TWENTY NINE

2.3K 293 26
                                    

*WADATA*
_Twenty nine_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad


Da suka gama na gyara ko ina dakina muka tafi muka kwanta ina tsakiyar su tun suna muna hira da hausar su mara dadi musamman Amaturrahman har suka yi barci. Na gyara musu kwanciya nayi musu addu'a. Kasa na dawo sai sabon kuka, wata kila ni kuma haka zan kare ban yi dacen aure ba, ga wasu can uba daya wata kila shima wannan dana haife shi Bashir ya sake ni na yi wani auren sai a fara lissafa min aure da kuma yara. Ranar ko sallar ma na kasa a kwancen nan nayi addu'a ta don nasan a ko wani hali nake Allah yana jina. Sai asuba na lallaba nayi sallah na tashi su Amatullahi suka yi sallah tare muka yi azkar dasu, kana muka koma barci. Kafin na tashi har sun tashi. Tashi na wai suna kasa, ina zaune parlour na ma mance ashe fa wai yau ake sallah ko? Sam ban ji hayaniyar su ba. Na tashi nayo wanka kafin na fito har sun dawo tare da Islam, ita ke ce min

"Aunty kinyi barci su Amatullahi suka zo Mummy tayi mana wanka muka je masallaci da ita a motan ta"

Nace Sannun ku da zuwa.... Na juya gare su me zaku ci ita tace sun sha cornflakes gun Mama wai sun ki cin abinci nace to kice mata na gode. Suna ta wasan su na shirya. Wayata na dauka na tura ma Yallabai message
    Assalamu alaikum. Da fatan kayi idi lafiya, Allah ya amshi ibadun mu ya maimaita mana. Ina so zan fita dasu Amatullahi zan je ziyarar sallah.
Ba jimawa ko ya turo min reply da cewar
    A'a kar ki fita ko ina.
Karantawa kawai na aje wayar. TV na kunna musu suna ta kallon MBC 3. Ni kuma ina nan zaune gefe, material ne jikinsu mai kyau background din baki sai fulawoyi pink jiki yayi kyau sosai. Ba laifi naji dadi abinda tayi musu mai da mahaukaci.
Ina sallar azahar Islam ta shigo wai su zo inji Daddy, Amatullahi ce tace mata bara na idar da sallah tace kuyi sauri park zamu je da gidan Hajiyan Zaria (Maman Barrister). Da na idar na sake musu kaya zuwa wani riga da wando na english wears kalar maroon a raina nace zabin Sulaiman, takalma ma duk na basu na fesa musu turare suka tafi. Basu dawo ba sai goma saura Abdul ne ya kawo su, sabe da Amaturrahman ita kuma Amatullahi tana tafiya da kafar ta nace

"Sannu Abdul tayi barci kenan?"

Yace

" Eh tun a Zaria"

Nace to sannu na gode tare da amsar ta nace kun dawo lafiya? Ya kuka bar Hajiyar yace lafiya kalau tana gaishe ki itama nace ina amsawa sosai.
Kwantar da ita nayi na canja mata kaya, itama Amatullahi tayo alwala muka zo muka kwanta.

Yau ina zaune kan kujera na juyo kukan Amaturrahman a kasa ban wani damu ba don nasan rakin ta. Ba jimawa ko sai gasu da tablet dinta hannun Amatullahi nace

"Ya dai?"

Tace

"Mami kinga Islam ta fasa tablet din Amaturrahman ta cije ta shine su yayar ta suke dukan ta, wai ta cije ta shine Mummy tace itama Islam ta rama"

Nace

"Zo Amaturrahman"

Ta taho na kalli hannun gashi nan gurin ya shata a farar fatar ta nace

"To kiyi hakuri kin ji ko? Nan gaba in kuna wasa bana son fada"

Tace

"Ayya sai na yama"

Nace

" A'a kiyi hakuri Amatu na."

Da kyar na lallashe ta tayi shiru na amshi tablet din nace gobe in naje school na tsaya a gyara maki. Da dare da ya shigo ina kallonsa ya kama kunnen Amaturrahman yace

"kece mai cizo da kika cije min yata ko?"

Tace

"Itama ta yama"

WADATAWhere stories live. Discover now