shi kuwa Mustapha gaba d'aya hankalin sa nakan Saudala da take jira ya bata hanya ta wuce.

Ganin irin kallon da yake mata sai taja tsaki tace ,

"Zan wuce ".

K'ara lumshe ido Mustapha yana jin yadda muryar ta ke ratsa jikin sa.

Cikin d'aga murya Saudala tace ,

" zan wuce kaban hanya!!."

Firgigit ya dawo daga tunanin da ya tafi ya bata hanya ta wuce,

"Sorry beauty wuce."

SAUDALADonde viven las historias. Descúbrelo ahora