TWENTY SEVEN

2.2K 308 34
                                    

*WADATA*
    _Twenty seven_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad

*Farida Akilu, Salma Alhassan, Hauwa Hamisu, Halima Abubakar and others..... The page is yours*

Zaune yake a office, aiyukan hannunsa yake so ya kammala na settling exams questions dinsu saboda a cikin satin nan yake da burin yayi submitting komai. Wayar sa ce ta fara ringing ya kai duban sa kan screen din, Sunan Rahama ya gani kamar ya share amma sai ya fasa bai san dalilita na kiran shi ba. Don haka ya daga wayar, Gwaggo Hafsu ce ta daga ya gaida tace

"Dama jikin Rahmatu ne ya motsa gamu nan zamu tafi asibiti"

Yace

"To da kin bari Gwaggo yanzu da nazo na kai ku"

Tace

"A'a kayi aikin ka yanzu zamu je mu dawo ba zai wuci juyin yaro bane"

Yace

" To kudi fa?"

Tace

"A'a duk yadda ake ciki zaka ji"

yace to. Kana ya kashe wayar. Duk yadda yaso kammala aikin amma ya gagara gani yake ai ya kamata ace yaje yaga jikin nata, don haka bai ma gama ba ya rufe office ya taho gida. Sai dai ba kowa, wayar ta da ya kira not reachable. Yana nan har hudu bai samu wayar ta ba, kawai ya tashi yayi sallah ya kuma tafi ya dauko su Amatullahi a makaranta, da suka dawo yasa sukai wanka. Cereal ya hada masu da suka riga suka horu da shanshi matsayin abinci su. Har magriba basu dawo, sai gabannin isha sai gasu sun dawo ko sannu da zuwa bai yi musu ba yace

" Ina kuka shiga haka?"

Gwaggo Hafsu tace

"Allah sarki Sulaiman nasan kana ta neman mu, da muka tafi sai naga abin ba na asibiti bane don haka kawai sai muka tafi gurin mai magana gashi yanzu ya bata saiwoyi"

Takaici bai barshi yayi magana ba illa iyaka kawai yace Allah ya kyauta. Hannun su Amatullahi ya kama ya wuce dasu daki, Gwaggo Hafsu ke ce masa kudin fa bai juyo ba yace zan bayar.
Alwala yasa suka yi ya koya masu home work, kana suka canja kaya zuwa na barci. Suka yi addua ya kashe masu fitila. Dakinsa ya tafi yayo wanka shima yazo yayi sallar isha dinsa. Kana ya taba aiki har zuwa sha daya, dakinta ya tafi tana zaune tana shafa mai ya shigo bai ce da ita komai ba ya hau gado itace tace

"Wai me ya faru ne naga sai wani cin magani kake?"

Nan ma bai ce mata komai ba tace

"To dama kudin mai magani dubu shida Gwaggo ta bashi biyu sauran hudu kuma gobe zaa kai masa Gwaggo ta zare kudin ta"

Yace

"Ba dai nace zan bayar ba to ki rabu dani"

Tace

" Ai ba wuyanka na rike ba nima kawai dai na fada maka ne kafin gobe kayi wannan ficewar wurin da ka saba"

Yace

" Zan fita da wuri kudi kuma zan bayar amma duk ranar da cikin ya baki matsala ki kuka da kanki"

Se tayi dariya tace

"Yanzu kayi magana, ai kace kawai haushi na kake ji kuma insha Allah haihuwa, yadda na samu ciki cikin yan mintuna haka zan haife shi cikin yan mintuna"

yace Allah yasa.
Yana jin kunkunan ta amma yayi banza da ita har ta hayo gadon ta kwanta abinta.
  Da safe tun wuri ya tashi ya tada su Amatullahi suka yi sallah da azkar sukai wanka dukda abin seda dubura amma Haka suke dagulawa, Tea ya hada masu da bread suka ci tunda mutanen gidan basu tashi ba, ya dauko masu lemo da cookies sai ruwa na tafiya makaranta. Ya fito ya iske Nasir zai kai su Aisha makaranta sai ya amshi su Amatullahi suka tafi tare dasu.
Gida ya dawo ya dan kwanta. Sai tara ya tashi ya shirya ya fito, ita da Gwaggo ya samu a parlour suna cin jallof din shinkafa da duk safiya suke ci, shi ko inda abinda da ya tsana bai wuce ta ba. Ita ke ce masa baka ci abinci ba fa yace kar ki damu zan ci office tace to ba tare da wata damuwa ba. Aljihunsa ya zura hannu ya dauko naira dubu bakwai yace gashi ta amsa ta kirga tace dubu bakwai yace good, kudin magani da cefane tace to. Sallama ya masu yasa kansa ya fice.
  Sai da ya kammala aiyukan sa na yau gaba daya sannan ya yi submitting questions din, yana da meeting don haka Rahmatu ya kira yace taje ta dauko su Amatullahi a makaranta tace to. Meeting din sai karfe shida suka kammala, an zabi wanda zaa tura can Egypt Al-azhar University don yin wani seminar na sati daya Allah cikin ikon sa har dashi aka zaba ba wata murna yayi sosai ba don kwanan baya son nisa da gida saboda yaransa da kuma matsalar cikin gidansa.
Ranar litinin kam jirgin su ya tashi, ya bar masu komai a gida mussaman na haihuwa don a lissafin sa cikin ta yana wata na tara duk da dai taki zuwa awo harta da ragunan suna biyu manya manya ya bar masu, da kudin cefenen suna.
Kwanan sa biyar aka kira shi wai ta fara labour yace to su je asibiti amma Gwaggo Hafsu tace A'a ba inda zasu tafi maza su gane ta yace to bara ya ma wata nurse magana tazo tace wai A'a itama zata iya. Abu kamar wasa har kwana biyu bata haihu ba kuma ba sun ki yarda aje asibiti ko da ya kira mahaifiyar ta ma amsa daya ce.
An so ya sake kwana amma yaki, bai biya ko ina ba sai gida. Kallo daya zaka mata ta baka tsananin tausayi amma a hakan sun hana a kaita asibiti dakin ba abinda yake banda warin jikon saiwa sai kuma turaren hayaki wai na haihuwa. Bai san lokacin da ya kinkime ta ya kai mota. Gwaggo Hafsu ta biyo shi tana fadin ina zaka kaita ba dai gurin mayun man ba? Yace kar ki damu ba ita zan kai ba dana kawai zaa cire min na baki yar ki.
Asibitin mallam ya wuce da ita sai Labor room kamar yadda ya zata ko haka abin yake har tama zarta don kuwa ya sha fada kamar zasu buge shi ba doctor ba nurses ba bai kuma ga laifin su kowa aka ma haka zai ji ba dadi ba ta da wani record tunda bata antenatal don haka komai kawai yi mata akai  haka Allah da rahamar sa da suka dan daura mata ruwa da allurai sai karfin ta ya dawo da kyar ta samu ta haifi yar babyn ta mace wadda itama ta cigita. Daga nan kuma sai jini yace a bashi wuri. Duk dubarar su da kyar aka samu jini ya tsaya mata. Sai kuma aka taho neman jini Allah ya taimaka nashi yayi match ya bata leda daya aka samo donors suka bada Sauran pint biyun, Itama baby sun caje ta sai dai ta wahala ta kuma sha ruwan saiwoyi a ciki dole sai an zuke wani daga ciki. Sai da aka gama itama aka yi (SCBU) wato gurin kula da yara masu matsala.
Sai da ya gama biyan bill da ya jijjiga aljihunsa kana doctor da wata nurse suka bi ba'asin ya aka yi haka ta faru bai boye komai ba ya fadi masu sun kuma tausaya masa. Metron ta sha alwashi na gyara.
Inna ya fara kira ya fada ma haihuwar da aka yi da safe. Tayi murna ba adadi, gida ya koma sai da yayi wanka kana su Amatullahi suka fado masa ya san basu wuci gidan Nasir ba don haka can ya tafi.
Sai da aka masa izini kana ya shigo duka suna parlour yara na ta wasa su kuma suna ta hira, sai yaji ina ma shine ya more aure haka? Su Amaturrahman na ganin shi suka yo kanshi da gudu. Nasir ne ya fara tambayar sa ya mai jiki? Yace

"Ta sauka da baby girl amma dukkan su ba lafiya suna kwance"

Cikeda tausayi yace

"Subhanallah  Allah ya basu lafiya, wallahi aboki har gidan muka je saboda a akaita asibiti amma wannan Gwaggo tata ta hana dole muka hakura sai yaran kawai muka dauko"

Yace

"Ba damuwa aboki na gode sosai nima Allah ya ara min ranar da zan kyautata maka"

yace ba wani abu, Sauda ce ta kawo masa abinci yace madam abincin nan na koshi kawai tace haba dai yace Allah. Duk yadda suka so yaci amma yace ya koshi, ba wani jimawa yayi ba ya tafi abinsa su Amatullahi ma gidan ya bar su yace idan komi ya lafa zasu tafi.
Gida ya dawo zuciyar sa a cunkushe. Hakan nan ya kwanta kan gado ya kifa kansa kwai sai ya tsinci kansa da kuka. Sosai ya dau awanni yana yi kamar wata mace abinda bai taba ba kai shi ba zai iya ma tuna last hawayen da ya zuba a idon sa ba. Sai da yayi mai Isar sa kana ya tashi ya dauro alwala nafilfilu yayi tayi in ya gaji ya karanta alqur'an har asuba tayi yayi sallah kana ya dawo gida. Dan jiri jiri yake ji don hhaka kitchen ya shiga ya dauki mug ya juye maltina da madara peak ko wani gwangwani daya ya juya ya shanye. Daki ya tafi ya hau gado sai barci mai nauhi ya dauke shi wanda a ciki ya yayi mafarkai da dama da Aishan shi.
Sha daya ya tashi yayi shiri, makaranta ya je don bada excuse dinsa. Ya kuma yi saa Nasir har yayi reporting abinda yayi masa dadi sosai. Karfe biyu ya tafi asibiti, zuwan sa mutanen yan leman dana Adamawa har sun karaso, ya sha fada gurin Inna da Gwaggo Hafsu ta gama mata famfo wai baya kula da su jiya gaba daya bai kawo abinci ba sai yau da matar abokin sa ta kawo. Nan ko Inna ta kara hawa da wadda yake so ce ai da anan zai kwana yana jinya. Bai dai ce mata komai ba har ta kammala ya bata hakuri. Number din Dr. Ya kirawo shi yayi masa jagora har dakin ta har yanzu barci take bama tasan wake kanta ba, ta sake fari ta washe sosai dankwali kanta ya zame manya manya kalba dake kanta guda shida duk tsagun hade saboda yadda ake yawan zuba ma kan ruwa. Tabbas Rahmatu kyakkyawa ce asalin fulanin Yan leman da Yola sai dai ba hali ko kadan. Baiga babyn ba saboda staff ne kadai ke SCBU.
Restaurant yaje yayi masu order ya kawo masu suka ci. Kwanan ta biyar ta ware amma sai da ta kara sati tana jiran baby kana suka sallame su da gargadi mai yawa.
Nan ne kuma kurar suna ta tashi sai ya bada kudi na cefane ba kunya Gwaggo Hafsu tace kudi an yi magani raguna kuma an ba mallam zai yi sadaka dasu ai bai san sa'adda ya dankarawa malam din ashar ba ya kuma ce sai dai suyi sauran hidima a aljihunsu don shi bashi da sauran kudi. Yarinya kam yayi mata huduba da Aisha nan ma wani masifar ta sake tashi a gidan abu har  da Gwaggon ta ma a ciki kada ma Inna taji labari don tamkar zata Ari baki tayi magana. Ala dole ya canja suna ya maida mata kamar yan uwanta wato Amaturrahim. Da suna Inna ta fiffike Ido tace sai ya sake yin komai haka kuwa ya sake yi din ba yadda ya iya.
  Ranar suna ma sai da aka sha rigima tsakanin su Wasila da kuma dangin Rahmatu akan su waye zasu yi suya da kuma rabon abinci, ba kunya Gwaggo tace ai kowa ya sani dangin mace su ke da gida ranar suna don haka su ja gefe duk yadda ake ciki zaa fada masu abin ya taba ran Inna amma bata nuna don tasan indai masifa ce to Lami ta dama ta ta shanye sai dai ta zuba. Aiko sun ga wulakanci abinci ma zubo musu shi aka yi su duka a tray guda biyu sai ruwa da kullin zobo kowa dai dai.
  Da aka gama suya wannan raguna manya guda biyu aka raba hanji gida hudu kaso daya na mai jego rabin kaso daya kuma na miji daya da rabi na dangin mai jego daya kuma na dangin miji da matan unguwa kowa aka kulle masa a farar leda har Inna aka basu. Inna har da kwalla yau ita aka bawa naman sunan gidan danta a farar leda yanka gudu uku, abinda ta saba nata a katuwar samira ake cika mata har tayi rabo amma yau ita ke rabawa.
Washe gari suya nan ba wanda aka ma tayi yaron Zinatu ne yaje ya dau yanka daya aiko ya sha duka gurin Gwaggo Hafsu. Hakan yasa Zinatu fitowa ta fara bala'in da aka saba kafin kace kanzil gida ya rikice da masifa ko ina ana jinsu. Fada sosai har matan unguwa sun fara shigowa ganin kwaf! Inna yau kukan a fili aka yi shi tana fadin

"Lami yau ni zaki wulakanta jini na akan tsokar nama daya? Duk halarcin da nayi maki?"

Gwoggon Rahama Tace

"Hallaci? Hallaci sai dan halak Sumaye amma ba dai ke ba, yaro ai mijin tane ko ta ina sai ta aure shi kuma baki isa ki hana ba"

Zinatu ce tace

"Ke jahilar banza uwar tawa kike zagi.……"

Rahmatu ce ta kama ta tana nuna

"Inna tace ga jahila nan amma dai ba uwata ba."

Aiko Wasila ta tsinke ta da ita mari itama ta rama, kan kiftawar ido ko sai dambe. Inna ce ta zube nan sumamma. Nan da nan ko su Wasila suka yo kanta.
Wayar Sulaiman dake bakin window suka shiga kira yana kallon su a ransa yana jin dadi da hakan ta faru. Kin amsa wayar yayi illa jallabiya da ya zura ya bar gidan ta kofar baya ……………

Yours Truly
Shatuuu

WADATAWhere stories live. Discover now