2

68 9 3
                                    


"Kuzo nan" abinda Malam Kwatiri ya fada ke nan yayinda fitsari yabi ta ƙafan Jamila, karamar cikin su kenan
Aiko nan take Azıma Mara tsoron cikin su tayi gaba ta tsaya ƙeƙam kanta a sama
'Gani' shine abinda tace
Ai be jira ta cewar taba ya ɗaga katotuwar dorinar ya zabga mata nan take ta zube ƙasa tsabar zafi har idanunta kakkafewa suke.
Sauran kuwa ganin abinda ya faru a take tsoro ya tsarga musu duk da sunsha yin latti yana bugun su amma sun kasa sabawa, babu abinda suke sai roƙon Malam Kwatiri akan yayi musu rai amma ko gezau
A haka yabi kowannensu yai musu bulala takwas-takwas wai ahakan yaji tausayinsu da suka ce an hana su wucewa ne, Jamila ce aka mata biyar dashike dukkanin su suna aji na bakwai in kacire Jamilan da take aji biyar
Shigar su aji suka zauna a ƙasan tabarma domin malami har ya shiga aji an fara darasi,
Malam Bala shine yake ɗaukar su Yaren Hausa, ya kasance mutum ne guntu sosai sai dan karen tsarguwa, abinda be kai ya kawo ba zai maida shi serious gashi sai dogon baki da kananun ido
Yayi musu batu akan insha'i da aka gama darasi sai ya bada aikin aji.

Kasancewar da ba kamar yanzu bane da idan yaro zashi makaranta za'a zuba masa abinci a kwano, kaga ya tafi dashi yaci a break time, Yanzun kuma sai kuna da shi ne zaka ga mutum ya dan kai kayan makulashen sa yana ci yana wa mutane yanga, Hakan ta kasance kuwa Ana cikin aikin ajin wata yarinya mai suna Zaliha ta paki idon Hafsa sai ta watsa mata soɓo akan littafin ta ai kuwa aka fara faɗa,
'Menene yake faruwa hakane'? Malam Bala ya tambaya. Buɗan bakin Zaliha sai tace "Malam zagin ka takeyi wai kai guntu ne idan aka gwada tsayi zata iya finka, shi ne nace zan faɗa maka shine tace in na faɗa sai ta zubar min soɓo na shine fa ta ɗauka ina ja itama tana ja shine ya zube mata a takarda, toh sanin halin Hafsa da rashin kunya yasa Malam ya fusata ya sata zuba guiwoyinta a kasa, ranta a dagule tare da niyan kece raini in aka tashi take tunani har aka gama darasi Malam yafita.

Sun sake yin darrusa kusan uku kafin karfe sha biyu yayi dai dai da lokacin tashin su daga makaranta ai kuwa suna fita Hafsa ta cakumo wuyan Zaliha dambe ya kaure da kyar aka raba su
Hafsa bata wa kowa magana ba tayi tafiyar ta gida, ko babu komai dai ta rama.
Tun daga bakin layin su ta hango samarin layin su yan zaman kashe wando masu zaman majalisa suna tsallen kwado, bata kwashe da dariya ba sai da ta hango Ashiru(saurayin Azıma) yana yin nashi daban ga fadawa sun taru a gurin hannayensu da bulalai sai hura hanci suke,
Meye Hafsa zatayi in banda dariya, aiko suna haɗa ido da Ashiru ya wani duburburce ya rikice ma'ana baya son yan gidan su Azıma su ganshi a irin yanayin nan domin idan zaizo hira har wani extra mai yake shafawa a giran sa da saman ido wai shi a dole gayu yazo yana wani babban ƙarewa shi ala dole gaye.

A zuciyarta kuwa caa take Allah ya kawo Su Azıma suzo suga Ashirun da ake mata gori akan sa yana tsallen kwaɗo yana wani sussunne kai, Addu'ar ta bata karbu ba domin su Dije ko walankeluwa basu kusa ba, Shi kuwa baa zata yaji saukar bulala nan take ya ƙara himma,
Sai da aka musu lilis taga wata budurwa da baza ta wuce sa'arta ba ta fito daga lemar da aka kafa mata ta sha kayan sarauta kai kace Sarauniya ce, tukunna ta ɗaga hannu alamar ya isa
"An gaishe ki ranki ya dade Gimbiya tace abarku, talakawa asararru" abinda wani bafade ya faɗa kenan aka barsu ita kuwa budurwar ɗalewa kan dokin ta tayi suka yi gaba.
Sakar baki Hafsa tayi har taga wucewar su kamar haɗin baki sai gasu Azıma, Dije da Jamila sun karyo kwana.
Tana ganin Azıma ta kwashe da dariya sai da tayi mai isar ta sannan ta shige gida tare da cin karo da ledoji da robobi tsaki tayi ta nufa hanyar dakin su, sai ga Lawan shima ya fito daga nasu ɗakin dai dai shigowan su Jamila kenan

Azıma ce tace " nikam Lawan taron nan da hayaniya na menene?, mun dawo mu kaga samari sai jan jiki suke meye faru ne?
Lokacin da tagama tambayar sa lokacin su Kulu suka fito
"Wai ma yar waziri ce tazo wucewa da fadawanta shine jikinta ya bata kamar ana kallon ta aikuwa taga samari sun cika maƙil ana zaune a majalisa shine tace a hukunta mata ya'yan talakawa "Ya ƙara da faɗin " ai ni Allah ne yamin alam nashra tare pa muke zaune kamar an tsikare Ni na mike nayo gida fitowa ta zan koma kenan naga abinda yake faruwa shine na tambaya aka gayamin, kar ku so kuga Ashiru yana tsallen kwaɗo" ya ƙarashe maganarsa yana dariya
Meye Hafsa zatayi in banda dariya
Ahaka Lawan ya fice daga gidan a cewar sa zai tafi jaje ne

Malam Sule mai rini haifaffen garin Bauchi ne nan cikin unguwar Wunti in da a yanzu ma yana unguwar tare da iyalan sa, a lokacin Bauchi bata zama jiha ba amman babban birni ce kuma sarauta ita ce ake ji da ita a lokacin, da yake karatun boko ma bai iso ba yawancin mutane sunfi bada himma a makarantar allo ko kuma a kai yaro koyon sana'a zuwa garuruwa daban daban to hakan ce ta faru da Sule aka kai shi Almajiranta da yayanshi Musa da shike su uku aka haifa sai kanwarsu ƙarama Hansatu.
A haka suke Almajiranta har suka zama ƙolo har suka zo suka samu sana'a,
Musa shi sana'ar fata yakeyi, shi kuma da kyar ya samu aiki a fada a matsayin dogari haka dai rayuwa tayi ta tafiya har Musa yayi auren fari yaransu biyu Salisu da Ramatu sannan ya kuma neman wata a lokacin shi kuma Sule ya haɗu da Kulu har an saka rana anyi komai sai ga wata wai ita Lantana daga ƙasar Gombe.

Tana zuwa ta haƙiƙance akan cewa duk duniya babu wanda take so kamar Sule a haka aka haɗa auren kasancewar Lantana marainiya ce, lokacin ne Sule ya gane akan su mugayen ƙazamai ne yayi taƙaici da hakan matuƙa, bayan aure da shekara Kulu ta haifi Lawan sai bayan shekara biyu Lantana ta samu ciki itama kuma Kulun tana da çıkın lokacin domin lokacin har Kulu ta fara ma Lantana gorin rashin haihuwa
Sai da Lantana ta haifi Adamu da sati biyu Kulu ta haifi Garzali sai da suka sake shekara biyu kafin Kulu ta haifi Fati ita kuma Lantana ta haifi Halime.
Alokacin ne wataran Sule yaje fada ya gama aikinsa a hanyar sa na fita ne ya hango wata kyakkyawar yarinya bazata wuce shekara sha takwas ba. Jikinta kuma kayan bayi ne.

A zaune ya hango ta tayi tagumi nan take tausayin ta ya kama shi ya karasa gurin ta tare da yi mata sallama
Barkanki"
"Barka dai, ta ce
Meya sah meki
Kawai ta pashe da kuka

Shin wacece yarinyar?
Just follow me to find out

Vote and comment please 🙏
You can message me on Whatsapp through this number if you want me to add you to my group
09020588802

Yariman Hafsa.Where stories live. Discover now