18

1.6K 121 2
                                    

Wani mugun kallo mai cike da tsantsar tsana billy tabi yareemah babagana dashi, k'o'karin fita yaga tana yi daga cikin d'akin yayi saurin rik'ota tare da matseta ta baya a jikinshi yana shafar cikinta wanda yayi tudu ta sa hannunta ta ture nashi daga kan cikinta cikin masifa wadda be san tana da ita ba yaji tace,

"Malam ka cika ni bana son wannan salon iskancin."

Tana matsen a jikin shi ya hura wata iska daga bakinshi zuwa kunnanta nan da nan kafafuwan billy suka fara rawa ya kuma hura mata iskar cikin kunne jikinta yayi sanyi ya sanyan hannun shi yana shafar wuyanta zuwa saman kirjinta, nan da nan sakon nashi ya fara shiga cikin kwakwalwarta ta fara lumshe ido tana sauke wani irin nishi ya fara murna kawai yaji tayi saurin kwace jikinta ta juyo tana hararar shi ya shafa kanshi idanunshi sun wani shanye cikin masifa ta kuma cewa.

"Me ya kawoka gidan nan? Ina son dan Allah idan kai ba maye bane kafin ka fita ka bani takardar saki na domin  bana son ka na tsaneka...!"

"Kiyi hakuri my billy bazan iya sakinki ba iya wuya muna tare fata na ki dawo gare ni dan Allah wallahi tun abinda ya faru tsakanin mu na rasa nutsuwata soyayyarki ta sauya ni karki bari kuma ki gujemin domin idan kika yi min haka ban san yadda zanyi ba, a yanzu haka my Billy rayuwa ta tana hannun Allah tana hannunki sai yadda kika yi da ita, kyautata mata ko kuntata mata."

Kuka ta sanya a gurin shi kuma ya k'arasa gurinta, da sauri ta mik'e tana d'aga mai hannu alamar karya ta6a ta ya tsaya cak cike da tausayin ta yana ji tana yi kukan har cikin brain d'in shi.ya d'auki tsawon lokaci kamin ya tashi ya tafi bayan ya ajiye mata uban kud'i wanda ko shi besan ko nawa bane yayi masu abba sallama ya fita.

A b'angaran su yareemah Ngari kuwa shirye-shiryen bikin shi ake tayi sannan sarki Aliyu hydar da kanshi yasa aka yo irin zanen gidan da za'a cancarawa yayan nashi tun daga India..

Cikin one month an kammala gini kasan cewar akwai kud'in a k'asa, cikin sati biyu aka fara gudanar da shagalin biki anan cikin shehuri kasan cewar itama Ammi an gyara mata apartment d'in kusa da mijinta shehu Bulama kasan cewar SB yace ta dawo kenan baza ta sake komawa damboa road ba tunda an riga an warware duk wani kulli daya haddasa barinta cikin shehurin yanzu hankalin kowa a kwance yake ba kamar su Meenah dan sarki Aliyu hydar da kyar yake iya fita fada dan ya raini Meenah da soyayyar shi salo-salo kuma yanzu ta zama kwararriya ga lecture din aunty yaruwaiya da suke b'ata kud'i a waya tana gaya mata hanyoyin mallakar miji ba boka ba malam dan haka yasha k'in fita hudubar juma sai gab da za'a tayar da sallah tukunna zai tafi ba kunya dan yama fara wani tunani kuma yana nan yana son aiwatar dashi jira yake ayi bikin Ngari.

Alhamdulillah anyi komai na bikin yareemah Usman (Ngari)Shehu Bulama Goni da zankadediyar amaryar tasa Asmau(Asmy)Bunami Indimi Goni cikin jin dad'i da kwanciyar hankali lokacin layla tana watan haihuwarta ita kuma Kiara ta harbu sai dai ba'a tab'a ganewa kasan cewarta doguwa sai cikin yake bin jikinta,Basmah kuma da kyar da addu'a da rokan da Meenah ke mai akan shariyar daya kewa Basman ta samu Aliyu hydar ya karkato kanta dan yanzu ta riga ta b'arar da duk kusan rabin soyayyar da yake mata sannan kishi suke yi mai zafin gaske dan Meenah tana da tsananin kishi ko ranar da zai koma side d'in basmah sai yayi lallami sosai kafin ta barshi duk da shima ba a son ranshi yake barinta ba.

Anyi bikin yareemah Ngari da kwanaki biyu layla ta santalo baby boy d'inta murna a wajan abokiyar zamanta wato kiara har kuka tayi dan har tafi Modu murna.

SON RAI KO ZABIN IYAYE?!(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now