5

48 6 0
                                    

A amalanke aka ɗauki Mama Zenabu aka kaita gida, Jamila kuwa ba abinda take sai kuka.

Suman mama Zenabu har biyu tana farfaɗo wa, daman ance uba da ɗa sai Allah, duba da yadda Hafsa ta cika rashin ji amma da shike ba tanan sai da yan gidan suka ji ajikin su, Bama wannan bane matsalar a'a ko Baba ya dawo bashi da ikon da zai ja da yan sarauta, kai ko fadawa ne bai isa ba ballantana ɗan Sarki, ɗan sarkin ma me jiran gado.
WAYE SHİ ai bai isa bama,
Da haka da suka ga ba sarki sai Allah kuma har kusan sati Uku abu shiru yasa suka dangana, suke addu'a kuma suna jiran dawowan Baban su ji yadda za'a yi.

___________
Fitar Samira keda wuya Sarauniya Kilishi ta kwashe da dariya, tare da tafa hannun ta sai ga bayin sun dawo kowa ya kama aikin gaban sa
A zuciyarta kuwa caa take " gwara ki aure san inyaso na haɗa dake, inci Ubanku tare akan abin da mahaifin ki waziri yaimin".
Ɗaga hannun ta tayi sama alamar su bata ɗaya daga cikin kayan itatuwan da take ci
Aiko nan take wannan tsohuwar baiwar ta mika mata inibi hannun ta na ƙyarma
Amsa tayi ta jefa a baki tana taunawa tare da yin wani mummunan murmushi
Kilishi kenan

Fitan Samira sashen Fulani ta wuce gurin Bilkisu
________

"Shamsu kana ɓata mun lokaci pa"
Hayatu ya pada yana sake haɗe rai
"Yi hakuri dan Allah nakusa fitowa"
Inji Shamsu yana dariya
Aiko sai gashi nan ya fito da shigansa na sarauta shi da Hayatun duk shiga iri ɗaya ce a jikin su
"Muje"
Nan suka kama tafiya, da ka gansu za kaga zahirin Kamar da suke da junansu, kamar sun da har ta ɓaci.
"Gaba salamun baya salamun
Yayan sarki jikokin sarki "duk inda suka taka za kaga ana ta musu ƙirari
Tafiya suke cikin ƙasaita dogarai na biye da su har suka ƙara sa sashen dan uwansu wanda shekaru biyu ne kadai tsakaninsu kasancewar Yarima Idriss ɗin ne babba.

Da shigar su sashen suka sami Sulaiman a zaune yana bubbude wani littafi yana dubawa
"Gafara dai Wazirin gobe"
Muryar shamsu ce ta ƙarade dakin
"A'a sannun ku da zuwa yan tangwaye"
İnji Suleiman ɗin
"Shekara biyu naga ka bamu da kake wani cewa "'ƴan'" 
Hayatun ya faɗa yana mai yatsina fuskar sa.
Ehhh ko minti biyu na baku ai na girme ku bare har shekara biyu'
Suleiman din ya fadi yana ɗaga girar sa ɗaya
" Wai ina İdi ne yana ɓata mana lokaci pa"
Shamsu ya faɗi
"Sau nawa zance maka bana son sunan nan meye wani 'Idi' 😏?.
Idriss ɗin ya fadi yana fitowa daga uwar ɗaka
Kwashe wa gaba ɗayan su suka yi da dariya
" Muje"
Suka haɗa baki a tare nan suka ƙara pashewa da dariyan banda Idriss

Shi Idriss indai yan uwansa ne yana son su shiyasa ma watarana sukan biyo musu shida Suleiman su tafi pada tare, saboda basu dauko halin uwarsu Kilishi bah.
Nan suka mike suka fara tafiya duk inda suka saka ƙafarsu sai kaga an durkusa ana kwasan gaisuwa ko kuma ana musu ƙirari
Su Suleiman ne ma masu ɗaga hannun su alamun sun amsa amma Yarima Idriss kam ko a kwalar rigan sa.

Sun ɗan yi tafiya sannan suka isa fada
Sai da aka sanar da Sarki isowar su tukun ya bada izinin su shigo

Shigar su suka zube a ƙasa suna kwasan gaisuwa a gurin Me martaba da Waziri.
Bayan kowa yayi shiru ne Waziri yake sake tunatar dasu gasan hawan da za'a yi a ƙarshen watan nan na Dhulhajji wanda ya kasance al'adar masarautar ne kowane karshen shekara suna gayyatar masarautu da dama, kuma suma wasu masarautun zasu iya gayyatar su domin yin gasa kala kala

"Yakamata ku zage dantse dukan ninku domin manyan masarautu tara muka gayyata kuma ko wane sarki zaizo ne da ɗansa da kuma mutanensa saboda haka nake jaddada muku da kar ku bamu kunya"
'Zaku iya tafiya'
Muryar waziri ne ta dakatar dasu daga tunanin da suka fada

Nan suka fito Shamsu da Hayatu suka bi hanyar su, suma Idriss da Suleiman suka bi nasu hanyan suna tafiya suna tattaunawa kan yanda abun zai kasance

Sun ɗan yi tafiya kadan sai ga wani bawa nan yazo ya durkusa a gaban su
"Me gida Suleiman Mama Zulaiha ke neman ka"
Bawan ya fada yana nan a durkushe a gun
"Muje ka rakani Idi Mama ke nema na" inji Suleiman ɗin yana kallon Yariman.
"A'a karka damu akwai inda zani nima" Yariman ya bashi amsa
Sai Suleiman ɗin ya wuce ya koma Gidan su shikuma Yarima ya fice a masarautar baki daya shi da wasu fadawa suna take mishi baya
Sallahn magrib da isha ma a waje yayi
Da shike a kan doki yake sai suka bi ta wani Unguwa, shi daman abinda yake fitar da shi a wannan lokacin shine idan ya gamu da  bata gari kama su yake sa ayi akai su fada a hora su

Muryan wani yaji yana fadawa abokin sa da suke hira tare cewar 'kaga wadancan maza biyun da yan mata ukun kaf unguwan nan babu wanda ya kai su rashin mutunci musamman mazan sukam nasu sai a hankali dan har kisa nake jin za su iyaa dan... '
Yarima be kaiga jin karashen zancen ba ya je shi daf da wadanda ake maganan nasu ilai kuwa yaga zahiri domin daya daga cikin su sai zage zage yake sauran kuma sai hure masa kai suke
Shine yama fadawan alamun su kama su.
Kama su keda wuya mutane suka fara cika wajen duk wanda yazo yaga waye ne se yaja bakin sa yayi shiru
Can zasu juya yaji wata murya me cike da fitsara tace
" Uban waye ya hana mutane wucewa"?
A lokacin sai ranshi ya baci
Yana juyawa yaga har wani bafade ya fara mazgar ta
Jin muryar shi kawai yayi yace
" Ku hada da ita"
Aiko nan take bafaden ya wurga ta cikin sauran lokacin gurin har ya fara cika, kowa ya shiga matsanancin tashin hankali da tsoro
Nan yasa aka hankado keyar su sai cikin Masarautar Bauchi
Wannan kenan
___________

'Zuuut' 'Zuuut' 'Zuuut'
Ƙara da zuugi da zafin wata arniyar dorina mai baki Ashirin da biyar ne ya farkar da ita daga baccin wahalan da ya same ta ga uban sanyi, ga sauro ga wani uban yunwan da yake damun ta kamar ana kwashe mata kayan cikin ta
ZZuuut'
Ta ƙyara wata uban ƙara, ai bata san sanda ta mike tsaye a gigice ba tana kallon wani wagajejen bafade wanda girman sa ya kai girman Wargaji.
A firgice ta tsaya kallon sa, jikin ta babu abinda yake sai rawa, ga wani uban hajijiya da ya fara kama ta tsabar yunwa dan rabon ta da abinci tun jiya da rana
"Ku biyo baya na"
Wannan mummunan bafaden da ya jibge su ya faɗa
Ai nan take suka fara binshi a baya sai yanzu ma ta lura da yan dakin duhun kasancewar cikin dakin a kwai duhu bata lura da su ba sai yanzu
Mata ne sunkai goma kuma duk zasu girme ta sai wata yarinya ce a cikin su da sai kallon ta take, yarinyar za tayi sa'ar ta
Bata lura da yarinyar ta karaso kusa da ita ba sai da taji ta tace 'sannunki'
Yauwa" kawai ta faɗa
Nan suka ci gaba da bin bayan fadawan daga sun ɗan tsaya sai a zuga musu BULALA
Zungura ƙeyar su akayi sai sashen bayi
Ɗakuna ne zasu yi guda ɗari biyu ko ma fiye da hakan
Kuma ko wane ɗaki mutum huɗu yake dauka
A bakin wani ɗaki bafaden ya tsaya yace mutum biyu su shiga
Nan take yarinyar dake bin Hafsah tayi wuff ta janyo hannun Hafsan suka shiga cikin dakin sauran kuma suka yi gaba
Shigan su cikin ɗakin suka kalli wasu yammatan sai dai waɗan nan za suyi shekaru ashirin ashirin

Kwano Hafsa ta hango ai batasan sanda tayi wufff tayi kan kwanon ba ɗayar yarinyar ma jona ta tayi suka kafa kai sai jibgan wata dankararriyar tuwo suke yi yan dakin kuma ido suka zuba musu. Sai da suka gama suka fara sauke numfashi
Sai yanzu ma suka lura da yanayin dakin
Dakin yana da filin sa kuma a siminte yake
Ko wannensu da katifarsa. Katifarda  da ita da babu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya
Yarinyar da suka shigo tare ne tace "sunana Murja"
Tun farkon saka ki a ido na naji kin kwanta mun rai sannun ki
Ke meye sunan ki?
"Hafsa"
Hafsa ta bata amsa
Sai yanzu ta lura da yarinyar sosai, tana da tsayi amma ba can can ba kuma bata da haske sosai
"Kema sannun ki "
'daga yau mun zama ƙawaye babu yaudara, babu cin amana.'
Murjan ta fada tana saka hannun ta cikin na Hafsa
Murmushi kawai Hafsan ta mata itama ta rike hannun Murjan sosai
"Toh ƴan ƙannen mu mu baza a tambaye mu sunayen mu bane bayan an gama cinye mana abinci?
Wata daga cikin ƴar ɗakin su biyun ta tambaya.
"Wayyoo kuyi hakuri gaba daya hankalin mu baya kan ku ne ga yunwa ayi mana afuwa "
Murjan ta bata amsa
"Ayyah babu damuwa sunana Shafa'atu ƙawata kuma Lantana"
Ta fada tana nuna ɗayar
"Yauwa yanzu tunda an kawo ku ɗakin ku ku yi sauri ku fita ku karbo kayan bayi kapın wadannan yahudawan masu jibga jibgan jikin suzo su jibge ku"
Ai nan take Murja ta mike tsaye sukayi hanyar waje tare da Hafsa

Nidai bazan gaji da cewa ayi mun voting, commenting da sharing bah!

Taku ce Fadrees

İnnalillahi wa inna ilayhirraji un
Kulli nafsin zaa ikatul maut
Kuji tsoron Allah ya ku mutane
Ku kauracewa saɓawa mahaliccin ku insha Allah zakuyi kyakkyawar ƙarshe Allah kasa mu cika da imani, kasa mu gama da duniya lahiya, kasa mu a Aljannatul Firdaus kaji ƙan musulmi Allah kasa ƙasar mu ta samu zaman lapiya
Ameen ya Allah

Fatima Idriss 🥀

Yariman Hafsa.Where stories live. Discover now