💥 *Hannah*💥
*Romantic love story*
3️⃣2️⃣*Maryam Abdullahi (Oumramadan)*
*Whattpad@OumRamadan1*Shagulgulan biki sun cigaba da gudana tako ina anata hada hada kowa ka gani fsukarsa d'auke da farin ciki abinci kuwa gashinan a jibge kaci ka koshi kowace kala kakeso can na hango Yan hanna fans Group 1,2,3, anata hada hadar kaiwa ciki bako kara wasuma har dan guzuri suke yi suna turawa cikin jaka nidai ina gefe na kasacin komai ina jiran yan tawagar fans din mk suzo mu jajantawa juna ganin yunwa tana neman illatani ba Shiri na faki idanun jama,a na kwashi abinci na koma gefe inaci Ina kwalla sbd rashin gabatowar fans din mk,
Hanna kuwa tanacan kwance zazza6i ya rufeta dan sosai tai kuka ,kuka na takaici da rabuwar masoyi kukan bakin cikin yaudarar da mk yay mata ko abinci dakyar tai loma 2 shima tanayi ta amayar gashi dama bajin dadin abincin taiba sbd damuwa ,
Bangaren mk kuwa duk iya neman da abokansa sukai masa kasa samunshi sukai har guesthouse d'in sa suka duba bashi ba alamarsa gajiya sukai kowa ya kama gabansa , senate kuwa hankali kwance ya sallami manyan bakinsa da suka samu halartar bikin Saida ya nutsu sannan ya d'aga waya ya Kira mk 2miss call senate yay masa sannan ya d'aga on serious tone senate yace "duk inda kake kazo ka sameni a gida" yana fad'a ya kashe wayar ya d'ora kafa d'aya kan d'aya yana jijijigata kana kallan fuskarsa zakasan ba sauki a tattare da ita, kusan 1h sannan mk ya shigo fuskarsa shima murtuk ba alamar fari,a kansa a sunkuye ya shigo can kasa yay sallama ya zauna kasan carpet a takaice ya amsa yana binsa da wani irin kallo,
Fuska ba walwala yace "jeka kiramin mahaifiyarka" batare daya amsaba ya mike a bai yarda ya shiga part d'in ba yasa yan aikin daya gani sunata hada hadar rabawa mutane abinci su Kira masa ita,
Bata wani jimaba ta fito ta fito cikin shiga ta kece raini as usual, fuskarta a washe take da fara,a a bakin kofar part d'in senate ta samu mk yana ganinta ya shige ta bisa da a baya a haka suka shiga ta nemi waje kusa da senate ta zauna tunda ta shigo dama ta fuskanci akwai matsala ganin yadda fuskar senate take a mugun d'aure , d'aurewa tai tace "my senate lfy? Ko jikinne?" Bai kalleta sai idanunsa daya maida kan mk a kausashe yace "kana mamakin sauyin auran da aka samu ko? Kana murna ka lalata musu yarinya ka yaudareta sannan kace bazaka aure taba sbd ka zama abinda ka zama ko? " Mikewa yay ya fuskanceshi da kyau yace "babban kuskuran da zakai ka saki wannan yarinyar daka zalunta ,idan har hannunka ko bakinka yay gangancin sakinta ba tare da ta taka dokar Allah wlhy sai dai ka nemi wani mahaifin bani ba" mikewa hajiya sara tai cikin tsananin kaduwar abunda ya fad'i tace "senate wai me yake faruwa? Bangane maganganun da kake fad'a ba" kallanta yay ransa a mugun 6ace yace "yarinyar daya yaudara ya cuci rayuwarta yaki auranta na aura masa yau,tun kwanaki iyayen yarinyar da aka sa musu rana suka gano mugun halinsa suka fasa ni Kuma na aura masa wacce ya guda sbd son zuciya irin nasa da rashin tunani" a firgice hajiya sara tace "senate kana nufin da wata aka d'aura bada wacce muka sani ba?" Wani kallo yay mata baice komai ba a fusace tace "Kai mustapha wato duk fad'an da nake ma bakaji ko? Wato shashancin da kake dama baka daina ba?" Da mamaki senate yace "wato dama kinada labarin irin rayuwar da yakeyi baki ta6a sanar dani ba kenan?" Shiru tai cike da 6acin rai gyad'a kai senate yay cike da takaici yace "yayi kyau ,toni ba mutumin banza bane yaje ya zauna da wacce ya cuta Kuma na rantse muku da Allah ka kuskura Kai mata wani abu ta Kuma kawomin kararka saika fuskanci mummunan 6acin raina" daga haka yay shigewarsa bedroom kamar zai fad'i sbd 6acin rai, kuka hajiya sara ta fashe dashi cikin tsananin takaici da tsanar yarinyar murya na rawa tace "kaga abinda ka jawomin ko mustapha,waima tukun wace Yar matsiyatar ka samomin ne, yanzu me zancewa kawayena da wannan abun kunyar " shidai baice komai ba sai kansa da yake k'asa a lokacin jiyai ba Wanda ya kaishi tashin hankali da bakin ciki ransa tafarfasa kawai yake yana huci baison yana son hanna ba saida ta su6ce masa rufe idanunsa yay yana hango hanny da irin kalar ukubar za zata fuskanta daga garesa Kuma yasha alwashin bazai ta6a bari ta samu kwanciyar hankali ba baisan rashin mutuncin Hanny yakai haka ba baison sharrinta da makircinta sun wuce tunaninsaba, a tsawace hajiya sara tace "ina tambayarka kamin shiru wace Yar mutsiyar ka jajibo mana cikin family,ina murna ka samo mana Yar dangi ga kyau malam sai nunawa friends d'ina nake inajin dad'i yanzu Kuma ace labari ya canza salo" mikewa yay ya fice zuciyarsa na bugawa a duk sanda tai zancan hanna sai yaji kamar ya had'iyi zuciya ya mutu dan bakin ciki bai ta6a tunanin kaunarta yake ba sai yanzu mota ya shige ya figa da k'arfi ya fice daga gidan,
Kuka hajiya sara ta zauna tanayi cike da bakin ciki da tsanar yarinyar babban damuwarta me zatacewa kawayenta da duk suke shirin zuwa d'aukar amarya ,fatanta d'aya Allah yasa wancan ba Yar matsiyata bace amma ya zamar mata dole ta nemi mafita dan bazata ta6a bari kimarta da darajarta su zube a idanun kawayenta ba,
"Sister yakamata ace kinbar kukannan haka jifa jikinki yadda yad'au zafi" basma tace da ita cike da damuwa rushewa da kuka ta sakeyi cikin sheshsheka tace"nidai ku barni inyi kukannan inji dad'i kawai a rasa waza,a auramin sai wannan mugun" ta sake fashewa da kuka, dariya Yanmmatan d'akin suka fashe da ita basma ta d'aure duk dariyar tana cinta takiyi tace "kece baki fahimci Yaya bane amma yana sonkifa hanna" ta d'ago da jajayen idanunta tace "a haka yake sona yanamin mugunta?" Dariya basma tai tace "kema fa rashin kunya kike masa shiyasa" ta had'e rai ta juya tace "na rantse indai yamin saina rama bazan kyaleba ni ae nasan halinsa kaf" rauda tace "toh tunda kinsan halinsa Kinga zaman sai yafi dad'i ba kida bukatar tsayawa ki gane halinsa" ta galla mata harara ta juya tana sheshsheka tana jinsu suna mata shakiyanci tai musu banza,
Karfe 6 na yamma aka gama shirya amaren anan parlourn big daddy aka tarasu da angwayen da iyayensu mata,nasiha sosai me ratsa jiki iyayensu maza sukai musu akan hakkokin aure da hakuri tuni su hanna suka fara kuka iyayensu ma harsun fara hawaye dama daganan ko wacce gidanta za,a mikata fita angwayen sukai da iyaye maza aka barsu suyi sallama , rumgume aunty hanna da basma sukai suna wani irin kuka me ta6a zuciya duk yadda aunty ta kai ga rike kukanta kasawa tai haka suka had'u suka ringa kuka dakyar sistern aunty da kawayenta suka banbaresu d'aga jikinta,
Fad'awa jikin mami hanna tai ta kankameta tana sakin wani kukan juyawa tai ta banbareta da karfi ta fita daga parlourn tana share hawaye ,
Haka aka sa kowacce a mota suna kuka aka wuce dasu gidajen mazajensu, a harabar katafaran gidan daya kayatu da kyau da tsari motoci suka tsaya tun daga nan zakasan gidan ba karamin had'uwa yay ba haske ta ko ina tamkar rana ga kyayatattun shuke shuke masu kyau da kamshi , sistern auntyce hajiya halima da wata Yar uwarsu abba suka fito da hanna da har yanzu take kuka suka shige da ita had'ad'd'en gidan daya gaji da had'uwa banda kamshi ha abinda yake tashi a parlourn kud'i kam sunyi kuka kana ganin gidan da kayan da aka zuba kasan kayane masu kyau da tsada ,gida fa ya mugun had'uwa komai saidai ace masha Allah,
Upstairs suka wuce da ita nan ma wani parlour ne daya amsa sunansa komai na cikin parlourn light purple ne da ratsin light pink hatta da rantsatstsun Kujerun ciki kalan sune a haka aka shige da ita bedroom d'in aka zaunar da ita kan bed d'in da aka lailayesa da bedsheet mai kyau sai tashin kamshi d'akin yake ,
Kusan minti 30 kowa ya watse sai Yan uwa da basufi su 3 ba sabon fad'a suka sake yiwa hanna sannan suka sake gyara inda aka d'an 6ata wasu kayan aka fito mata dasu hajiya halima ta feshe su da turaruka sosai ta ajiye mata su a kan bed d'in har kofar toilet ta kaita suna ganin shigarta suka fito da sauri dama drivern daya kawosu yana jiransu ba 6ata lokaci suka shige get man ya bud'e musu get suka fice daga gidan.*#HH*
*#Hanna_Haydar*
*#Oum Ramadan*
*#oneluv*

YOU ARE READING
Hannah
Historical FictionBincike a rayuwa wani abune da ALLAH ya hallata ku biyoni cikin wannan labarin na soyayya da kuma fadakarwa