THIRTY

2.2K 307 33
                                    

*WADATA*
_Thirty_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad

Ganin haka jikin yan uwan yayi sanyi, Zahra ta silale ta kira uwar su. Ai ko sai gata a fusace janye ni tayi tace

"Malama lafiya zaki kama man yarinya da bugu?"

Nace

" Su kara man rashin kunya su gani saa kika yi ma da duka kawai na mata ban fasa bakin ta ba"

Tace

" Dako baki sake ba wallahi don wallahi sai kin kwana hannun hukuma"

Nace

" Ashe ba zaki iya daukar mataki da kanki ba."

Mufida ce tayo kaina wai sai ta rama nace zo da alama dukan bai ishe ki ba sai nayi maki wanda zaki kasa tashi ne.
Waya Sa'adatu ta dauka ta kira Bashir. Hello Daddy...... Wani lafiya matar ka tana nan zata halaka min yara na.......... Ni dai kawai kazo. Ta kashe wayar. Ina nan zaune ina jiran zuwan sa, Kamar minti ashirin sai gashi yazo a hargitse shi me 'ya'ya, su kuma sai wani kuka suke ya tambaye ta me ya faru ta fara tsaro masa gaskiya da karya da ta gama ya juyo gareni yana fadin

"Yaya aka yi?"

Nace

"Abinda ta fada maka gaskiya ne kuskure daya tayi da bata ce maka kashe su nayi ba zuwan ta suka farfado."

Yace

"Duk ba wannan ba, wai ke me ya hau kanki ne?"

Nace

" Abinda ya hau naka kan"

Yace

" Ni Kike gayawa haka? Saboda ke gidanku ba manya"

Da sauri na mike tsaye nace

"Ni da kai dai saboda kai ma da da manya gidanku da baku yiwa 'ya'yan ku tarbiya haka ba, kuma da kannen iyayen ka suka maka magana da baka yi fatali da ita ba"

Shiru yayi bai ce komai ba. Nayi wucewa ta na gane su kawai nima magana zan na sakar musu wata kila a zauna lafiya kawai.
Da dare ko sai gashi wai bai ji dadin abinda nayi dazu ba nace to a kiyaye gaba. Yaji mamakin magana ta shine ya zauna kusa dani yana matsa kafata yana fadin

"My Eesher gaba daya kwanan nan kin wani koyi fada why? Har da nima mijin ki"

Ban ce masa komai ba ya karaci surutun sa ya fice ya bar ni.
Da safe naje na zana final exam dita cikeda farin ciki Yau dai Allah Ya nuna min karshen Paediatric nursing Wanda Haka kurum nake sonahi to gashi na kamalla. Gida na dawo a nan na iske shi wai ya samu wata letter daga Federal government zaa tura shi Malaysia na wata tara in yayi qualifying zai zama SAN. Na tayi shi murna sosai don yace jibi zai tafi.
Ranar a kasa ya wuni gaba daya suka fice ban tambayi ina suka je ba, washe gari ma haka. Ni kam shiri nake sosai, nayi masa doughnut, chin chin sai dambun nama na kaji guda shida da Plain Vanilla cupcakes. Ranar sai wani dadi yake dani abun da muka jima baa samu ba.
  Washe gari da sassafe ya tashi na yi masa duk abinda ya dace na dauko masa kayan da nayi masa. Nace gashi ka tafi dashi guzuri yace duk wannan wahalar har kinsa na sake jin kunyar ki nace kunya kuma Yallabai yace eh.
Yar dage nayi na masa kiss a kumatunsa nace

"I'll miss you"

Yace

" I'll miss you more.......akwai sako nan na bar maki hannun Sa'adatu zata baki"

Na bata rai nace

"Me yasa baka bani a hannuna ba? "

Yace

WADATAWhere stories live. Discover now