13

2.3K 126 0
                                    

*A* cikin kitchen suka jiyo motsin ta dan haka can kiara ta nufa da saurinta tana kiranta da,

"Sister where are you?!"

Da sauri layla ta ajiye knife d'in hannunta tare da juyawa tafita,kusan cin karo sukayi da juna gaba d'aya suka sakarwa juna murmushi kiara ta bud'e hannuwanta suka rungume juna suna dariya, a hankali kiaran ta kai hannunta saman cikin layla cikin gwarancin hausarta da ta fara iyawa yanzu tace,

"Sister yaya babyn mu hope yana mosi?!"

Da sauri Modu ya girgizawa laylan kai alamar tace a'a aikuwa layla tayi kalar tausayi da fuskarta kafin tace,

"A'a sister 4 day's kenan banjin komai am scared."

Gaba d'aya hankalin kiara ya tashi ta rud'e tare da jan hannun layla ta fito da ita daga cikin kitchen d'in ta kamo na Modu ma tace,

"Let's go to the hospital please ina son wannan baby muje aI check up ."

Dariya taji sunyi gaba d'aya hakan yasa tabisu da kallon mamaki kafin ta had'e rai,Modu ya zame hannunshi daga cikin nata sannan ya kamo kumatunta yana kallon cikin idanuwan ta yace,

"Sorry my dear lafiyan baby fine and good it was just a joke,we are kidding you m sorry"

Ya fad'a yana kuma yin dariyar,dukan wasa takai mai gaba d'aya suka dara sannan layla ta koma kitchen ta samo musu abin motsa baki ta dawo parlorn ta zauna suka ci gaba da hirar su tamkar ba kishiyoyi ba anan ne kuma kiara ta sanarwa da laylan cewar tana son musulinta layla tayi murna sosai harda hawaye dan dama abunda yake damun ranta kenan kin musulintar ta amma yanxun sai taji wani farin ciki tamkar yau ta haihu.

"Toh sai muje a sanar da baba ko honey?!"

"Yap abinda nace kenan nasan zasuyi murna sosai idan suka ji wannan zancen."

"Sister ina son idan na yi musulma asa sunana Nanarh Aisha ina sonta sosai."

"Alhamdulillah sister insha Allahu as you wished Allah yasa ki amfanar da addinin musulinci Allah kuma ya karb'i tubanki."

"Amin."

Cewar Modu daya karkatar da hulan kanshi kowaccen su kokarin faranta mishi takeyi shi kuma sai k'ara narkewa yake kamar wani k'aramin yaro.

*SHEHURI*

Kuka Meenah ta dingayi tamkar bazata bari ba,da kyar ta iya motsa hannunta tana laliban wayanta so take ta kirawo aunty yaruwaiya amma wayam babu ita a inda ta ajiyeta,hawaye na zubar mata ta mik'e da kyar tana ci gaba da neman wayan amma bataganta ba wayar kuwa kamar sarki Aliyu hydar ya sani ya d'auketa ya tafi ta ita bedroom d'inshi nan ta ci gaba dayin kukanta har wajan asuba sai a sannan ta mik'e da kyar ta wuce bathroom babu abinda yafi d'aga mata hankali irin jinin da ta gani ya fito mata sai ta kuma sakin kuka lokacin sarki Aliyu hydar ya shigo d'akin yana sanye cikin wata jallabiya mai masifar kyau.

SON RAI KO ZABIN IYAYE?!(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now