*HANNA*.......💥
©Maryam Abdullahi(OumRamadan)
*50*
*THE END*Karfe 8:30 na safe haydar ya sakko hannunsa rike da briefcase, dayan hannun kuma yana rike da hanna ya zagaye cikin , a nutse suke sakkowa bata yarda ta barshiba saida ta rakasa har bakin kofa ta dawo ,
Dakyar ta zauna tana yamutsa fuska , dan tun da asuba mararta ke murda mata d'aurewa kawai take sbd kar hankalin haydar ya tashi ,
Baba mairo ce ta fito daga dakinta da aka sauketa ta zauna kan carpet cikin nazarin hanna tace "Uwar dakina lfy kike kuwa? " Hanna ta sake yamutsa fuska tace "wllhy baba marata ke ciwo , amma ba wani abu bane dama na saba" baba ta girgiza kai tace "aa yar nan gwara muje asibiti a dubaki , gani nake kamar haihuwace"
Hanna tai wata dariya kana ganin dariyar kasan ta karfin halice tace" ba komai fa baba, kuma edd dinama bai cikaba " badan baba tasoba ta kyaleta saidai tana hankalce da duk wani motsinta ,
Tun Hanna na daure ciwo harta fara salallami sbd jin ciwon take yana gaba, durkushewa kasa tai sbd jin kugunta yay wani irin sarawa kamar zai balle , baba dama tun dazu ta kira mami da wayarta , kusan minti 30 mami da aunty suka iso lokacin tuni Hanna ta had'a Uwar zufa sai yarfe hannu take ,
A rikice mami ta kamota , tana ganinsu ta bude baki zata fara kuka aunty ta girgiza mata kai cike da tausayinta , aunty CE ta tuka motar mami da Hanna suna baya akabar baba mairo a gida,
Suna zuwa akai labour room da ita , haydar kuwa tunda ya isa office yakira Hanna as usual, saida yay mata few miss called bata dagaba , tuni hankalinsa ya tashi ya kira baba mairo , baba mairo ta sanar masa tuni an wuce da Hanna asibiti bai jira ta karasaba ya d'au mukullin motarsa ya wuce da sauri ,
Zaman jugum jugum akai a asibitin dan har sannan Hanna bata haihuwaba sai salati take , haydar yana bakin kofar idanunsa sun kad'a sunyi jajur , kana kallansa zakasan ba,a nutsuwarsa yake ba , abinci kuwa ba wanda ya kalla baran tana yabi ta Kansa,
Kimanin awa 5 Hanna ta d'auka tana labour kafin Allah ya sauketa lfy ta haifi sunkuceciyar babynta dake kama da babanta sak, sai hasken mamanta data dakko, tunda haydar ya rike Babyn bai saketaba sai kallanta yake yana zuba murmushi , dakyar Farouk ya karbi Babyn yana nunawa basma ita ,
Tuni haihuwar ta zaga family , da yake daga ita har babyn lfy suke awa biyu suka k'ara akai discharged dinsu, direct gida aka wuce , tuni mami ta sille katuwar jajiriyar baba mairo ta gasawa hanna jiki da ruwan zafi ,
Haka yan uwa da abokan arziki suka dinga tururuwa zuwa barka , a haka har ranar suna ta zagayo inda baby taci sunan mami za,a ringa kiranta da *hanan*,
Mejego Hanna da babynta hanan da uban gayyar haydar sunyi mugun kyau na fitar hankali, kudi sosai haydar ya fitar yaywa baby hanan da Hanna siyayya sosai ,
Haka mami ba karamin kudi ta kashewa Hanna da takwarartaba , aunty da bassam mus,ab farouk da basma ba ko wanne ya taka rawar gani,
Daddy ko kyautar wani dankareran gida yaywa sabuwar amaryarsa kuma jika ta farko a wajensa , mutan Lagos ma sunzo suma sosai suka taka rawar gani abindai sai sam barka ,
A gurguje hilis😎
3yrs ltr
Cike gidan yake da jama,a , ta ko ina ka hango gilmawar mutanene a makeken compound din gidan , gefe ga masu kid'an kwaryanan sai wasa manyan mata suke ana cashewa , bikin mus,ab da bassam ake , mus,ab wata yar kawar mami ya aura yayinda bassam ya auri yar cousin dinsu aunty ,
Shagali sosai akai a bikin kafin dare tuni mutane sun kama gabansu wasu sun tafi dakko amarya sai yan uwa na nesa da zasu sake kwana .
Hannace ta fito zata apartment din mami , hannunta rike da hanan da take ta zuba mata shagwaba , jin wayarta na ringing ta fiddota daga cikin jaka , sallama tai daga can bangaren haydar ya langwabe murya yace "sweet aji dani pls , tunda aka fara bikinnan bakida lokacina ko?"
Kamar zatai kuka tace " wllh habibi wannan hanan din CE duk ta dameni ,taki yarda ta zauna wajen kowa " murmushi yay yace "oh sorry sweet munyi laifi ba,amu sake ba, amma ki rarrasheta mana sweet ta daina rigima kinji" ya karasa shima a shagwabe , murmushi tai tace "Allah baby duk kai hanan ta gado , kaimafa shagwababbene Allah" murmushi shima yay yace "duk shagwabarmu batakai ta sweet ba , any way ki samu ki kaiwa mami ita ko taho parking space ina jiranki " daga haka ya kashe wayar ,
Wayar tabi da kallo tana murmushi can ta kalli hanan data tsura mata manyan idanunta cikin shagwaba tace "Ammina" Hanna tace "yes my dear hanan " murmushi hanan tai nan kumatunta suka lotsa tace "nidai wajen abeiy zani" hanna tace "abiey yace ki zauna wajen mami yanzu zamuje mu dawo ko dear" bata jira cewartaba ta shige parloun mami , can bedroom ta sameta itada kawayenta , kwace hannunta hanan tai ta tafi wajen mami da gudu ta dane cinyarta , Hanna ta tabe baki tace "dama wajenta zan kawoki ai , bakina ya huta na kwana biyu" dariya mutanan dakin sukai mami tace " itama ta huta da fadanki Hanna , sai kace bake tayo ba " murmushi Hanna tai tace "wlh dan bakisan hanan bane , dama yaya yace gobe zai taho mata da kayanta ta kana biyu mu samu mu huta da bari bari" mami ta tabe baki tana shafa bayan hanan data lafe a jikinta tace "kudai kuka sani ba ruwana , hanan kuma a kawomin kayanta kaff in rike abata , ni bazan gaji da itaba bangaji da uwartaba lokacin datai tashenta baran tana ita dana fi so" Hanna ta hade rai tace "yanzu mami kinfi son hanan a kaina" mami tace "kwarai wacece kuma Hanna?" Juyawa tai ta fice daga bedroom din kamar zatai kuka tanaji mami na kiranta tana dariya ta wuce,
A parking ta tadda haydar yana zaune a motarsa yabar murfin motar a bude, kai tsaye ta shiga tana kumbura fuska , kallanta yay yana hadiye dariyarsa ganin yadda take cika tana batsewa, shiru yay sbd yasan yan rigimar suna kusa, motar ya tayar ya fice daga gidan batare dayace komai ba Wanda hakan ya sake kular da Hanna,
Suna zuwa gida ta bude murfin mortar ta fice fuuu tana huci , ledojin da suka tsaya sukai take away ya kwaso ya shigo dasu ,
A parlour ya tadda ita ya ajiye ledojin ya wuce bedroom ta bisa da kallo ,
Bataji fitowartaba sai jitai an dagata sama ta juyo a firgice dan unexpected abun yazo mata, kukan da take dannewa ne ta rushe dashi kamar warce akaima wani abun, baibi ta kantaba ya wuce toilet da ita yana mata murmushi,
Kusan 40m suka d'auka suna wasa kafin su yo wankan tana makale a jikinsa tana zuba masa shagwaba , da Kansa ya shiryata cikin wasu tattausan sleeping dress masu azabar kyau da d'aukar hankali , a kujera ya ajiyeta ya dauki ledojin daya shigo dasu ya wuce kitchen bai jimaba ya fito da plate din gasashshiyar kaza sai Kamshi take da cups ,
A jikinsa ya zaunar da ita ya ringa bata cike da so da kana itama tana bashi , saida suka koshi tass sannan ya d'agata sama yace "sweet zo muje master bedroom na baki wani sako" make kafad'a tai tana turo baki tace "naki wakon" yana murmushi yace "pls mana my sweet dina ,vitamin abcdef,,z fa zan baki duk ke kadai" dariya ta fashe da ita tace "toh babyna , amma meye master bedroom?" Kallanta yay take moment din daya wuce 3yr back ya tuno , wani lallausan murmushi ya saki ya langwabar da kai yace "kinaso kisan master bedroom?" Ta daga kai a hankali yace "toh zo muje in nuna miki shi ,in kuma baki vitamin din da ake bayarwa acan" a tare suka kyalkyale da dariya cikin tsananin so yace "I love u Hanna ,I love u so much sweet wife ," kiss ta manna masa a cikin son mijinta tace " I love u too my sweet yayana, ina alfahari kasancewarka mijina, ina kuma rokon Allah ya barmu tare ya had'amu a aljanna baki d'aya" can kasan ransa ya amsa da amin kafin ya wuce da ita master bedroom idanunsu sarke cikin na juna suna aikawa juna sako.*Alhamdulilah nan na kawo karshen wannan buk din mai suna Hanna , kuskuran danai Allah ya yafemin , ina kuma godiya da jiran da kukaiwa wannan buk din bakuyi fushiba ngd ngd sosai*
Jinjina ga duk daukacin groups din da nake ciki harma da Wanda bana ciki masu bibiyar wannan buk din Allah ya hadamu
Sai mun hadu a buk na gaba Wanda bazan fara post dinsaba harsaina kusa kammalawa ma,assalam.08107942566 gamaison document a satinnan za,a had'a insha Allah ngd
*Maryam Abdullahi OumRamadan*

KAMU SEDANG MEMBACA
Hannah
Fiksi SejarahBincike a rayuwa wani abune da ALLAH ya hallata ku biyoni cikin wannan labarin na soyayya da kuma fadakarwa