9

20 3 2
                                    

Not edited.

Dariyar mugunta me kama da abun tsoro Boka Kafoor ya saki
Halittar seda ta tsorata duk da kasancewar duk sanda ta ziyarce shi se ta iske hakan amma ta kasa sabawa da hakan
Sujjada ta masa na kusan minti biyu kapin tai kokarin dago da kanta ta dube shi, tunda take bata taɓa hada ido da shi ba, cabb to wane ita, ai idan ta haɗa ido dashi sede ta ganta a lahira
Shiru bokan yayi yana jiran abinda zata ce duk da ya ga hakan a cikin tunanin ta, shi dariya ma taurin kan Bil Adama suke basa, abinda ya hanata taje ta aikata saboda ta kasa jiran lokacin da yace ta jira
Duk da yasan mind din kowa a duniyar ko meye kake kitsawa a mind din ka ya sani saboda duk wadanda suke zuwa gurin sa yana karantar tunanin su a kallo ɗaya da yake musu.
Amma yapi san ka furta masa da kanka sbd hakan yapi bashi nishadi.

Ita kanta tasan Kuskure tayi shiyasa tazo ta bashi hakuri
Can dai tayi karfin halin cewar "Yakai wannan hatsabibin Boka, ina me neman gafara a gare ka, ka gafarta wa wannan baiwar taka, nasan na tafka kuskure amma bisa kaidin zuciya ta ne da ta kasa hakura, dan girman tsafinka kai mini gafara"
Dariya me kaman kukan zaki ya saki sannan yace "kije zakiga hukuncinki"
Ihu halittar ta saki tana kuka
Nan take ta ɓace ɓat

_____________

Tun da Asuba su Hafsa suka tashi, gabaki daya a tsorace take, amma se tayi kokarin ta danne hakan, Murja kuwa da ta fahimci hakan ta, ta tisa ta a gaba akan se ta gaya mata me take boye mata, abinda ta fada ya razana Murja dan har ta fita tsurewa, ko karban abincin safe basu tsaya yi ba suka wuce sashen Sarki, suka zauna, duk da kasancewa ko bude sashen ba'a yi ba, a tunanin su idan Yarima ya aika ba za'a same su a sashen su na bayi ba.
_____________

Da safe tayi kuwa, kamar karfe goma Yarima ya farka, se yaji kaman ba shine ba lapiya jiya ba, bama haka ba, ji yayi kamar be taba ma rashin lapiyan ba, gefen sa ya duba be ga Sulaiman ba se yayi tunanin ko yana cikin makewayi, bari ya jira sa ya fito shima ya shiga, ya kara kusan minti goma yaji shiru, nan ya mike ya tura kofar yaga ba kowa a ciki.

Tsaki yayi tuna ko sallama Sulaiman be masa ba yayi tafiyar sa, shigewa bandakin yayi, se lokacin tunanin abinda wannan baiwar tayi masa jiya da daddare ya fado masa, ransa a mugun bace ya wuce gun da aka hada masa ruwan wanka, a gaggauce ya fito, bafaden sa ya shirya sa, take yayi ma bafaden umarni akan yaje ya kira masa jakadiyar Sarki.

Tsakanin Sashen Mai Martaba da Yarima akwai tazara sosai, amma cikin kankanin lokaci Jakadiyar Sarki ta iso, a dakin shaqatawar ta jira, har ya fito a cikin takun sa me cike da ƙasaita, tana hango shi ta duka kasa tana me kwasan gaisuwa a gurin shi tare da yi masa kirari

"Gaisuwa nake dan zaki
Gaisuwa nake dan damisa
Gaba salamun baya salamun"

Daga mata hannu yayi, akan ya isa haka

"Ina so ki kirawo min baiwar da kika aiko jiya da daddare, yanzu yanzunnan".
Ai be kai ga gama maganar sa ba jakadiya ta fita ta saka wani bawa yaje ya kira mata su Hafsa da su Murja, ba'a jima ba se gasu nan, hantar cikin Hafsa duk ta kada, Murja kuwa kamar kace mata caaa ta saka gudu

Suna shigowa suka zube a kasa, suna masu kwasan gaisuwa, shikam Yarima Idriss kawai kallon Hafsa yake, yana jinjina taurin kai da rashin tsoron ta, amma bari ze koya mata hankali

Daga Hannu yayi se ga wani bakin basamuden bafade, dauke da dorina a hannun sa, nuni ya masa da su Hafsa, ai nan Murja ta kwanta flat a kasa tana roqon sa gafara, alama yayi ma dayan dogarin da ya matsar da Murjan, nan yayi abinda aka umarce sa, Hafsa kuwa bakin ta ya kara yaudaran ta, ta kasa bada hakuri, shi kuwa bafade abun nema ya samu

Ya hau jibgan ta, ba shi ya bari ba seda yaga ta suma, alama Yarima ya ma duk bayin gurin da suyi waje kowa ya fice hadda Murja da ta kusan shidewa saboda kukan ganin yadda aka gama dukan Hafsan

Se ya rage daga Jakadiya se amintaccen bawan Yariman, se kuma Hafsan da take kwance a kasa kamar wata gawa.

Budan bakin Yarima cewa yayi "wannan yarinyar ta dawo aiki nan daga yanzu"
"Godiya take ranka ya dade" fadin Jakadiya tana fita waje dan ta koma bakin aikin ta.

"Ka tabbata ta tashi ta fara aikin ta, sannan ka sallami duk masu yin aiki a nan".
Yana fadin haka yayi hanyar waje, shi kuma bafaden da sauri ya fada wa wani bawa sakon Yarima kapin yaje ya take masa baya

____________

Kilishi ce zaune akan gadon dakin ta, da ka ganta zaka san a firgice take, ita tsoron wannan hukuncin take, sannan kuma tana tsoron kar yaran ta su rasa wannan sarautar, amma zata je tayi yanka dan ta seta komi ya zamo daidai, sannan zata dauki fansa akan Waziri da Yarima, saboda kaf fadin masarautar nan sune masu shige mata hanci

Yanzu bari ta shirya taje ta gaida sarauniya babba, su tattauna akan gasar nan da za'a yi karshen makon nan

Da wannan tunanin ta mike tayi ma amintacciyar baiwar ta alama da ta shigo
____________

Saukan wani ruwa me uban sanyi taji a tsakar kanta
Ai a hargitse ta tashi zata sa gudu, nan ta hada ido da wannan basamuden, harara ya banka mata tare da fadin
"Kin dawo nan da aiki, daga yau har illa Masha Allah, kuskure kadan idan kika yi an bani umarnin in canza Miki kamanni"

Ita ba maganan da yake bane matsalan ta ma, ciwon da jikin ta yake shine matsalan ta, ta ya zata iya aiki fisabilillah tana jin jikin ta kamar ba nata ba, gaskiya da sakel, abun fa da kamar wuya, tukunna ma ina Murja?

"Ina Murja"? Tayi karfin halin tambayar sa
Kamar ba zai bata amsa ba, can dai yace "Wannan kuma ke ta shafa, kowa ya koma bakin aikin sa"

Mikewa tayi dakyar da kama bango, ta shiga kikkintsa gurin, can dai ta nemi guri ta zauna, yunwa yana ta nuqurqusar ta, kai inaa, da taga baza ta iya ba ta mike ta fara da shigewa can uwar dakan Yarima, ta fara dube dube ko Allah ze sa ta samu abinda zata sa a cikin ta, dan Allah ya gani baza ta iya aiki ba in bata ci wani abin ba, dan a yanda take jin jikin tan nan zata iya fadi ma.

Let's meet in the next Chappy
Don't forget to, vote, comment and share it pls.

@fadrees_20.

Yariman Hafsa.Where stories live. Discover now