💥 *Hannah* 💥
*Romantic love story*
2️⃣5️⃣*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1Hanny tana daga nesa tana kallan mk da hanna da suke zaune akan wasu kujeru,ranta tafarsasa yake sbd bala,in kishi da bakin ciki cizon yatsa tai tana ganin ya wuce ta taho inda hanna take saida taga yayi nisa ta saki fuska ta k'araso kusa da hanna can kasa tai sallama,
Bata d'ago ba ta amsa ciki ciki itama hararar tsana hanny ta watsa mata ta zauna kusa da ita tace "matar yaya baki ganeni ba?" Sai sannan ta d'ago da kanta ta kalli hanny ta saki fuska kad'an tace "au kece sannu ykk" jinjina kai hanny tai tana mata murmushi tace "lfy lau matar yaya ina yayan nawa" murmushi kad'an tai batace komai ba dan haka kurum taji hanny bata kwanta mataba kodan yanayin shigar da take tana kulata ne kawai sbd tace sister mk ce ,hanny ta katse mata shirun da tai tace"matar yaya inataso in kawo miki ziyara abubuwa sunyi yawa amma insha Allah a satinnan zanzo mu gaisa"
"Allah sarki nagode" hanna tace ba yabo ba fallasa mikewa hanna tai tace "tom zan wuce lokacin shiga lecture yayi" itama mikewa hanny tai tace"toh baki bani address din naki ba" karanto mata tai hanny tace "Zaki ganni soon amma ki bani no dinki Koda ban ganeba saina kiraki"
Duk ta kagu ta tafi wayar hanny ta kar6a ta rubuta mata no din ta mika mata wayar, wani shegen murmushi hanny tabi hanna dashi bayan ta wuce saving numbern tai tana wata dariya tace "soon zaki ganni a gidanku a matsayin bakuwa bakuwar da bazaki ta6a mantawa da itaba" dariya ta sake saki ta wuce tana juya idanu,
Kwanci tashi asarar me rai kwanaki suna komawa watanni yayinda watanni suna komawa shekara kwanan bawa a kullum karewa yake ya Allah ka karbi ranmu muna muminai Allah ka karbi ranmu muna ambatonka Allah ka tsare mana imaninmu karka bamu ikon shagala da duniya,
A kwana a tashi biki yanata karatowa kwata kwata baifi wata d'aya da sati 1 ya rage ba, ta kowanne bangare shirye shirye ake ba kama hannun yaro , tsakanin basma da farouk sai gaisuwa ita tsabar kunyarsa takeji shi kuma inya had'u da ita duk saiya rasa mezai ce mata sai dai yayta kallanta a sace suna had'a ido yake wucewa ,
Bangaren fannah da Sameer kuwa ba laifi a hankali fannah takejan sameer duk da bai cika Zama a Kano ba duk Friday takan tura masa text na gaisuwa bata ta6a nuna masa tana sonsa muraran ba tun baya reply a hankali shima ya fara tura mata saiya zama kullum sai sunyi waya da juna duk da bai fito ya nuna mata zallar soba hankalinta ya kwanta koba komai tasan baya k'inta tasan akwai lokaci Wanda take fatan yanan zuwa nan gaba kad'an,
Dama tunda aka sa rana Mami tad'au dawainiyar gyara amare maganin sanyi take basu nasha dana zama ingantattu tuni ta hanasu amfani da ruwan sanyi hatta ruwan da zasu sha ta hanasu shan na sanyi,
Next week aka kawo lefen basma da fannah duk a bangaren big daddy aka saukesu a matsayinsa na babba,sosai yakejin dadin karramar da suke masa tukwici me tsoka ya bayar ,ba karamin kokari mazajen sukai ba kayane na kece raini aka zubawa ko wacce sai sam barka set 2 2 ko wacce akai mata ,
Ranar Friday daya kasance saura 3week biki Kuma a ranar ne za,a kawo kayan lefen Hanna, dama mami tunda taji matane zasu kawo ta shiga Shiri na musamman kayan snacks kala kala akai masu yawa sosai lemuka katan katan aka jibge ga Kuma girke girke lafiyayyu da akai tuni friends din Mami dana aunty suka halarta sunyi shiga ta wayayyun mata yan gayu ,dakakken lace Mami tasa daya amsa sunansa tasha gwal daga hannu har wuyanta da zobuna, guda mutanan dake parlourn suka saki sanda ta sakko suka shiga mata kikari da uwar amarya dan duk wanda yasan Mami yasan Hanna,
Murmushi kawai mami take a haka ta nemi waje ta zauna suna hira karfe 3: daidai motaci suka ringa shigowa , su takwas friends din hajiya sara aminanta suka sakko suna karewa gidan kallo ko wacce tayi shiga ta kece raini drivern da sukazo dasune suka ringa daukar akwatinan suna shiga dasu saida suka shida da akwatina set 3 masu azabar kyau da tsada suna tsaye aka gama shiga dasu sannan suma suka shiga,
Cikin aji da wayewa Mami da friends d'inta suke musu lale tuni kawayen hajiya sara suka saki fuska ganin irin shigar da sukai zama sukai aka shiga gaisawa ana raha a nutse ba hayaniya tuni aka gabatar musu da abin motsa baki, lafiyayyan girkin da akai musu aka gabatar musu dashi da yake duk wayayyune ba wani kauyanci sukaci abincin su Mami kwata kwata basu bud'e kayan lefen ba sai hira da ake ana ciye ciye , tukwici 200k Mami ta basu aka kwashi kayan da akai musu na snack da lemuka aka fitar musu dashi har parking space suka rakasu anata godiya Saida suka wuce sannan su Mami suka shiga duba kayan rike baki Mami tai ta kasa cewa komai sbd uban yawan kayan gasu masu mugun tsada da kyau set din gold 3 aka zuba da awarwaro hajiya sara tayi mugun kokari duk da dama ita akwai harkar manya tun suna kirga kaya har suka koma shiru sai dai gani kawai kawar auntyce ta rangada guda ta kalli Mami tace "gsky hajiya dotana tayi goshi tubarkalla ji lefe iya lefe" murmushi Mami tai tace "ae ta cancanci hakane hajiya bakiga Yar takiba son kowa kin Wanda ya rasa,ae kimarta takai haka wlhy" mum d'in fannah tace "gskyne Mami" cikin farin ciki akacigaba da ganin lefe tuni mutane suka fara zuwa ganin kwakwaf,
Gaba d'aya amaren Mami ta dawo dasu part dinta aka fara musu gyara na musamman, hajja yakura ce take musu gyaran jiki daki guda Mami ta ware musu a part d'inta gefe guda tana had'a musu da ingantattun hadin garirrika masu asalin kyau da inganci,
Biki yanata karatowa inkaga amaren dolane ka kara kallansu sbd kyau tun bama hanna ba da fatarta har wani sul6i take ko rike abu tai sai yayi kamshi duk inda ta dosa kafin ta karasa sai anji kamshinta shiyasa mami ta hanasu fita inba wani part d'inta,
Anata shirya yadda za,a gudanar da biki bangaren hajiya sara ma gagarumin biki take shiryawa na only son d'inta Shiri take bana wasa ba dinkuna kuwa tayi ba adadi,
Ranar Sunday daya kama saura sati 1 biki hanny ta shirya tsaff ita da kawarta guesthouse d'in mk ta nufa itada kawarta zeey dayake tanada key d'in gidan kai tsaye ta shige zama tai tana karkada k'afa ta fiddo da wayarta tai dialling number mk saida taimai Miss call 3 ana 4 ya d'auka cikin sanyin murya hanny tace "baby pls kazo ina gidanka akwai muhimmiyar maganar da zamuyi kafin na tafi" shiru yay baice komaiba ta sake kaskantar da murya kamar gaske tace "pls baby inaso mu had'u kafin na wuce karkace bazaka zoba"
"Ina Zaki?" Ya tambayeta,hararar wayar tai tace "maiduguri zani dangin momyna zanyi kamar 1m kafin na dawo shiyasa nakeso mu had'u " ajiyar zuciya mk ya sauke sosai yaji dadin tafiyar hanny sbd kwata kwata hankalinsa bai kwanta da itaba ji yake kamar zata kawo masa wani cikas da sauri yace "ohk ganinan" kashe wayar tai ta kwashe da wata dariya zeey na tayata wayarta ta Mika Mata tace "ki shiga wancan lungun daga sanda ya shigo zaki fara mana vedio har sai ya fita karki min kuskure ki 6atamin aiki fa" zeey tace "haba kawata bakida damuwa" tafawa sukai zeey ta wuce inda hanny ta nuna mata ta 6uya.

YOU ARE READING
Hannah
Historical FictionBincike a rayuwa wani abune da ALLAH ya hallata ku biyoni cikin wannan labarin na soyayya da kuma fadakarwa