TWENTY FIVE

2.2K 265 22
                                    

*WADATA*
_Twenty five_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad

MamanMaimoon Take the page Anty...... I heart you big

Da Yamma naga abinda suka rubuta ni ban san shi ba sai kawai na yanke shawarar na san abin yi. Da suka dawo na saka su suka yi sallah, duk abinda na san zan dauka na diba nayi sama. A parlour na na basu abinci suna ci muna ta hira har na taimaka masu suka yi home work abinsu. Da muka yi sallar laasar na saka su muka yi azkar tare na lura ba wani iyawa suka yi ba na gyara masu.
Kitchen na tashi na shiga, cous cous na yi niyyar turarawa tare da kayan vegetables, sai kuma yar sauce ita ma na dora. Na yi pineapple juice da kuma coconut drink. Kan magriba na gama komi cous cous ne kawai ya rage. Wasu manyan warmers da Mama ta saya min jikinsu silver murfin kuma glass na juye sai salad tray shima nasu na juye a ciki. Wanka na shiga na fito na shafa mai, kitchen na koma na iske yayi na juye shima a flask. Zahra ce ta shigo tayi kiran su Islam suka shigo suka ce min sun tafi nace to kuyi ma Mummy sannu da zuwa. Suka ce to.
Ana sallar magriba na fara tawa ban idar ba naji shi ya shigo. A gagauce yayi alwala ya fice masallaci. Nima da na idar bedroom dina na wuce na dauke kayan da na turara jikin kabbasa da incence burner. Riga ce da skirt na material sky blue gaba daya sai aka sa min kwalliyar cin baki da navy blue. Kwalliya nayi sosai na kashe daurina na jan magana. Turare na sake ma jikina bari. Na jujjuya gaban madubi ni kaina na san nayi kyau sosai.
Dakin Bashir na nufa, shiga ta tayi daidai da fitowar sa a wanka. Tsayuwa yayi yana kallo na sai da naje na bushe masa ido nace

"Wannan kallo haka Yallabai ko kwalliyar bata yi bane?"

Ajiyar zuciya yayi yace

"Subhanallah! Tabarakhallah ko ban taba gode ma Allah ba, dole na gode masa yanzu da ya axurta ni dake"

Se da nayi fari da ido kafin nace

"Kai Yallabai yabo ko zagi?"

Yace

"Bara dai na shirya I can't wait to........"

Ya kashe min ido nima nayi masa murmushi da ya sukurkuta shi.
Gaban Mirror dinsa naje na dauko mai nace to zauna. Da kaina na shafa masa mai, na shirya shi, jallabiya ya dauko nace ba zaka sa jallabiya ba nima kwalliya zaka min. Kananun kaya na dauko masa da kaina na saka masa. Rungume ni yayi yace

"I love you so much My Easher"

nace

"I love you must Yallabai."

Kiran sallar isha ya katse mu ya sake ni gami da yi min rada nayi dariya tare da cewa sai na duba.
Sai da nayi sallah, na jera abubuwan bukata. Na tafi na jera su a dining table. Lokacin yayi dai dai da shigowar sa, hannu na ya rike muka shiga part din Sa'adatu suna zaune wasu na sallah su Islam na kallon cartoon. Tare muka zauna kan kujera dashi yace da mufida

"Ina Mummy?"

Tace

"Tana ciki"

Yace

"My Easher bara na kira ta,"

da ido nayi masa far alamar jeka, shima yayi dariya.
Basu fi minti goma ba suka fito, tana sanye da wata doguwar riga mara nauyi, kanta ta daura mayafi, da ka ganta kaga hutu da gayu. Sai da ta fito tace min

"Sannu da gida Aunty"

Nace

"Yauwa kun dawo lafiya?"

Tace

" Lafiya kalau."

Tare muka gurfana a dining ina makale kusa da mijina. Nayi ma kowa serving ni kuma na hade mana tare da shi, na kuma lura duk sakin fuskar ta ta dan canja yanayi, nima ina so taji abinda nake ji. Da tai laumar farko tace

WADATAWhere stories live. Discover now