Hannah part 24

364 37 6
                                    

💥 *Hannah* 💥
*Romantic love story*
        2️⃣4️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

Tana part d'in Mami sai zurga zurga suke ita da mami suna shirya lafiyayyan abinci a d/table  ,duk abinda suke haydar yana zaune akan Kujerar parlourn yana kallansu ya gefen ido ,
  Tsaf suka kammala shirya komai mami ta kalli Hanna tace "dota maza jeki shirya kafin in-law d'in nawa yazo ya same ki haka" murmushi tai tace "toh Mami" juyawa tai ta wuce stairs zama Mami tai dayan Kujerar ta kalli haydar tace "saurayin hanna ne zaizo ya gaisheni yamakata ka tsaya ku gaisa " shiru yay yana kallan mami ya kasa cewa komai,mami tace "bakaji abinda nace bane" numfashi ya sauke ya d'aure fuska kamar bai ta6a dariyaba yace "yanzu Mami ni zan tsaya yazo mu gaisa bama shi yazo ya gaidani ba? Kawai mami dai so kuke ku siyamin raini " bud'e baki mami tai tana kallansa tace "toh kada Allah yasa ka tsaya gyambo " daga haka ta wuce ya bita da kallo tashi yay a hankali ya ringa daukar abincin Yana kaiwa motarsa sai da ya gama kwashewa tsaf sannan ya d'auki mukullin motar yay ficewarsa daga gidan fuska d'aure,
   Mami ce ta fara sakkowa sam  bata kula da dinning d'in ba sai da hanna ta sakko taci kwalliya da wani lace ruwan hanta an masa ado da baby clour tayi daurin Zahra buhari kana ganin tulin gashin da tai parking d'insa,mayafi da takalmi da jewelry duk baby clour ne fuskarta tasha simple make up tayi mugun kyau tamkar ka saceta jikinta yana fidda wani sansanyar kamshi,
  Ajiyar zuciya Mami ta sauke tana kallanta harta karaso tace "Masha Allah dotana badai kyauba " murmushi ta saki daya karawa fuskarta kyau tace "nagode mamina" wayar tace ta fara ringing ta saci kallan Mami suna had'a ido ta juya bayan tayi picking call d'in a hankali tace "toh ganinan"
Juyawa tai tace "Mami yace yana parking space" Mami tace "ohk jeki taho dashi toh" batace komai ba ta wuce a nutse take takawa kamar me tausayin kasa,
  Tun daga nesa ya zuba mata ido yana kallanta kamar zai cinyeta wani irin abu yakeji a ransa daya ke tunanin tsabar sha,awartane yake damunsa ,ajiyar zuciya ya sauke me karfi sanda ta k'araso inda yake yana jifanta da wani irin kallo ,
Sassayan murmushi ta sakar masa tana shirin magana ya katsewa cikin cool voice d'insa data Kara wani low yace "partner zaki kasheni da gayunki "turo baki tai tace "Inka mutu in zauna dawa " murmushi ya saki yace "gsky kina mugun sona" juyawa tai tace "kaifa?" Saida ya zagayo inda take yana kallan tsakiyar idanunta yace "abinda nakeji akanki bai fad'uwa partner" a tare sukai murmushi kafin su jera suna tafiya a nutse had'a ido sukai da farouk da yake tahowa kamar ya juya ganin sunzo daf da daf yasa ya cigaba da tafiyarsa,
Kallansa ta ringayi rabonta dashi harta manta ko magana tai masa ta WhatsApp taga ko budewa ma bayayi a hankali ta Kira sunansa ganin yana niyyar wucesu kallan mk tai tace "ga yayana ya farouk" hannu mk ya Mika Masa farouk ma ya Mika masa ba yabo ba fallasa suka gaisa bai kalli inda take ba yay wucewarsa,
  Cikin sanyin jiki suka karasa part din mamii ,cikin fara,a mami takewa mk barka da zuwa shi kuwa sai sunkuyar da Kai yake dakyar ya yadda yadda zauna akan Kujera yana sunkuyar da Kai, Mami tana murmushi ta kalli hanna tace "dota maza ki kaishi yaci abinci ko?" Mikewa tai tace "to " shidai mk sai wani sunkuyar da kai yake , tun kafin ta karasa dining din ta hangosa wayam ba warmers d'in da suka jera da kofuna na lemo gabanta ne yay wani irin fad'uwa da sauri ta juya ganin Mami tana niyyar wucewa a stairs ta tsaida ita tana kwalalo ido tace "Mami kece Kika kwashe kayan dining" Mami tace "wane kaya?"  Kamar zatai kuka tace "kayan abincin da muka jera a dinning babu su ko d'aya Mami" mamakine ya kusa kashe Mami ta leka dinning d'in,ido ta zaro ganinsa wayam ba alamar komai a kansa sai adon da yake kai na wani golden din fulawa me d'auke da cup 6,
Rike Kai mami tai cikin bacin rai ta kasa magana cike da takaici ta kalli hanna da idonta ya kawo kwalla tace "jeki kitchen akwai abin motsa baki ki kawo masa ki ajiye akan center table kinji ,zan Kuma dau matakin daya dace " juyawa hanna tai ta shirya Masa snacks din da mami take lokaci zuwa lokaci ta had'a Masa da hollandia gaba d'aya ranta a mugun bace take komai , 6ata rai tai ganin yaki cin komai sai kallanta da yake kamar zai cinyeta d'anya cikin shagwa6a tace "sirrr" ya lumshe ido a hankali ya waresu shima cikin shagwa6a yace "ma,am" ,,,,,,"bakaci komai ba har yanzu" tace dashi tana sunkuyar da kanta dan gaba d'aya kallan da yake binta dashi sai ta ringajin wani iri, tagumi yay yace "toh ae bakison nacine" hararar wasa tamai tace "banaso kaci na kawo maka, nidai Allah kaci ko mu 6ata" ta k'arashe a shagwa6e,dan murmushi ya saki ya dakko cake ya nufi bakinta dashi , da sauri ta kauda kai tana yar dariya kad'an,yad'an 6ata fuska kad'an ya ajiye cake d'in, turo baki tai ta d'auka cikin tsananin kunya ta nufi bakinsa dashi ,
  Yana kallan tsakiyar idanunta ya kar6i cake d'in,a hankali yake taunawa harya cinye da wayo mk Saida yasa hanna ta bashi snacks yaci sosai duk yadda yaso ta kar6a kasawa tai sbd kallan da yake mata ya hanata sakewa duk ta tuno an kwashe wahalar datai ta 6ata lokaci tana shirya lunch ranta mugun 6aci yake,
Har suka rabu bata huceba sai bayan tafiyarsa ta zauna taci kukan takaici Mami ta rarrasheta ita kanta cikin bacin rai take,
  Bai yarda ya dawo gidan ba sai lokacin daya tabbatar Mami tana parlourn big daddy, warmers din da cups din ya ajiye a kitchen ya shige d'akinsa  bayan ya murza mukulli,
Kallan flask d'in da haydar ya ajiye mami ta ringayi duk da dama shi take zargi amma saida tai mamaki kwafa ta saki ta bud'e duk flasks d'in taga ba komai an cinye duk abincin sai dan burbushinsa kwafa ta saki ta wankesu tass ta goge ta rufe kitchen d'in,d'akinsa ta wuce ta kwankwasa kusan sau 4 sannan ya bud'e ,
Fuska d'aure ta shige bedroom d'in tana watsa masa harara zama tai akan sofa yayi yay kamar baiga harar da take Masa ba yace "Mami lafiya da darennan?" Takaici ya kuma kama mami cikin bacin rai tace "wlhy haydar ka fita idona in rufe waishin nidin sa,arkacene?" Murmushi ya saki yana shafa lallausan sajensa dayasha gyara yace "haba mamina waye ya ta6amin ke a darennan ya fuskanci 6acin raina, fad'amin ko waye mamii banason ganin ranki a 6ace ko kad'an" mami ta kasa magana ta saki baki tana kallan haydar girgiza kai tai tace "Allah ya shiryaka haydar ,yanzu abinda kaimin ka kyauta kenan, sirik,,,," bata karasaba ya rufe mata baki yace "wai Mami sai ayta magana guda kaina ciwo yake mami ina bukatar bacci" ta dad'e tana kallansa ta kasa cewa komai harara ta galla  masa ta fice daga bedroom d'in da kallo ya bita yana wani murmushi dashi kad'ai yasan na,anarsa.

HannahWhere stories live. Discover now