BABI NA BAKWAI

640 29 1
                                    

🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌴🌴🌴🌴
🌳🌳
🎄

😜 SAUDALA 🥴
❣❣❣❣❣❣❣

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta sai barinta,burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_




*STORY & WRITTEN*
*BY*
*NEAT LADY*✍🏻




*Dedicated to My Fan's*🥰

*_Bazan manta da k'aunar da kuke nuna min , ina yinku nima irin totally d'in nan 💃🏻._*




*Bismillahir rahmanir rahim*


51&52



*Bayan sati d'aya*.

Shirye-shiryen biki ake sosai , ta b'angaren Abdul kuwa har yanzu ya kasa tantance abinda yake rainsa, farin ciki yake ko akasin haka oho .

B'angaren Saudala kuwa gyara take d'auka wajan Mama , Dan yanzu in ku kaga Saudala ba lallai ku gane ta , ta k'ara fari sosai har wani yellow take ,ta k'ara ciki kamar ba y'ar sha hud'u zuwa sha biyar ba .

Sam Saudala bata damu da wani aure ba dan in ba tuna mata akayi ba mantawa take.

Saudala ce a zaune tana tunanin wai ita za'a yiwa aure , a ranta tace , "Wai yanzu iskancin da 😲 malamin islamiyya ya fad'a mana anayi in anyi aure nima sai nayi". A fili tace , " Tab ni ba y'ar iska bace Aradu bazan yarda ba , in ba haka ba sai na had'a shi da Abba da Baba🤭

Da wan'nan shawara ta kawar da zancen daga zuciyar ta.

An had'awa Saudala lefe kamar yadda aka yiwa Hadiza itama haka aka yi mata .

Bayan kwana biyu

Yau ta kasance saura kwana uku d'aurin aure , B'angaren Fadila shirin biki kawai take .

Abdul kuwa baya wani shiri Mustapha ne kawai yake shirin biki.

Da daddare ana zaune a parlour ana hirar yadda biki zai kasance.

Saudala kuwa tana d'aki tana game , yunwa ta fara ji hakan yasa ta mik'e ta fito parlour, bata tsaya kula mutanen parlourn ba direct kitchen ta shiga .

Abinci ta zuba san'nan ta fito parlour ta zauna tana ci .

Mutanen parlourn kuwa banda maganar biki bb abinda suke yi, duk tana jinsu tayi musu banza kamar bata san me suke cewa ba.

Haka suka gama hirar su suka tashi kowa ya wuce part d'insa .

*Rana bata k'arya*

Yau juma'a bayan an sakko daga masallaci aka d'aura Auren *_Abdulrahman Umar Abdulrahman_* da *_Saudat Ahmad Abdulrahman_* akan sadaki dubu D'ari.

Bayan gama d'arin auren Abdul ya shigo gidan shida MMustapha, main parlour suka shiga suka tadda Hajiya Iya akan kujera an d'au kyau , tana ganin sa ta washe baki tana fad'in, "kaga ango wan'nan babbar riga haka ."

Murmushi yayi baice komai ba ya juya zai fita , muryar Fadila yaji tana cewa , "ina kuma zaka je bayan ba'ayi hotuna ba."

Juyowa yayi yace "To gani ai na tsaya." Fadila tace "kokai fa , bara a kira Saudat d'in."

Juyawa tayi ta shiga d'akin , babu jimawa ta fito tana rik'e da hannun Saudala.

Fadila tace "yauwa bro ga Saudat d'in ta fito." Yana juyowa suka had'a ido da Saudala , aikam ta sakar masa wata harara tare da murgud'a baki.

SAUDALAWhere stories live. Discover now