💥 *Hannah*💥
*Romantic love story*
4️⃣0️⃣*Maryam Abdullahi (Oumramadan)*
*Afuwan ba editing kuma yau ba yawa inada uzurine*
Rumgume ta haydar yay ya kasa tsaida hawayen da suke zarya a fuskarsa ya kasa tantance hawayen dad'ine ko na tausayi, idanunsa a lumshe suke cikin wani daddad'an yanayin dabai ta6a ruskarsaba , murmushi ne me sanyi ya saki yana dad'a kamkameta a jikinsa tamkar wani zai k'wace masa ita wai yar yarinyar nan ce ta zautar dashi ta rabasa da nutsuwarsa ta wucin gadi,
Duk yadda yake tunanin hanna ta wuce wajen wata tsabtatacciyar kaunarta tana sake shiga lungu da sak'o na jikinsa ga jinsa yake sakayau har wata iska na shiga ta kowane kafa na gashin jikinsa,
Zafin da yaji yana ratsa jikinsa yasa ya sake ta da sauri yana salati, ganin yadda take rawar sanyi yasa ya mike da
sauri shi kansa jikinsa ya fara d'aukar d'umi ,komawa yay ya zauna sbd jirin da yakeji ga k'afafuwansa da suke rawa dakyar ya mik'e a daddafe ya shiga toilet ruwan zafi ya had'a ya fito ya d'auketa batada wani k'arfin yin musu sai idanunta data kauda danba karamin haushinsa take jiba ,
Wani marayan kuka me ta6a zuciya ta saki sanda tajita cikin ruwan zafi a rikice take kokarin mik'ewa ya riketa ji yake kamar ya saki kuka sbd tausayinta dakyar ya danneta tana kuka tana cizon hannunsa gashi muryar tata ba fita take ba ,
Bai yarda ya kyaletaba sbd yasan shine kad'ai gatan da zai iya mata saida ya canza mata sau 3 sannan ya barta cikin ruwan a lokacin ko kukan batayi sai ajiyar zuciya dan sosai ta farajin dad'in ruwan , mik'ewa yay ya koma bedroom d'in ya cire bedsheet d'in ya sake wani ya koma toilet d'in yasa a washing machine,
Kallanta yay cike da kauna da wani mugun tausayinta harta fara bacci cikin ruwan, dakyar ya samu tai wankan tsarki shima yay ya nad'ota a towel ya kwantar da ita kan bed ,
Cikin k'arfin hali ya fita parlour dan shima tuni zazza6i ya rufeshi bai jimaba ya dawo hannunsa rik'e da plet da cups akai ,zama yay ya ajiye akan drowan dake gefen gadon ya tallabota jikinsa cikin sanyin murya irin ta wanda ya fara jin jiki yace "baby tashi kisha magani" wata uwar harara ta zuba masa cikin dashashshiyar muryarta tace "bansha" ta koma zata kwanta ya rikota cikin rarrashi yace "sorry baby ,in kikasha zakiji dad'in jikinki kinji"
Shiru tai tak'i magana sai sheshsheka da take,dakyar ya samu tasha fresh milk d'in ya bata magani, sai da yaga ta koma bacci sannan ya sauke ajiyar zuciya shima yasha maganin kusa da ita ya kwanta ya tsurawa fuskarta ido a haka bacci ya d'aukeshi,
9am
Kukan tane ya farkar dashi daga baccin da yake me mugun dad'i baccin daya dad'e rabon da yay irinsa, da sauri ya mike yana lumshe ido a hankali yace "kukan me kike baby" lafiyayyar harara ta zabga masa data basa dariya ya daure ya had'iye kayarsa cikin masifa tace "tambayata ma kake" shiru yay ya langwa6ar dakai, ta rushe da matsanancin kuka tace "ae dama dole ka tambayeni ai kasan kalar muguntar da kamin ,jifa tun d'azu nakeso na tashi na kasa ashe duk yadda nake tunanin muguntarka kafi haka toh wlhy nima saina rama".
Dak'yar ya rik'e dariyar da take cinsa ya maida fuskarsa kalar tausayi yace "sorry lollipop zo muje na sake gasaki zakiji dad'in jikinki" ta sake zabga masa harara a fusace tace "eh tunda masara ce ni dole kace zaka gasani, tun yaushe ka gama k'onamin jiki " juyar da kansa yay ya janyota jikinsa ya kwantar da ita cikin rarrashi yace "sorry babyna zona duba kona ji miki ciwone" tak'i tanka masa sai harara da take kamar idonta zai fad'o , dakyar ta yadda ya duba ta ya girgiza kansa taji ciwo amma ba sosai ba , toilet ya shiga ya sake had'a mata ruwan zafi tana kwance ya d'agata ya kaita har toilet d'in ,
Shagwa6a da raki ba wanda baishaba a toilet d'in har shidai sai dai yace sorry dan yasan fiye da hakama zai gani,
Da kansa ya shiryata da kaya marasa nauyi for the first time daya shiga kitchen da kansa ya had'a mata breakfast tana zaune a parlour sai turo baki take a gabanta ya dire yana yarfe hannu yace "baby tashi kiyi breakfast" dakyar ta motsa tana yatsina fuska tace "me wannan d'in?"
Bud'e mata plate d'in yay taga soyayyan dankali ne sai kwai da tea ta sake yamutsa fuska a shagwa6e tace "nidai bashi nake sha,awaba" ajiyar zuciya ya sauke ya rik'e kugu yace "toh me kikeso"
"Farfesun kayan ciki nakeso sai kamin kunun couscous" zaro ido yay yace "me ? ni ban iya kunun couscous ba bari na kira mami tai miki" ta had'e girar sama data k'asa tace "nidai naka nakeso Allah" dafe kansa yay da hannu d'aya cikin rarrashi yace " baby kinsan ban iyaba wannan d'inma dak'yar nayi" kukan shagwa6a ta saki tace "nidai Allah shi nakeso kuma yanzu, kad'au wayarka mana kai searching zakaga yadda ake".
Girgiza kansa yay ya d'akko wayar kusan few minutes sannan ya kwashe plate d'in gabanta har ya wuce ya dawo ya d'akko cup d'in tea ya mika mata yace "toh ki d'aure kisha love tea d'inne kinji" saida taja wasu sakanni sannan ta kar6a tana yatsina fuska ya wuce kitchen d'in ta murguda baki tana murmushi a hankali take shan tea d'in tana yatsina fuska,
Kusan awa d'aya ya d'auka sannan ya fito duk yayi gumi ya ajiye cup d'in kunun daya dama mata sai farfesun da tace a gabanta yana sauke nishi yace "tashi kici baby" a shagwa6e tace " toh ka d'agani mana"
Zama yay ya d'agata har kan carpet ya zaunar da ita,kunun couscous d'in ta fara kur6a da sauri ta furzar dashi kamar zatai kuka tace "me haka yaya"
A rikice yace "me? zafi? badai kin k'one ba"
"Haba yaya kamar dai abincin marasa lfy bafa sugar a ciki kuma madara bata jiba" dafe kansa yay ya mik'e bai magana ba tabisa da kallo tana dariya k'asa k'asa,
Tsurfa kala kala hanna ta tsiro da ita ko abincin da mami ta kawo bata ciba sai tace nasa takeso ya girka mata, in yace bai iyaba tasa masa kuka harsai yay searching ya wuce kitchen yake samun salama, hakimar tana kwance a kan kujera tana kallansa yana kaucewa ta fashe da dariya.
Mk ne zaune a parlourn sa ,yay zurfi cikin tunanin mafita duk ya rame sbd tunanin hanna, baijin a ransa zai iya rabuwa da ita duk yadda yay k'okarin samo gidan da take ya kasa, babban farin cikinsa shine sanin inda haydar yake aiki yana jiran ranar da zai dawo office lallai sai ya gano inda hannarsa take,
Dogon tsakin da yaji an saki ya sashi waigawa firgigit irin na wanda yay nisa a tunani, hanny ce taci wasu matsatstsun kaya da sukai mugun fito da surar jikinta , kauda kansa yay yana had'e fuska shi kansa in yace bata had'uba yay karya ga matsananciyar sha,awar da take damunsa a kwanakinnan dan wani iskanci hanny ta tsiro dashi indai yana gida marabarta da tsirara kalilan ne hakan da take yana bala,in tayar masa da sha,awa girman kai ya hana ya nemeta.

YOU ARE READING
Hannah
Historical FictionBincike a rayuwa wani abune da ALLAH ya hallata ku biyoni cikin wannan labarin na soyayya da kuma fadakarwa