One

9.2K 552 12
                                    

*WADATA*
_ONE_

✍️SHATUUU

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥shatuuu095@wattpad: Vote, comment and recommend...... Ilysm

*Where's my Anty Sumayya Abdulqadir Takori? This page is yours...... Wholly yours kiyi yadda kike so dashi....Issa token of appreciation sister ♥️*

Ina zaune bakin mangal ina tukin tuwo Wanda Ya kasance na dare, Umma ce ta fito a dakin ta tace

"Ke"

kamar yadda take Kira na wasu lokutan kasancewa ta yar fari a gurinta, na juyo nace

"Na'am"

Leda ce viva a hannunta tace

" In kin gama don Allah Kai wa Rabi kayan nan kice sauran bayani mayi a waya"

nace

"To"

Juyawa tayi dakin Mama ban dai san mai ta fada mata ba na dai ga ta fito ba ledar ne kawai
Ba jimawa naji Mama ta kwada min Kira tace

"Zo Ki amsa Ki tafi"

Mikewa nayi Ina amsa mata bayan na rufe tukunyar na tafi daki, zaune kan gado na same ta tace min

"Kibar tuwon na qarasa zo kije ki dawo da wuri kan malam ya dawo yayi fada"

Kaina na gyada nace

"To"

Kayan jikina na sake na dan yi kwalliya kadan kasancewar ni ba maabociyar kwalliya bace amma ban yadda na fita fururu ba. Hijab na saka Mama dake zaune Tana bina da kallo tace

" Ke dai na rasa wace iri ce Ko ina da hijab bakya canji"

murmushi nayi kawai ban ce komi ba Se karasa shiryawa da nayi sannan na kalleta batareda na furta komai ba amma tasan abinda nake nufi hakan yasa Ta dauko dari biyu tace

" Ki hau mota amma don Allah ki dawo da wuri kar babanku ya riga ki dawowa yayi ta fada"

Murmushi nayi a raina Ina ayyana fadan Baba nace

"Inshaaa Allah"

Daga Haka na fito bayan na leka nayiwa umma sallama, Ina fita na hau Napep zuwa unguwar tishama inda anan gidan Aiken nawa yake, Tun a zaure yaranta suka tare ni da murna suna fadin Aunty oyoyo na rungume su baki daya
Yaya Rabi dake kicin ta jiyo hayaniyar mu sai ta leko tace

"Aw! Ashe kece na xata Fati ce da suke ta wani murna"

murmushi kawai nayi don na gane nufinta bana xuwa gidanta ni kuma yawo bai dame ni ba kwatakwata, Dakinta muka nufa muka xauna kan kujeru ta dauko kudi ta ba babbar yarta Amira tace ta anso man ruwa a shago
Sai da muka gaisa nace

" Gashi inji Umma tace sauran bayani sai a waya "

Ta amsa tana fadin

"KO da naji ni dai masan ba don Alla kika xo ba. Ke kam Allah ya shirya ki kan kin xumunci in kin yi aure bansan ya xaa yi ba"

Hakan yayi dai dai da shigowar Amira da ruwa a plate na amsa nace na gode tare da mika mata ledar biscuit da Mama ta bani nace

"gashi inji Mama"

suka amsa tare da godia, mun dan taba hira take tambaya ta yaushe xan koma skul nace Mata sai lahadi ta sama tace Allah ya kaimu nace amin
Biyar dai dai nace tafiya xan yi tace

" Kin isa ma !"

nace

"Allah yanxu ma kimga fadan da su Mama suke wai kar na zauna har Baba ya dawo yayi fada "

WADATAWhere stories live. Discover now