EIGHTEEN

2.5K 297 27
                                    

*WADATA*
  _Eighteen_

✍️WADATA♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad

⚠️Not edited, read at your own risk, ignore the mistakes plxxxxx.

Daki na dawo na kwanta kan gado Mama tana sallah. Ba abinda yafi damu na irin yadda Baba yace ko ya mutu kar na koma gidan Sulaiman duk da nasan har abada bani ba shi amma fa abin ya tsaya man a raina sosai.
  Da safe na gyara kayana deep freezer din da ya saya min na ware nace a maida masu ai ba tawa bace shi ya saya. Kaya na da yawa babu, amma ban ce komi. Yaya ya amshi kayan ya kai man gidansa ya aje abubuwan da baza su lalace ba. Gado na da wardrobe na kafa a dayan dakin Mama na tashi nawa bedroom din. Kujeru na kuma na bawa Baba.
Kayan saka ta ma har su na hado abuna na ci gaba da abuna.

A kwana a tashi na kammala idda ta abinda ya rage man shine na cire son Sulaiman da tunanin sa cikin raina. Result dina ya fito alhamdulillah banda matsala sai shirye shiryen service kuma. Abinda muka shirya da Sulaiman ba zan yi ba zai man cuku cuku. Da yan kudade na na saka da Wanda Sulaiman ya bani na idda na hada muka tafi da Rukayya kasuwa na yo sayayya har da ta kayan saka ta. Ina jinta suna waya da Ahmad bayan ta aje nace rukayya tace na'am nace sai yaushe zaki cire Ahmad ne a ranki bayan kin dai ji irin furucin da Baba yayi ko? Tace Yaya Mami ina son Ahmad ne sosai nace I know danne zuciyar ki zaki yi koko kina tunani in ma Baba ya yarda mahaifiyar shi da yan uwanshi zasu bar ki ki zauna lafiya? To gara tun farko kuma kanki fada ki kyale shi. Allah zai kawo maki wani tace to.
Na dora rayuwata kan hakuri akan duk kalubale da ya same ni. Na dangana lamura na ga Allah, don shi daya zai tsaya man. Yara na basu fashi duk sati suke zuwa gurina. Anan nake sanin halin da suke ciki, Sulaiman da Sauda na matukar kokari Kansu a raina nace ai ya dace da uwa. Don in banda dace yaushe uwa zata so yaron ta ya sha wuya. Gaba daya shi yake playing role dina da nashi in banda Sauda tana basu abinci. Muna kuma waya da ita amma bata taba nuna mani ga wahalar da take masu ba sai dai ni ina mata godiya ban kuma taba mantawa na saka ta a addua ba. Tun su Amatullahi na tambaya ta yaushe zan koma har suka hakura suka rabu dani.
  
Yau na shirya zan je can gidan Amina Bello tun last week take kira na wai tazo kano nace to zan zo. Cikin doguwar riga nake ta material milk da maroon. Pure cotton ce mai mayafi yar saudia Mai kyau. Ta amshi jiki na sosai. Flat din takalmi nasa sai yar purse. A tsakar gida na samu Mama nace mata na tafi tace to nace ko kudin mota? Tace uhhm! Wannan kyau in kin hadu da siriki na ya biya maki. Murmushi kawai nayi na tafi.
Drop din adaidaita sahu na dauka har gidan ta dake can Abdullahi Bayero Road. Farkon layin take na sauka.
Ita na fara gani da cikin ta a gaba tana cin abinci, da sallama ta na shiga ta amsa nace sannu uwar mata daga aure sai ciki. Tace to ya zaa yi ai a gunki naga salo. Dariya muka yi tace ina tsaraba me kika riko min nace babu komai tace kin isa ma yadda kike samun kudi nace nice ma ke. Tace to ki ce aiki saki sha dama yanzu Umar ya fita sai ya dawo zai man girki amma tun da kunzo kya ki man. Nace ba matsala. Mai aikinta ce ta kawo min ruwa da lemo nace Amina you've changed completely tace to yaya zaa yi na gama cika burin duniya ina tare da Umar dole nayi kyau nace haka ne tace ina kids ina? Nace suna gurin babansu tace kai haba nace Allah tace Allah ya kyauta ke kuma ya kawo maki miji na gari nace amin. Tace ko Umar dina zan baki? Dakuwa nayi mata nace you're not serious.
Ranar kam tayi man dadi sosai. Nayi nishadi da na dade ban yi irin sa ba. Ina son Amina sosai. Sai da nayi sallar laasar bayan nayi mata girki na gyara mata gida don cikin ta ya tsufa da yawa nace gaskiya zan so naga ranar da zakiyi crashing tace ai ko baki gani don ko metron dinku tayi kadan nace ko? Tace yadda muka dama furar mu ni da Umar hakan zamu shanye nace zaki shanye dai shi kam ai sannu ne nashi. Tace ai mu na daban ne nace haka ne.
Da kyar ta bar ni na taho bayan ta bani tsaraba tace min saudia suka je da Dubai shine tayo man tsaraba na ko ji dadi. Kafin mijin ta ya dawo har na tafi.
Ina tsaye titi ina jiran adaidaita sahu. Wata mota ta gifta sai gata kuma ta dawo, Da muryar mai maganar na gane shi yasa na juya Aunty Maijidda ce ke driving sai Anisa  gefen ta. Da murmushi na karaso nace Aunty na ta kaina tace ba wani nan nace da gaske tace shi yasa kenan kika kasa nema na nace kiyi hakuri tace naji.. Yanzun ma daga asibiti muke Shukhra muka kai kuma na rasa mai daura mata drip sai gaki Allah ya kama min ke nace to. Ba yadda zan yi dole na shiga. Naga dan qaramin yaro kwance nace Anisa kin haihu ne? Uhhm kawai tace man nace ALLAH sarki akan Sulaiman dai ke kin yi aure ni kuma ya sake ni kuma sakin da ba kome to meye abin kishi ? amma a fili kuma nace Allah ya raya tace amin. Baby din kam kyakkyawa dashi. Nace sannu Shukhra.
A can bedroom dinsu na sama muka je. Magunguna da allurai nace amma me yasa baku tsaya an sa mata can asibitin ba? Tace wallahi gaggawa ce ta hana ni ga emergency din very noisy mutane an cika nace wanne? Tace nassarawa. Na kulla mata drip din bayan nayi mata allurai a ciki. Ba jimawa ko ta fara barci Aunty tace sam mazan zamani ba hakuri tun aure ake fama ya bar ta nan amma yace A'a yayi ta yawo da ita yana morewa sai yanxu da bata da lafiya zai san aikinsa na tafiye tafiye ne, murmushi nayi nace dama sai hakuri. Mun dan taba hira nake tambayar ta ina Ummi? Tace wai fa jumping baban ta yayi mata yanzu ss 3 take can Turkish ta Abuja wai baya so ta wuce sixteen years bata gama makaranta ba nace OK. Kaya na na dauka nace tafiya fa zan yi Aunty tace haba dai kin isa ma nace don Allah ki bar ni tace na dai gane laifin wani ya shafe mu ko? Ni na dauka ai mun zama daya har abada nace haka ne Aunty bana so Baba ya dawo ya same ni a waje tace in kin ce masa nan kika zo sai yayi fada? Nace Baba fa yayi man sharadi kan yan uwan Sulaiman... Idona ya kawo ruwa na ci gaba nasan kina da labarin duk irin abinda yan uwan Sulaiman suka yi min har da kawo man kayana gida? Hawaye na ta share tace duk na sani ki kara hakuri Allah duk yana tare da mai yinsa. Na gwada mata yadda zasu cire mata da zan taho har da turare ta bani. Ta sani a adaidaita tunda naki shiga motar gidansu. Allah kuwa ya taimake ni Baba bai riga ni dawowa ba.
Sai da nayi sallah naga tsaraba ta. Dogayen riguna ne guda biyu Arabians masu masifar kyau. Sky blue sai kuma baka sai turare na Kala biyu duk na "Jannah" sai al-bahrain. Da takalmi daya. Sai alawoyi na bawa yara. Aunty Maijidda ma ta bani turare da muski na kuma ji dadi a raina Sosai. Alawan na fitar na bawa kowa a matsayin tsaraba na kuma nuna ma Umma da Mama abinda Amina ta bani.
  Washe gari kam da wuri na tashi na fara saka. Amina nake yi ma baby layette na kayan sanyi set biyu har da zanin goyo. In ta haihu zan kai mata.

Cikin satin ko Allah cikin ikon sa ta suntumo mana baby girl. Ni ta fara ma waya ta fada mawa. Shi yasa ko tara har na bar gida. Anan gida ta haihu, ita da Umar dinta. Zuwa na ko gyaran gidan basu gama ba. Ni na taya shi muka gyara gidan tayi wanka nayi ma baby wanka. Sai wani tayi lakwas da ita na dan ga alama taji jiki. Tea na hado mata da bredi nace taci kafin na sama mata wani abu. Suna rungume da yar su abinsu, sai nan nan Umar yake da ita hakan nima ya tuno man da rayuwata gidan Sulaiman. Waya ya shiga buga ma yan uwa da abokai kan cewar fa sun haihu. Abinsu abin dariya gaba daya basu da kunya shi da Amina.
  Gyada markadaddiya na dauka nayi mata kunu na dora mata farfesun kayan ciki. Kafin na kammala gida ya fara cika da yan barka ta ko ina. Dana kammala na kai mata daki suna tayi min sannu da yake yawan ci duk na san su wasu kuma lokacin biki muka saba dasu. Taci sosai don har ta ba yarinyar ta nono.
  Ni na zama uwar gida mai masaukin baki ranar. Don ni nayi ta dawainiya da mutane, sai dare yayar Daddy dinsu tazo daga Kiru don itace zata zauna da ita. Nan ma sai da nayi mata tuwo na sake dama mata kunu ina fadin ki dai rika ci a sannu in ba haka ba zaki bude cikin ki da yawa.
Umar har da roko na na kwana nace A'a gobe dai zan dawo. Shi da kanshi ya kaini gida.
  Haka na jera har sati kullum zan je mata na yini sai dare Umar ya maida ni gida, ni ke dafa mata duk abinda zata ci ita da mijin ta, da sauran yan barka sai dai in yan barka sun zo su taya ni. Tabbas Amina mutum ce rayuwar da muka yi a makaranta har kawo dawainiyar da tayi dani lokacin biki gaskiya dole a jinjina mata. Shi yasa ban taba gajiya da yi mata dawainiya ba. Gwaggo ta Kiru ma na yaba min sosai tana cewa sannu ke dai yar nan, kina wahala da yawa damu. Allah yayi maki albarka na kance amin. Wani lokaci in sun yi fada da Amina akan wanka tayi ta mata tsiya tana cewa ke kam baki halin kawar ki ne? Komai naki raki Amina? Allah dai ya shirya ki.
Ana ya gobe na zo da niyyar kwana ranar kuma na taho mata da kayan sanyi na bata tako hi dadi sosai don gefen ta ta aje su duk Wanda yazo barka ta nuna masa.
    Mun yi snacks ranar, an hada da juice, dabino, biscuit da yajin daddawa an jefa cikin jakar soveniours da jotter wadda zaa raba ranar suna.
A dakin da aka ba Gwaggo nan muka kwanta tare don jinin mu yazo daya da ita. Ta tambaye ni ina mijina nace mata ai banda aure ta cuta abin sosai tana ta mita akan irin rayuwar auren yanzu. Har da bani irin labarin zaman su da kishiyoyi nasu. Na kuma dau darasi sosai akai.
Ranar suna baby taci suna Maryam. Tun safe ake hidima kowa yaci kwalliya abinsa nima nayi kwalliya. Wasu Sabin kayana nasa riga da skirt ne na Lagos lace sky blue nayi kyau sosai abina. Mun sha hotuna sosai don yan makarantar mu sun zo sosai. Husna dai bata zo ba ana can Benin ana service. An yi rabo sosai suna yayi armashi kowa ya watse cikin farin ciki. Gwaggo tasa na kulla hanji na jefa cikin ko wace jaka don wani in ya tafi not possible nama ya biyo shi.
  Washe gari sai da muka gyara gida na aje mata komai yadda yake nace to ni fa tafiya zan yi? Tace haba dai! Nace Allah da gaske tafiya zan yi ba wasa tace to. Don tasan ko tayi magiya tunda na niyyata ba zan zauna ba. Ta bani naman suna na kaiwa su Mama ta kuma bani turmin atampa da sinkin sabulu nace A'a bani amsa. Gwaggo ta matsa dole na amsa ba don raina yaso ba. Umar ne ya kai ni har gida.

WADATAWhere stories live. Discover now