14

1.7K 115 0
                                    

*S*ake gurfane Mangu tai cikeda nutsuwa tafara magana kanta a k'asa,

"Hak'ik'a rankishi dad'e manzon Allah (SAW)yayi gaskiya da yace mai hakuri yana tare da nasara hakurinki yayiwa wad'anda basu dashi mugun ciwo ne domin har kullum dai kece a saman su duk kuwa ta inda aka bullo miki.Nikam naga ishara koda na sanar miki yanzu nasan an cuceki a baya sai dai nasan ked'in mai afuwace dan Allah rankishi dad'e ki gafarce ni,wallahi duk wani tuggun da ake shirya miki tun daga kanki har zuwa 'ya'yanki rashin lafiyar yareemah Ngari wallahi duk sihiri ne wanda ni suke aikawa wajan k'arb'o musu shi."

Jakadiya Mangu ta rushe musu da kuka Ammi ta bita da kallo cikin tsananin mamaki,cikin masifa aunty yaruwaiya tace,

"Suk'e turaki ki k'arb'o su suwa ye?!"

Hawaye basu bar zubowa daga fuskar jakadiya Mangu ba jikinta sai b'ari yake tace musu.

"Su...su...su abokan zaman nata wallahi su Kansu a had'e yake duk tare suke yin komai sai dai a baya komai sukayi boka yana basu sa'a sab'anin yanzu da duk abinda suka b'ullo miki da shi rankishi dad'e baya faruwa a kanki sai ya koma kansu musamman ma ita wadda take sawa ayin wato hajja..hajja mahaifiyar yareemah babagana,sam bata kaunar taga kin cigaba dake da 'ya'yanki da duk wani wanda ya rab'eki dan Allah rankishi dad'e kiyi min afuwa kinga nima tsautsayin daya afka min duk ta sanadiyar zuwa k'arb'o abinda za'a cutar daku ne,

"Wallahi Allah hajiya hatta rashin samun haihuwar matar maimartaba na yanzu wato maryamu da batayi ba duk makircin sune da suka dinga d'orata akai na cewar zata mallaki mijinta zai sota kamar babu wata d'iya mace a duniya ita kuma da yake yarinya ce sai ta yadda har suka illatata amma wallahi rankishi dad'e itama ba laifinta bane duk makircin sune akwai abubuwa da dama rankishi dad'e wanda ake ta shirya muku wani ma bakina bazai iya fad'ar shiba sai dai nace kiyi hakuri ki gafarta min gashi ban karu dasu da komai ba sai asarar sashen jikina da nayi."

Jikin aunty yaruwaiya har kyarma yake yi saboda tsabar kid'ima bakinta sai motsi yake da alama rashin mutunci take son yiwa jakadiya amma idon Ammi ya hanata dan tasan da ta fara zata katseta, duk gurin babu wanda be shiga cikin tashin hankali ba dajin wannan bayani na jakadiya sab'anin Ammi da take ta sakin murmushi wanda duk cikinsu babu wanda ya gane kona meye.kallon jakadiya Mungu Ammi tayi cikin jin dad'i da nuna kamar babu abinda taji tace mata.

"Toh sai muyiwa Allah godiya daya sa kika gane cewar abinda kuka aikata ba dai-dai bane Alhamdulillahi kuma na yafe miki jakadiya duniya da lahira har dasu d'inma duk na yafe muku,Allah ya ganar dasu suma su gane cewar Allah shine kadiran alaman yasha,duk mulkinka duk matsayinka duk tarin dukiyarka indai har baka sa Allah a cikin lamarinka ba toh ka tab'e tun anan duniya na kuma k'ara yadda da lamarin ubangiji domin dashi na dogara yau gashi ba wani takura muku akayi ba a'a da kankin kanku kuka fallasa abinda kuka b'oye Allah ya shirye mu ya shiryi duk wani musulmi dake fad'in duniyar nan."

"Amin Ammi."

Cewar Aysa yayin da Yaya gumsu tayi caraf tace..

"Wallahi basu isaba kanbala'in can!yo ai dama da walakin goro a miya dama sai da nace abincika matan nan amma k'iri-k'iri aka wani ce zato zunubi toh wallahi sai sunyi zaman gidan yari,muza'a wulakanta kema munafuka ba ciwon kafa ba ko ciwon me kikeyi wallahi sai kin k'arbi hukunci tunda kece munafukar,bulalai da xaman gidan kaso shiya kaman ce ku"

SON RAI KO ZABIN IYAYE?!(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now