20 (END)

3.4K 139 29
                                    


  *G*urfane sarki Aliyu hydar yayi a gaban maimartaba maimurabus yayin da gefe guda Ammi ce take dama fura da nono kasan cewar baya son shan wadda akayi blending d'inta,kusa da Aliyun kuma yareemah Ngari ne da yareemah babagana sai Modu a kusa da Ammi duk girman parlor'n amma yaje ya nanik'e mata.

Shehu Bulama ya gyara zama yana kallon Aliyu hydar yace,

"Ranka ya dad'e kai muke jira ka taramu kayi shiru sai faman  kallonmu kakeyi ince dai lafiya ko?!"

Kuma gyara zama Aliyu hydar yayi tare da shafa gashin dake zagaye a fuskarshi,sunkuyar da kai yayi yana neman ta inda zai fara dan kowa na gurin shi yake kallo ganin haka yasa shi cewa.

"Amm....Dama....Baba abinda yasa nace zanyi magana daku akan maganar kujerar da nake kai ne.."

Yayi shiru su kuma suka sake zura mai ido danjin k'arin bayani,shi kuma ya sake sunkuyar da kai sannan yace.

"Ina son na sauka daga kai na bawa d'an uwana zaifi kulawa da ita sannan shine yafi cancanta da ita ba niba,ina son na sauka na bawa baah Ngari dan Allah karkuce a'a tunda duk d'aya ne nida shi."

Bak'ara min mamaki kowa yaji ba amma banda Modu kasan cewar tare suka shirya komai,baki bud'e shehu bulama yake kallon Aliyu hydar kafin ya d'ora Modu ya karb'e zancen da cewa.

"Haka ne baba wallahi gara ya sauka ya bawa wanda zai iya dan wannan sarkin kawai cukwan kujera ne amma baya komai sai tara mutane yana binsu da eh ko a'a, dan Allah baba a bawa baah kawai..."

"Why me brother?ni yanzu me na sani akan sarauta zaku ce a bani?bana so baba bansan komai akanta ba taya za'a bani ragamar jagorantar mutane?kuna gani sai yanzu nake fara sanin abubuwa da kuma yanayin rayuwa, gaskiya bana so a bawa babagana idan shi yana ganin baya so."

Cewar yareemah Ngari yana magana cikin yanayin damuwa da jimami dan shi yasan akwai abubuwan dabe sani ba dayawa a cikin masarautar,baba maimartaba yayi shiru na tsawon lokaci yareemah babagana yayi dariya kowa ya maida hankali gurin shi yana dariyar yace,

"Ni za'a bawa sarauta ko?hmmm da kunjawa masarautar nan zagi dan wallahi sai tayi rugu-rugu sabida ba zaman fada zanyi ba,babu abinda na tsana a rayuwata irin naga an takura min ko an samin ido bare a kaiga kawo min koke-koke kunsan babu wanda zan saurara bikon matata nake yi kuna gani dai tak'i dawowa."

Dariya Ammi tayi jin abinda babagana ya fad'a sai faman kad'a kai takeyi yayinda shehu bulama ya sake gyara zama ya kalli Aliyu hydar sosai dan yana son gano da gaske ne baya son sarautar kokuwa dai akwai abinda yake damun shi,murmushi ya saki sannan yace.

"Idan na fahimceka Aliyu kana sone kawai ka zauna a gurin matanka ko?!"

Shiru Aliyu hydar yayi domin da kunya ya amsa wannan tambayar ta maimartaba,muryar Ammi suka ji tana cewa.

"Hakuri zakayi Aliyu kaci gaba da rikon wannan matsayin domin Yayan ka yafika gaskiya kafishi sanin duk wasu abubuwa dake faruwa da kuma akeyi ko ake so a cikin masarautar nan tunda dai shi duk a kwance yayi rayuwarsa so kar a takura mai gaskiya."

SON RAI KO ZABIN IYAYE?!(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now