Hannah part 36

540 43 9
                                        

💥 *Hannah*💥
*Romantic love story*
        3️⃣6️⃣

*Maryam Abdullahi (Oumramadan)*




Hajiya bintace tsaye a bakin k'ofar Ward d'in da aka kwantar da siyama sai kanin siyama da shima yake zaune cike da damuwa duk sunyi jugum jugum kana kallan hajiya binta kasan taci kuka wayarta ta d'aga dake ringing takai kunnenta tai sallama,daga can bangaren abban siyama yace "hajiya ya jikin nata" ta sauke numfashi tace "toh da sauki gatacan kwance dr ya mata allurar bacci" abban siyama yace "ohk nima inanan tafe insha Allah nan da 2h jirginmu zai taso " 
"Toh Allah ya kawoku lfy" daga haka ta katse wayar tana tsurawa siyama dake kwance ido ta goge idonta ta koma kan Kujera ta zauna,
  Tunda siyama ta farka take wani irin kuka me ta6a zuciya rarrashin duniya hajiya binta da Yan uwanta ba wanda basuyiwa siyama ba taki shiru ,a haka abbanta ya diro daga k'asar duk yadda yaso ya lallasheta kitai dama karshe burkice musu ta ringa kiran haydar tana zata mutu  a taimaketa ,saida Dr ya sake mata allurar bacci suka samu sauki,
  Kuka hajiya binta ta zauna ta dingayiwa Abba bayan likita ya gama musu bayanin jininta yahau sosai ga Kuma damuwa datai mata yawa , cikin kuka tace "yanzu alhaji haka zamubar yarinyar nan tana wahala kana gani fa irin halin da take ciki" huci abban siyama ya saki yace "toh me zamuyi mata hajiya , sai dai mu tayata da addu,a kawai "
  Hajiya binta ta katseshi da sauri tace "akwai mafita mana,ni zanje har gidan iyayan yaron na rokesu tunda dai ta nacewa yaron tun tanaban haushi ta dawo bani tausayi duk yadda nai na rabata shi tak'i, ina ganin kawai hakan ce mafita" wani kallo Abba yay mata yace "ban amince ba, ba Kuma zan amince ba ,idan ke bakida tunani ni inadashi   karna sake jin makamanciyar wannan maganar ni zan samowa mafita amma bazan wulakanta kaina da 'yata akan abinda take soba ,wannan ma darasine a gareta tasan ba komai kake kwallafa rai akan abu ka sameshi ba " mikewa yay ya fice daga ward d'in hajiya binta ta bisa da kallo ranta na tafarfasa amma tad'au alwashin daukar mataki dole sai taje gidan iyayansa ta rokesu arziki koba da sanin saba,
  Tana zaune a gaban mirror daga ita sai towel tana tsane gashin kanta kwata kwata bataji shigowar saba sai jin tai an dafa kafad'ar ta a tsorace ta juya idanunta suka sauka akan haydar da sauri ta juya sbd ganinsa datai dagashi sai single gaba d'aya taji ta kasa ci gaba da tsane kan da take,
  Towel d'in hannunta ya kar6e ya sunkuyo da kansa daidai kafad'ar ta yana kallan ta ta madubin duk da ta sunkuyar dakai sai dogon gashinta da yake gani, dan yatsansa yasa ya d'ago da fuskar ta runtse ido da karfi ya sumbaci kuncinta yace "shine kika gudu kika barni baki bari munyi tare ba ko" batasan sanda ta waro ido ba tace "me zamuyi tare" hararta yay yace "wanka Mana" hangame baki tai cikin su6utar baki tace "ta6 lallaima yaya k'atoto dakai saimu shiga wanka tare?" Ta ta6e baki tace "lallaima yaya ta inama hakan zai yuwu" kad'an ya rage baiyi dariyaba ganin yadda tai da fuska ji ,jitai kawai an d'agata sama ya nufi toilet da ita dukan bayansa ta fara a rikice tana "me haka yaya ba kyaufa " baibi ta kantaba har saida ya dangana ta da toilet sai ihun ya saketa take  towel d'in jikinta yake kokarin janyewa ta rik'e a rikice ta fashe da kuka tace "me haka Yaya" da karfi ya fizge towel d'in ta fasa ihu da gudu ta mak'alk'ale jikinsa tana fashewa da kuka,duk yadda yaso janyeta daga jikinsa kasa wa yay duk ta kanainayesa kamar zata tsaga jikinsa ta shige lokacin d'aya yaji nutsuwarsa tana neman barin jikinsa tana manne a jikinsa ya sakar musu shower me sanyi,
   Ajiyar zuciya ta sauke ta sake kamkame jikinsa dakyau a haka akai wankan idonta a rufe sai hawaye take still tana manne a jikinsa suka fito daga toilet d'in kai tsaye kan bed ya kwantar da ita yana kallan fuskarsa da muryarsa data fara canzawa yace "ki bud'e idonki ki kalleni" ta mak'e kafad'a tana turo baki cikin nutsuwa yakai bakinsa daidai kan nata wani irin sakonni masu wuyar fassara yake mata cikin nutsuwa da kwarewa mutsu mutsu ta fara gashi ya sakar mata nauyinsa sai idanu da take zarewa ,haydar kuwa tuni hankalinsa ya fara barin jikinsa a zafafe yake bin ko wane lungu da sako na jikinta yana sakar mata kiss masu matukar kashe jikin lafiyayyar mace ,duk da halin tsoron da take ciki hakan baisa ta kasa kar6an sakon saba tuni itama jikinta ya mutu ta kasa d'aga kai ta kallesa sai kuka da take da iya karfinta ,ganin yana neman wuce gona yasa ta fasa ihu da k'arfi sai sannan ya farajin kukan da take sama sama,
  Kwanciya ya sakeyi ya birkitota ta dawo samansa numfashinsu yana had'u waje d'aya hawayenta yana d'iga saman fuskar sa  bai samu damar rarrashintaba saida ya samu yar nutsuwa ,hannunsa yasa a hankali yana shafa bayanta slowly yana yawo da hannun a jikinta tun tana kuka k'asa k'asa har yaji tai shiru sai ajiyar zuciya da take saukewa daga karshe numfashinta ya ringaji kallan fuskarta yay yaga tai bacci guntun murmushi ya saki kamar wata kwai ya kwantar da ita yasa mata pillow a gefenta ya lullu6e ta da duvet ya shiga toilet yay wanka ya fito sanye da rigar wanka ya dad'e yana kallanta yana murmushi wani yanayi na farin ciki dabai ta6a jiba yana shigarsa fita yay ya shige nasa bedroom d'in ya shirya cikin wasu kananun kaya da sukai masa kyau sosai ,
  Baccin kusan 1h tai ta farka bakinta d'auke da salati mikewa tai ta janyo towel d'in da yake gefe ta d'aura tuno abinda ya faru yasa ta rintse ido cike da matsananciyar kunya mikewa tai a kasalance ta shige toilet, acan ma ba karamar kunya da haushi taji ba da tazo tsarki haka ta gama tsarkin tai wanka duk jikinta a sanyaye ta fito doguwar riga ta atamfa tasa dark blue da adon orange bata d'aura dankwalin ba ta yane kanta da wani siririn mayafi orange mai kawai ta shafa ta feshe jikinta da turaruka saida ta had'e girar sama data k'asa ta fito daga d'akin ,
   Bata sameshi a parlourn ba, a yan kwanakinnan datai ta fuskanci yafison zaman parlourn k'asa  ,kwanciya tai akan doguwar kujera ta rufe ido tana tuno abinda ya faru ita yanzu gani take da wani idon ma zata kallesa danta lura shi kwata kwata baimason kunya ba, jitai tanason waya da auntynta da mami harma da basma da fannah mikewa tai ta sauka downstairs fuska a had'e tai kicin kicin ,
  Samunsa tai yana aiki a loptop wayarsa na gefensa ta bayansa ta dinga bi cikin sand'a ta zura hannu zatad'au wayar caraf taji ya rik'e mata hannu, "me zakimin da wayata?" Ya tambayeta idanunsa still nakasan loptop d'in,cikin shagwa6a tace "nifa ba abunda zanyi da ita kawai aunty da mami zan kira" hannu ya sakar mata tad'au wayar ta harari bayansa ta wuce upstairs , dialling number aunty ta fara ringing 3 aunty ta d'aga cikin 'yar kunya da nauyi tai sallama dan duk ta d'auka haydar ne ,wani farin cikin hanna taji jin muryan aunty cikin rawar murya tace "aunty" sai sannan aunty ta saki jiki itama cike da farin ciki tace "autata" kuka hanna ta fashe dashi tace "nayi missing d'inki sosai aunty ji nake kamar nai tsuntsuwa nazo gida na ganku keda abba da ya Bassam" murmushi aunty ta saki tace "hoo autana yanzu fa kin girma kukan me Kuma kike" rufe fuska tai tace "Allah ni aunty har yanzu ban girmaba " dariya ta saki tace "to naji ina yayan naku"
  "Yana parlour"
Sun d'an Jima suna waya aunty tana mata nasiha da shawarwari a fakaice sannan sukai sallama ta kira abbanta basu jimaba ta kashe ta kira mami tana d'agawa ta fashe da kukan shagwa6a tace"Allah mami kin manta dani ko cigiyata bakiyi" murmushi mami tai tace "Ina cigiyarki mana dota,komai dai lfy ko?"  "Lfy Lau mami, yaushe zakizo" rik'e baki tai tana dariya tace "zuwa ,tom zanzo in kin kwantar da hankalinki"
Marairaice fuska tai tace "Allah mami na kwantar sosai ma kuma fa bama fad'a da Yaya yanzu" cikin jin dad'i tace "toh Allah yay muku albarka dota sai mun sake waya" daga haka sukai sallama ta kira basma bata same taba fannah ma wayarta switch off haushi taji tai cilli da wayar kan Kujera,
   Karfe 3 na yamma hajiya binta tai parking d'in motarta a harabar gidansu hanna kai tsaye wajen me gadi taje ta tambayeshi apartment d'insu haydar da kansa ya nuna mata tai masa godiya ta wuce duk da jin gwiwoyinta take a sage dakyar ta d'aga kafa ta kwankwasa k'ofar parlourn.

HannahWhere stories live. Discover now