15

1.8K 122 0
                                    

    *S*hiru Shehu Bulama yai yana jinjina kai hade da ajiyar zuciya ya jima a haka kafin ya maida dubansa ga Ayiya dake gefan yakolo cikin sark'ak'iyar murya a tausashe yace,

"Ayiya hanxarta kikai ta xuwa asibiti kafin ku k'arasa xan kira dr na b'angaren optometrist(ido)ya duba idanun.."

"Toh baba"cewar Ayiya..

Mikewa Aysaa tai ta temaka Ayiya suka tafi da yakolon xuwa asibiti..

Da azama yareemah babagana yayi saurin fita ya cafko hajja gajiram wadda ke faman k'ok'arin fita harabar masarautar hannuwanta ya kamo hawaye nabin kuncinsa ya fara kokarin janta zuwa wani d'aki anan cikin apartment d'in amma ta kafe guri d'aya.da kyar yasa iya karfinshi yajata tana dukanshi tana yakushin hannunshi tare da harb'in shi da kafarta amma haka ya daure duk da cewar yanajin zafi ya shigar da ita tare da janyo k'ofar ya rufe sai faman dura zagi take yi tare da bankad'a asirinsu.

A gurin ya zauna yana kuka yayin da can parlor kuma kowa yashiga yin jimami mai martaba maimurabus yace ayi addu'a kowa ya koma harkar gabanshi.Modu ne ya daga hannu alamar zai fad'i wani abun sai faman sosa keya yake yi Shehu Bulama yace,

"Toh Modu muna jinka kai muke jira."

"Dama baba tun jiya muka zo akan maganar kiara, domin ta shaida mana cewar tana son ta musulinta,jiya munzo muka samu jakadiya kolo hakan yasa bamu zo mun sanar dakai ba nace ta bari sai yau."

Babu wanda beji dad'i ba a cikin ranshi yayin da Shehu Bulama yayi murmushi yana girgiza kai yace.

"Lallai sai yau na kuma tabbatar da cewar har yanzu kud'in yara ne,shi Aliyu be iya gudanar da harkokin cikin fada duk ina lura dashi sai soyayya daya saka a gaba.kai kuma Modu daka ga baka samu damar gani naba ai da saika bata kalmatush-shahada,irin wannan Ai ba'a jira ace sai wani yazo ko sai yana nan,

"Alhamdulillah dama abinda muke son jikenan yanzu kaje ka yi duk abinda ya dace bawai dole sai ka kawota nan ba zamu zo da kanmu muyi mata murna."

Cike da murna yayi wa baban godiya sannan sukayi addu'a kowa ya fara yin inda zai tafi.kusa da sarki Aliyu hydar ya matsa wanda da alama so yake ya tafi da Meenah ita kuma taga su Ammi ko kallon inda yake batayi ba dan karta bishi, Modu ya rab'a yace.

"Guy kana ruwa wallahi tunda har baba ya gano matsalarka king of love..."

Aliyu hydar ya yatsina fuska cikin rashin damuwa yace.

"Eh naji kaga ba ta yadda za'ayi kenan a dinga rabani da matata,kuma naji dad'i tunda sun gane cewar *ZAB'IN IYAYE* ya sanya ni zama hakan ai da ba haka nake ba."

Modu ya kyalkyale da dariya yace.

"Hope dai kayi kokarin aje kaya dan gashi ni har zan riga ka ajewa..?!"

"Ok abinda ka aike ne yi kenan dama?toh ban sani ba ka samin ido fa da yawa."

SON RAI KO ZABIN IYAYE?!(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now