Hannah part 4

524 27 1
                                        

💥 *Hannah* 💥

        0️⃣4️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramada)*
Whattpad@oumramadan1

Ranar Friday da wuri su hanna suka taso daga makaranta ,a gurguje tai wanka saboda kushin da zasuje ayi musu na bikin da zasuyi a family d'insu ,doguwar riga hanna tasa ta shafa powder da lipstick ta yafa mayafin doguwar rigar sosai tai kyau parlour ta fito tace "aunty zamu tafi"
Aunty tace "to saikun dawo "   fita tai bayan ta kar6i kudin da abba ya basu itada da fannah da basma ,sai da ta fara biyawa part din mamii mus,ab ta samu a parlour yana kallo tana ganinsa ta had'e rai zata koma,
  Dariya yayi yace "abun yar hakane parrot " ta turo baki tace"ae nidai yaya mus,ab mun 6ata yau kwana 3 da kamin alkawari har yanzu shiru"
  Tashi mus,ab yayi yace "to yanzu zo muje na siya miki shikkenan ko?" Shigowa parloun tai tana sakin murmushi tace "eh amma yanzu kunshi da kitso zamu in mun dawo saika kaini kuma ni kad'ai"  mukullin mota ya d'auka yace "Muje na kaiku daga nan saimu wuce ki siyo burger d'in"
  Tace"to bari naga mamiina"  tana gama fad'a ta wuce bedroom ,jim kad'an ta sakko tana sakin murmushinta mekyau tace "to muje"  baice komai ba suka wuce a compound suka tadda fannah da basma ,motar mus,ab suka shiga ya kaisu wajen da ake kitson ,
  Zama yayi a mota yana kallo a wayarsa har aka gama musu kunshin da lallen da yake ba ja sai  basu d'ade ba suka fito, star bakery and more ya tsaya dake titin kabuga  yasiwa hanna burger d'inta basma kuma da fannah yasai musu pizza ,  ranar asabar sukai shirin zuwa bikin yar kanwar mamansu dake tudun yola ,kaya kala 3 hanna ta d'auka na ankwon da akai musu biyu na yammata 1 kuma wanda mamii tai mata na mother's day,
  Karfe 3 aunty da mamii da mum suka shigo tudun yola ,mum sosai tai musu kara ba ankwon da batai ba na bikin dan kansu a had'e yake ko biki ake a familyn d'aya haduwa sukai suyi komai  ,taro akai na wayayyun mata yan gayu ko wacce burinta tafi wata kece raini, da dare amarya da ango sukai dinner hanna  da fannah sai kanwar amarya farha sunyi ankonsu ba karamin kyau sukai ba basma dama tana cikin tawagar amarya da kawayenta, sai karfe 10 na dare aka tashi ,
  Washe gari k'arfe 1 na rana aka d'aura auren ana gamawa su big daddy suka wuce sai haydar da Farouk da mus,ab suka shigo cikin gidan, mamii sai kallan haydar take daya cakare cikin wata Australian gizna kyau yayi sosai saidai fuskar nan ba fara,a  abokan wasa sai jansa suke yana fusgewa,tab'e baki tai tana magana da mus,ab,
  Farouk sai wurga ido yake yaga ta inda hanna zata 6ullo can yaganta tare da farha kayansu iri d'aya shaddace coffee akai musu dinkin riga da sket ,sosai tai wani mugun kyau ya kasa d'auke idonsa daga kanta tana zuwa ta zauna kusa dashi tana murmushi tace "kayi kyau yaya Farouk "  karan hancinta yaja yana ware idanunsa kasa kasa yace "kema kinyi kyau yammatana"  murmushi tai ta gaidasu mus,ab yace "parrot baza,ayi pic bane"  tasowa tai ta dawo kusa dashi tace "yanzu kuwa yaya mus,ab "  haydar kansa yana k'asa sai operating waya yake,
  Hotuna suka d'auka sosai aunty ta kalli haydar tace "yayansu kazo ayi hotuna mana"  mamii ta ta6e ,tashi yayi yana d'an shafa keyarsa ya shiga akai hotunan duk ya kagu ya bar wajen mamii tana kula dashi,suna gamawa ya fice batare daya jira su Farouk da suketa surutu da hanna ba,
   Karfe 6 aka mik'a amarya gidanta dake rijiyar zaki,daganan gida su su hanna suka koma sbd akwai skull gobe,
Ringing d'in da wayarsa take ya katse masa aikin da yake a loptop ,lokaci d'aya ya saki wani siririn tsaki ya d'au wayar batare daya duba sunan ba ,siyama ta saki wata katuwar ajiyar zuciya ji take kamar ta zuba ruwa a k'asa tasha yau haydar ya d'aga kiranta,Jin anyi shirune ya k'ular da haydar yana shirin ajiye wayar yaji siyama cikin sanyin murya tace"assalam alaikum "
K'asa k'asa ya amsa yana mamakin maita irinta siyama,narke murya tai a hankali tace "haydar ya aikin, dafatan kana lfy"
  "Lfy"  yace mata a tak'aice dan wani takaicine ya k'umesa siyama ta sake k'asa da murya tace "dan ALLAH yaushe zamu had'u inason muyi muhimmiyar magana dakai haydar"   d'aure fuska yayi tamkar tana ganinsa yace "banida lokaci"  daga haka ya kashe wayar yana kuma sakin wani tsakin,siyama ta tsurawa wayar ido tanajin wani rad'ad'i yana taso mata daga zuciya a hankali wasu hawayen kunci da tarin san wanda bata ishesa kallo ba ya silalo mata,
  Siyama mate d'in haydar ce tare sukai makaranta a UK duk cikin matan da sukai aji d'aya ba wacce yake kulawa kamar siyama saboda yana ganinta da kamun kai yakan d'an sake mata fuska su gaisa ,sai dai iya siyama ba k'aramin son haydar ALLAH ya d'ora mata ba inta gansa ji take tamkar ta tsaga jikinta ta sashi ko zataji d'adi ,tun daga lokacin da siyama ta furtawa haydar kalmar so ya daina kulata sbd nacin da take masa har suka dawo 9ij siyama su biyu iyayenta suka haifa itace babba sai kaninta abdull mahaifinta shaharren dan kwangilane da gwamnati take damawa dasu,
  Siyama ta sake gwada kiran haydar kozai d'aga still taji bai d'agaba ,lokaci d'aya ta fashe da wani kuka mecin rai ALLAH ya gani tana k'aunar haydar ba kad'an ba duk irin yadda samari suke bibiyarta kasancewar ta kyakkyawa batako kulasu iyayenta harsun gaji da mata magana ta fidda miji amma tace duk basuyi mata za6inta shine haydar kullum shi take burin mallaka shi kad'ai take gani a matsayin mijin da zata iya zama dashi ,
  Kwanciya tai saida tai kuka me isarta sannan ta mik'e ta shige bathroom ta wanko fuskarta ta fito mukullin mota ta d'auka bayan ta yane kanta da siririn mayafi ta fice daga gidan kasancewar mum d'inta tana wajen aiki.

HannahDonde viven las historias. Descúbrelo ahora