THIRTY THREE

2.3K 331 42
                                    

*WADATA*
_Thirty three_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad

Ba dadewa sai ga Bashir ya dawo daga Malaysia, babu ko ounce of Kunya wai nazo yayi min gaisuwa nace ni kam babu inda zani dama lokacin saka nake indai don gaisuwa ai mun yi ma juna a waya. Haka nan kuma ya tsiri zuwa tun ana kula shi har kowa ya share ni gani nake yama raina mutane upon duk abun da yayi min amma don ya fetsere idon sa yace zai zo gidanmu.
Nabar permanent morning har ansa ni a a shifting, Yau kam evening duty nake, sai takwas na tashi kafin Nazo gida Tara Har tayi. Ban je da mota ba saboda na kai ta gurin service don haka adaidaita sahu na samu na hau. Bakin titi ya sauke ni lokacin tara har tayi ina ta sauri na isa gida nayi wanka na aza hakarkari na a gado kafin gobe. Na kusa layin mu na kara sauri bana son bi ta layin saboda karancin mutane ga dare. Kamar daga sama mota ta taho, sai kuma yayi full light, bana son abun nan saboda na motar yana kallo na ni kuma bana ganinshi, tsaki nayi na rufe idona ko bai ji ba ai dole dai ya gane. Kaucewa nayi amma ya biyo ni sai da ya sada ni da bango tukun a lokacin na saddakar ya buge ni ya gama kawai. Amma sai naji ya kashe fitilar  bai dai kashe motar ba. Kafin na yunkura na tafi har ya fito.
   Matsowa daf dani yasa na gane shi da kamshin turaren sa. Baya na kuma na hade da bango ina fadin

"A'uzubillahi minas shaidanur rajim!, malam meye haka ne?"

Sai da yazo daf dani har ina jin fitar numfashin sa a goshi na kamar yadda nasan zai ji nawa a kirjinsa yace

" Ni ba shaidan bane "

Nace

" Matsa mana Bashir, kana kokarin aikata mummunan laifi fa"

Yace

" To ina kika je, daga Ina kike da darannan? "

Nace

"Inda ka aikeni mana ubana"

Se ya saki dariya, hakan yasa Nace

"Ni duk ba wannan ba malam ka bani hanya na wuce"

Yace

" Magana zamu yi."

Duk da sanin baya gani na amma hakan bai hana na galla masa harara ba nace

" Ai magana ta kare tsakanin mu.. Ka matsa kafin nayi maka ihun kwarto malam"

Yace

" Bismillah."

Sake matsowa yayi yana kokarin kai lebensa kan nawa. Ban san lokacin dana hade karfi na ture shi ina fadin

"Lafiyar ka kuwa?"

Yace

" Kwarai gani nayi kar kiyi ihun a iska gara nayi da gayya..... Kawai ki taimaki kanki ki tsaya muyi magana."

Ban kula shi ba nayi gaba abuna ya riko hannu na. Yace

"Ki tsaya so nake muyi magana dake Aisha, akan yadda zamu maida auren mu, nasan banda bakin maki magana amma don Allah kiyi hakuri. Wannan course din da naje ina dawowa na samu matsayin Senior Advocate of Nigeria. Zan koma Abuja kinga sai na tafi dake Sa'adatu na bar ta Kaduna saboda makarantar yara, kinga in baa zauna gida ba babu wata rigima. Hakika mutuwar Muhammad ta canja komai gare ni, ki amince dani, ki sake bani dama a Karo na biyu don Allah."

Hannuna na fizge Har seda nashi suka bigi bomber din motarshi, Ni kalaman sa ma haushi suka bani suka kuma bata min rai, amma saboda ya rabu dani sai na ce masa

"Naji ka bar ni tukun nayi tunani"

Da murna yace

"Thank you Shatu na! I knew ba zaki taba disappointing dina ba."

WADATAWhere stories live. Discover now