💥 *Hannah*💥
*Romantic love story*
3️⃣3️⃣*Maryam Abdullahi a(Oumramadan)*
*Whattpad@OumRamadan1*Bata jimaba ta fito kayan da tagani akan bed d'in ta d'auka tasa sai 6ata fuska take a gurguje tasa ta fito parlour tana kwala musu kira,jin shiru gidan yay wani tsit yasa ta fahimci guduwa sukai komawa bedroom d'in tai da sauri ta kwanta akan gadon ta saki wani sabon kuka ga wani irin tsoro daya rufeta,
Kusan minti 30 tana kwance taji shigowar mota gidan jikinta ta sake takurewa cike da tsoro ta sake lullu6e kanta da mayafi, sama sama take jiyo maganganun mutane kusan minti 10 taji gidan ya sake shiru wani irin tsinkewa zuciyarta ta sakeyi ta runtse ido tana karanto addu,o,I karar bud'e k'ofar dataji ya sake sata fad'uwar gaba wani tsoro ta ringaji da bata ta6a jin irinsaba ,haydar kuwa dama kai tsaye bedroom d'in da yaji sheshshekan kuka ya nufa,
Cikin nutsuwa ya murd'a handle d'in k'ofar kasa kasa yay sallama ya shiga,
Ledar daya shigo da ita dama ya barta a parlour jingina yay da jikin bango ya tsura mata ido yana sauke ajiyar zuciya,kukan da take jinsa yake har cikin ransa jin kukan yake yana ta6a masa zuciya ji yake kamar ya je ya rumgumeta ya tayata kukan kozai samu sassaucin numfashin ya fesar me zafi ya taka a hankali har inda take kwance,
Kusan few second yana kallanta kafin ya zauna kusa da ita hannu yasa ya kamota ya sata a jikinsa bugun zuciyarsu na had'uwa waje d'aya a tare suka sauke ajiyar zuciya me karfi mayafin ya janye ya gyara mata zama a jikinsa yana shafa bayanta a hankali yana hura mata iska a kunne , lokaci d'aya ta daina kukan sai sheshsheka da take da ajiyar zuciya irin na wanda yaci kuka ya koshi,kusan 10mnt suna haka a hankali ya d'agota yana kallan tsakiyar idanunta ta runtse ido da karfi tana neman sunkuyar da kanta ,bai barta tayi haka ba cikin wata irin murya me sanyi had'e da shauk'in dayake dawainiya dashi yace "kukan ya isa haka uhmm,karkije ki ja mana wani ciwon bakiji yadda jikinki yad'au zafi ba" ita dai batace komai ba illa wata matsananciyar kunya data kamata, murmushi ya saki kad'an ya sake tausasa murya yace "toh bazaki bud'e idon ki kalleni ba?" Turo baki tai tak'i magana ,bakin data turo yay wa kiss da ya kusa tafiya da numfashinta, lunshe ido yay yanajin wani mugun dad'i yana ziyartarsa yana d'aya daga cikin abinda yakeso a wajen hanna irin yaga tana turo baki ba karamin burge sa take ba ji yake kamar ya kama bakin ya tsotse ,
Hanna kuwa jikintane ya fara rawa bata ta6a tsintar kanta a irin wannan yanayin ba wani irin tsorone ya kamata shi kansa bayan ya aikata yaji wata yar kunya ta kamasa kauda kansa yay gefe yana sakin k'aramin murmushi ya shafa lallausan sumar kansa da tasha gyara ,idan yana gaban hanna sai yay namajin kokari yake control d'in kansa zameta yay daga jikinsa ya mike yace "tashi muje na rakaki toilet ki alwala" batasan sanda ta waro masa manyan idanunta da suke kyalli ba ,dama abinda yakeso kenan ta bud'e idon ya ganta lallausan murmushi ya saki itadai gaba d'aya mamaki haydar yake bata bata ta6a sanin haka yake ba ,hura mata iska yay ta kauda kai da sauri ta turo baki ,bakinsa yakai daidai kunnenta yace "idan kina turomin wannan bakin wataran saina cinyesa" da sauri ta juya kamar zata kifa ta shige toilet da gudu , kallan ta yake har saida ta rufe k'ofar sannan ya juya ya fice daga d'akin ya shige nasa bedroom d'in,
Ta dad'e sosai a toilet d'in dan har kunyar fitowa take , bud'e kofar tai ta dinga leka d'akin ganin baya ciki yasa ta fito da sauri ta dafe kirjinta da har yanzu yake bugawa gaba d'aya mamaki nema yake ya kasheta bata ta6a sanin bashida kunya ba sai yau ta runtse ido har yanzu inta tuno da kiss d'in da yay mata sai taji wani yarrr a jikinta ,jin ana neman bud'e kofa yasa ta kwanta da sauri ta kulle ido ta kama baccin karya,
Tunda ya shigo ya kula ba bacci takeba sbd yadda idanunta suke mar mar ga kuma lemar data jik'a eyelashes d'inta tana d'iga ,nad'e hannun jallabiyar jikinsa yay yana kallanta , hanna dama duk abinda yake tana kallansa ta gefen ido ganin inda take yake nufowa yasa ta mike zumbur tana zaro ido a waje, dakyar ya iya rik'e dariyar da take cinsa ya had'iyi abarsa yace "taho muyi sallah"
Hijab din daya fiddo mata tasa batai musu ba dan bataga alamar wasa a tattare dashi ba ,cikin nutsuwa da kwarewa ya jasu salla raka,a 2 ya dad'e yana zubo musu addu,o,i sannan ya dafa kanta yay mata addu,ar da manzo Allah (s.a.w) ya koyar ga masu sabon aure baiyi magana ba ya mike ya fice daga d'akin ta bisa da kallo ta gefen ido kafin ta d'auke kai tana niyyar mikewa ya dawo hannunsa rik'e da leda da plate da cups dai karamar knife,
A gabanta ya ajiye ya bud'e ledar ya ciro fresh milk d'in da ke ciki ya juye kazar da take ta tashin kamshi knife d'in yasa ya yanyankata ya cika cup d'in da fresh milk ,yanka d'aya ya d'akko yakai bakin hanna ta kauda fuska tana turo baki,
"Haaaa" yace mata a hankali, tak'i d'agowa ta kallesa sbd jinta take a mugun takure , "kinsan Allah in baki bud'e ba na matso zan miki d'ura" ya fad'i in serious tone ,kallansa tai idanunta sun cika da kwalla ganin ba alamar wasa yasa ta bud'e bakin cinya kawai taci tace ta koshi bai takura mata ba ya mika mata cup d'in daya cika da fresh milk batai musu ba ta kar6a ta shanye tass,
Mikewa tai kamar munafuka tana satan kallansa yanacin naman ta wuce kan bed tana niyyar kwanciya taji yace "A haka zaki kwanta"
Harararsa tai ta gefen ido ta turo baki tace "toh ka koma d'akinka mana"
"Kinsan Allah in baki canza kayan jikinkiba na taso sai kin yabawa aya zak'inta" ya sake ce mata fuska ba walwala ,kuka ta fashe dashi a shagwa6e tace "nidai Allah ka tashi ka tafi tayaya zan canza kaya a gabanka, nidai an hanani cire ko mayafine a gaban wani" jinjina kai yay baice komai yaci gaba dacin namansa hankali kwance ,tana ganin ya mike ta kwasa da gudu ta shige toilet,girgiza kai yay ya kwashe plate da cup d'in da sauran naman ya fice daga d'akin,tanajin karar rufe k'ofar ta fito da sauri ta bud'e wardrobe d'inta ,inda aka jera mata kayan bacci ta duba ta d'akko riga da wando pink clour masu kauri tasa ta haye kan gadon ta rufe ido,
A tsorace take dan baccinma kasa d'aukarta yay tun tana tunanin zai shigo harta fidda rai batasan sanda bacci ya d'auketaba, a hankali ya turo k'ofar ta yanda baza,aji k'araba yana hangota daga inda yake tsaye tana baccinta cikin kwanciyar hankali duk da lokaci zuwa lokaci yanajin tana sauke ajiyar zuciya, jingina yay, yay folding hannayensa yana Kare mata kallo yanajin wani zallan farin ciki da nishad'i yana shigarsa , dadduma ya kuma shimfid'awa ya fara nafilfilu na godiya ga Allah kusan karfe 2 na dare ya sallame ya ninke daddumar ya cire jallabiyar jikinsa kamar me tsoro haka ya nufi gadon yahau ya jima yana kallan kyakykyawar fuskarsa ya lumshe ido yakai bakinsa daidai goshinta ya sakar mata hot kiss yana kallo ta d'anyi juyi da sauri ya matsa har sai dayaga ta koma baccinta ,ya sake matsowa a hankali ya sata a kirjinsa har wata ajiyar zuciya ta musamman ya sauke fuskarsa d'auke da murmushi bacci me mugun dad'i ya d'aukesu musamman haydar da har wasu mafarkai ya ringayi hakan yasa fuskarsa ta kasance a washe ,
*Asuba ta gari HH**#HH*
*#Hanna_haydar*
*#Oum Ramadan*

YOU ARE READING
Hannah
Historical FictionBincike a rayuwa wani abune da ALLAH ya hallata ku biyoni cikin wannan labarin na soyayya da kuma fadakarwa