4

51 7 2
                                    

"Na mutu na lalace"
Zaliha ne ke ta faɗin haka har suka ƙarasa shiga ofishin Malam Habun
"Kiyi min bayanin ME KE FARUWA tsakanin ki da Malam Kwatiri"
Malam Habu ne ya daka mata tsawa
"Wallahi Malam shine shine....
Shine meye Mallam Habu ya ƙara daka mata tsawa
'Shine kullum yake cewa zai bani kudi mu haɗu a lungun da ka gammu'
Salati Malam Habu ya sake yana tafa mai tafa hannayensa tsabar taƙaici
'Abunda dama kake yi kenan Malam Kwatiri?
Toh daga yau ka tattara naka ya naka na kore ka daga makarantar nan, ke kuma na dakatar dake daga zuwa har sai na neme ki'

Ai a take Mallam Kwatiri ya rikice ya fara sumbatu har da faɗin wai karya take amma a banza
Su Hafsa da suka koma gida sai nanata abun suke.
Sai bayan mako biyu Mallam Habu ya aika akan Zaliha ta dawo

Tafiyar Mallam Sule mai rini ya ƙara sa ma yaran gidan tabarbarewa a maimakon su nutsu.
Bayan watanni biyu su Hafsa suka kammala sakandare lokacin Malam Sule mai rini ya zo gida anan ne yace su kawo mazajen aure duba da yayyensu da suka riga da sukayi nasu auren
Hafsa rashin kunyar ta yayi tsananin da bata iya saurayi, sai Azıma ce da ta rabu da Ashiru akan bashi da sana'ar yi ne ta haɗu da wani kuma wai Saminu sai Dije da bata da tsayayyen arziki sai shegen ruwan ido, qazantar gidan su kuma sai abinda ya ƙaru
"Hafsa kizo kije gidan su ƙawarki Habiba ki karɓo mun saƙo a wurin Maman ta"
Inji Mama
Haba Mama wai Ni kullum ake aiki ba ga Jamila ba" tafada tana ƙunkuni
Ita dai bata kara cewa komi ba se ma fitan da tayi tana fadin
"Saura kuma ki dade"
Tazo fita daga zauren nasu ta haɗu da Sadiqu ai kuwa sai da ta dunde shi kafin ta wuce

Fitar ta be jima ba ta haɗu da Zaliha suka fara cacar baki daga nan suka kaure da dambe da kyar aka zo aka raba su
Daman yamma ne kuma kusan mangariba bata tafi aiken ba, sai a sannan ta kama hanya taje gidan su Habiban domin har angama Sallan mangariba, Sun ɗan taɓa hira kafin ta karbi sakon ta fito Habibah ma hijabi ta ɗakko zata rakata sun fito lokacin har Dare yayi, sun fara tafiya suka hango dandazon mutane an hana kowa wucewa
"Uban waye ya hana mutane wucewa"?
Sai a sannan ne tasan fadin wannan jimlar yasa ta tafka babban kuskure, kuskuren da yake hade da ƙaddarar rayuwar ta
Ashe Yarima ne yazo wucewa da fadawansa gefensu kaɗan kuma wasu mata ne guda uku da maza biyu dukkanin su babu mai aure a cikinsu
Wani bafade ne ya hankado ta ya fara lafta mata wani gabjejiyar bulala
" Ku haɗa da ita " abin da Yariman yace kenan kafin a hankada Hafsa cikin wadannan na gefen da ta gani da farko
Habiba kuma zuciyarta ba abinda yake sai bugawa
Dogarawanne suka hankada su suka fara tafiya sai a lokacin tsoro ya tsarga cikin zuciyar Hafsa amma being the Hafsat she is, se bata nuna hakan ba.
Sun dan yi tafiya me nisan gaske kafin su ka iso wani garin
Garin da aka masa lakabi da Masarautar Bauchi

____________
Wai ya Haryanzu Hafsa bata dawo bane "
Najiyo muryan Mama Zenabu na tambaya
Wasa wasa mangariba tayi suka ga shiru ai hankalin mama bai ƙara tashi ba sai da taga an ƙira isha'i amman shiru nan hankalin ta ya tashi suka fita ita da su Azıma da su Lawan gidan kuma yayi tsit kowa na jiran yaga ikon Allah, gidan su Habiba suka wuce suka ga suma hankalin su a tashe yake na ganin har yanzu shiru ba Habiba ba labarin ta daga rakiya.

Fita sukayi su ka bi sawun su tare da yan gidan su Habiban sun san daman ba lalle subi ta hanyar da Hafsan ta biyo da farko ba sbd normally haka suke idan aka aiki dayan su gidan dayan se subi ta dogon hanya dan su sami lokaci suna hira.Sun ɗan yi tafiya mai nisa kapin suka hango jama'a daga nesa,
Nan take suka karasa wurin, suna zuwa sukaga Habiba ne a durkushe a gurin tana kuka an zagaye ta ana bata hakuri
"Na shiga uku na lalace shikenan sun tafi da ita"
Abinda take ta fada kenan ai a take suka sandare a wurin
"Waye?" Lawan yayi karfin halin tambaya
"Hafsa, Yarima Idriss ne yasa fadawa suka tafi da ita?
Ta ƙarashe maganar tana kuka ai nan take Mama Zenabu ta faɗi sumammiya a gurin aka ciccibeta aka ɗaura ta akan amalanken da aka dakko daga gidan su Habiban sai gida.
Ana shigo da ita su Mama Lantana suka sha jinin jikinsu, su Jamila kam ba'a fadan irin tashin hankalin da suka shiga
Wannan kenan

____________
MASARAUTAR BAUCHİ
Masarauta ne da zamu iya alaƙanta shi da masarautun daa
Masarauta ne wanda yake da ginin siminti irin riqaqqun ginin nan na daa,wanda yake dauke da sashe daya kamar karamar gari Gabadaya.

Masarautar ya ƙayatu ta fannoni dabam dabam wanda idan nace zan misalta shi xan bata lokaci ne. Kudai kuyi imagining dinshi kawai.
Bayi, Kuyangu, Fadawa da dogarai ne ke ta zirya kowa yana yin abinda yake gaban sa
Da na shiga cikin masarautar a nan ne nagane cewa ba ƙaramar gari guda bace wannan masarautar

Bayi, Kuyangu, Fadawa da dogarai ne ke ta zirya kowa yana yin abinda yake gaban saDa na shiga cikin masarautar a nan ne nagane cewa ba ƙaramar gari guda bace wannan masarautar

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Wannan shi ne hoton masarautar Bauchi

Wata budurwa na hango tana tafiya cike da ƙasaita kamar baza ta taka ƙasa ba bayi na take mata baya
Daga nesa naso nagane fuskar ta sai Dana ƙara matsowa ne na gane ta sosai.
Wannan wanda Lawan yabada labarin tane, yar Waziri ce wanda ta hukunta su Ashiru
Wani ƙaton gida a cikin masarautar dama naga ta fito kuma yanzu naga tana nufan wanda yafi nasu komai da komai tsarin haɗuwa.
Kutsa kai tayi cikin gidan tana mai dakatawa itada da bayinta
Da gudu ɗaya daga cikin bayin ta ta nufa cikin ɗakin shakatawan ( zamu iya alaƙanta ɗakin da parlour kamar yanda mutanen yanzu suke cewa) dan neman mata iso.
An baki izinin shiga ranki shi daɗe
Baiwar ta da ta aika ne ta dawo ta fada mata sakon mai mallakin bangaren.

Shigar ta cikin tapkeken dakin shakatawan keda wuya naga ta zube ƙasa tana faman kwasan gaisuwa
Wata Hadaddiyar mata na kalla wanda a ƙalla ba zata wuce shekaru Arba'in da biyar ba ta ɗago kanta ta sauke idanunta akan wannan budurwa tana mai murmusawa

An gaishe ki Samira" wata dattijiyar mata a cikin bayin matar ta fada
Wani banzan kallon da wacce aka kira da Samiran ta mata ne yasa ta gane ashe tayi kuskure ba'a kiran ta Samira kai tsaye sai an hada da Gimbiya ( niko nace ji ƙarfin hali, babanki yana wazirin🤔).
"Ku bamu waje" inji matar
Nan take kowa ya watse da ɗai ɗai da ɗai ɗai
Dan Allah Umma ki taimaka kisa Yarima Idriss ya aure ni wallahi ina masa son da bazan iya misalta miki ba dan Allah Umma.
Dariyan manya tayi kan tace
"Baki da damuwa Samira indai Idriss ne kamar kin samu" ta ƙarashe maganar tare da jefa fresh tuffa a bakinta, kasancewar fruits ne kusan kala goma a cikin kwandan da ta dauka tuffan a ciki. Sarauniya Kilishi kenan mata ta biyu a gurin Mai martaba Sarki Alhaji Sulaimanu bin İdrissa

__________
Shigar su cikin masarautar ba'a wuce dasu ko ina ba sai wani ɗakin duhu sai da aka ci uban su da duka tukunna aka kyale su ko abincin dare ba'a ba su ba a cewar fadawan lokacin cin abincin dare ya wuce
Kwanciya tayi akan simintin dakin duhun sanyi na ratsa ta ga wani uban yunwa da yake damun ta ga uban sanyi
Alokacin ne ta tabbatar wa kanta wannan rana shine ranan ƙaddarar ta kuma haka zalika wannan dare shine daren ƙaddarar ta daren da a dalilin shi tasha wahala kuma a dalilin sa ta san cewa rashin kunya baida fa'ida kuma shine daren da yasa ta zubda hawaye kuma daren da yasa tayi dana sanin abinda tayi da farko
Da bata fada wannan jimlar ba da yanzu tana cikin yan uwanta duk da basa wani shiri
Da bata fada wannan jimlar ba da yanzu tana cikin gidan ubanta kuma akan gadon mahaifiyarta amma daman Hausawa sun ce 'baki shi ke yanka wuya'.
Hakika wannan dare shine KUNDIN ƘADDARAR ta.

Finally!!
Hh

Vote and comment please 🙏
Seee yahhh💓💓

Fadrees Bello che!.🤍

Yariman Hafsa.Where stories live. Discover now