2

5.1K 223 2
                                    

                   _2_

***Shehuri(shehun borno palace); convoy d'in motocin su yareema Hydar  nashiga fadawa sukazo suka taso suka saka bayan babbar rigunansu suka kareshi suka shigar dashi cikin masarautar, agajiye yake lik'is ganin mai martaba na fada suna meeting da wazirinsa yasa kansa tsaye ya wuce cikin gidah part d'insu, yana xuwa ya xaro handkerchief d'insa yai hanxarin toshe hancinsa as usual parlor d'in anyi littering d'inshi da leftovers na abinci se robobin lemuka kala kala duk a barbaje ga kwalin aspen taba awajen kamr parlorn mahaukata,dogon tsaki yareema Hydar yaja ganin haryanxu step brother d'insa yareema babagana yananan da halinsa na k'axanta da shaye shaye...

Compound yakoma na sashensu, a sukwane bayi/dogarai sukayo wajensa had'e da yin gurfane inda yake...

"Gaisheka yareema Hydar d'an sarki jikan sarki,d'an g...."basu k'arasaba yareema Hydar  ya tsayar dasu..

"Sarkin gidah inaso kazo da dakaran tsafta yanxu kuyi hanxarin gyaran sashenmu...."

"Angama yareema Hydar  kaga d'an sarki wanda xe gaji g..."

Basu k'arasaba yai saurin d'aga masu hannu don inda sabo yasaba jin wannan kirarin... A sukwane suka kwasa aguje sukai cikin gidah b'angaren su Hydar.Gyara sukahau yiwa wajen seda suka gyarashi tatas sannan suka bar sashen,se asannan ya shiga cikin sashen nasu yai hanyar d'akinsa,tafkeken d'aki ne komai fari had'e da parlor aciki kujerun blue da kayan kallo,band'aki yashiga yai alwala yai wanka sannan yai sallah, yad'akko abin turaren wuta ya jona ya bulala turaren wuta tuni d'akin yahau k'amshi ,ba'a jimaba mai martaba yak'are meeting sannan yareema Hydar yaje suka gaisa har sukaci abinci tare sanin halin kishiyoyin uwar tasa ba bashi xasuyiba seda yad'an caccakuna yaci ba lefi dayake ba ma'abocin abinci bane sannan mai martaba yace yaje wajen sauran iyayen nasa ya gaishesu ...

Sashen hajia gajiram yafara xuwa wacce itace uwargidah, kafin yashiga seda jakadiya tai masa iso Kamar wani bak'o,yashiga ko ajikinsa had'e da d'an tsugunnawa cikeda girmamawa cikin harshen kanuri yace;

  "Yayya inda dubdo?!(Ina yini yayya?!"yafad'a hakan cikeda ladabi..

Seda Hajja gajiram tacika ta batse kafin ta amsa da kyar kamar me ciwon magana;

  "Kelewa selai...(lapia Alhamdulillah)" tak'arashe  maganar cikeda tsana tana kuma wurga masa harara ta k'asan idonta

Bedamuba ya mik'e don yasan hakan xata faru inda Sabo yasaba ganin beyond hakama,sashen hajja yakolo yanufa itama ya gaidata same abinda tamai kenan, ko ajikinsa itama Haka ya mik'e yakoma sashensu,yana xuwa yaciro sim d'insa yasaka yai dialing number mahaifiyarsa hajia hajjagana ringing d'aya biyu tad'auka...

  "Salaam alykm Ammee inda dubdo?!"

"Kelewa selai Hydar,kazo garine?!" Ammee tafad'i hakan cikin nutsuwa da dattako

"Ehh Ammee"

"Dafatan komi lapia de?!"

"Lapia Lou Ammee,bamuyi magana da baban bade may be se xuwa da safe"

SON RAI KO ZABIN IYAYE?!(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now