8

29 4 0
                                    

Nan suka kwasa suka yi hanyar sashen, se da suka yi dan tafiya kapin su isa
Duk da a hakan ba wani nisa bane tsakanin sashen Fulanin dana Yariman.

Kwandon abincin kam akwai nauyi amma sanin ba yadda suka iya ya saka su kinkima suka kutsa cikin sashen yariman suka ajiye a harabar katoton dakin shaqatawarshi
Har za su juya Jakadiyar Sarki da basu san da zamanta ba ta tsayar da su
'Ku dauka kukai can cikin uwar dakan'
"Tohm ranki ya dade" suka hada baki gurin amsa mata suna dan rusunawa, nan jakadiyar Sarki ta zabga murmushi, aranta tana cewa "Kai gaskiya yaran nan akwai ladabi wlh"
Ita fa a Rayuwar ta tana so taga ana girmamata, Yes, ita ba yar sarauta bace face Jakadiyar Sarki shugabar Jakadiyoyin dukka jakadai mata na masarautar, itama idan hakane ai ta cancanci girmamawa. Haka ne ma Yakamata kam. Nan ta saki shu'umin murmushi mai ma'ana.

Su kuwa basu ma san tana yi ba sukayi shigewarsu ciki inda tun kafin su karasa suke jin hayaniyan muryan maza.
Knocking Murja tayi aka basu izinin shigowa suka shiga da sallama kansu a kasa

Shamsu ne ya tsaya kallan ikon Allah bama shi kadai ba dukkansu har shi uban gayyar, dan su duk a tunanin su Jakadiya ce zata shigo se suka ga akasin haka
Amma de basu ce komi ba.

Sauke Kwandon suka yi suna shirin fita Suleiman yace "kuyi serving dukkanin mu".
Tare suka rusuna suna fadin
"Angama ranka ya dade"

A take suka zuba musu abincin kowa kwanon sa daban daban sannan suka dora akan wani katon darduman cin abincin da suka dakko sa ita da Murja daga dakin shaqatawa suka kawo cikin dakin
Daganan suka shiga zuba ma kowa shayi
Idon Sulaiman da Hayatu ne ya fada akan Hafsa ko kyaftawa basa yi
Shi Suleiman yana yaba kyawun ta a ransa shi kuma Hayatu ban ma san me zance akan shi ba saboda kamar kallon kauna yake mata
"Ku muje mana"? Shamsu ne ya ankarar dasu Hayatu daga dogon tunanin da suka fada
Akan cewar su karasa kan darduman abincin

Hafsa kuwa nan take ran ta yayi fari, ganin sun sakko daga kan tumtum din da suke kai shi kuma Sulaiman ya taimaka ma Yarima saboda yanayin jikin sa.
Tuna abinda zata aikata ma Yarima yanzu ta huce haushin sa da take ji koda kadan ne ya saka ta sakin murmushin mugunta

Tana ganin Murja ta nupi dayan bangaren ta mika wa Yarima Shamsu da Hayatu kopin shayi, ta dauki kopi biyu itama na Yariman da Suleiman, a cikin kopi daya ta zambada yaji me uban yawa da gishiri da sugar
Ta mika wa Sulaiman kopi dayan mara borkonon a ciki shi ko se kallan ta yake shikuma Yarima ta mika masa nasa me borkonon hannunta har kyarma yake yi tsabar tasan abinda tayi ba daidai bane, amma se bata nuna ba hasalima kalar abin tausayi tayi
Nan Yarima Shamsu yace dasu "Zaku iya tafiya"
Nan kuwa suka yi waje Hafsa har tuntube take
Ai kuwa suka raka su da idanuwa musamman Sulaiman.

Sede kuma wani abun al'ajabin da ya faru bayan fitar su shine da Yarima ya kai kopin shayi bakinsa yaji wani zafi me matukar azaba ga manda me uban yawa ya ziyarce harshen sa a take besan sanda ya furzar dashi ba idanun sa ya firfito besan sanda yayi jifa da kofin ba
Shi tunda yake anya ya taba jin azaba irin wannan?
Shi daman haka yake shan shayi duk zafin sa kurba daya yake masa yasha rabi
Amma wannan shayin da ya sha ji yake kamar garwashin wuta aka daura masa akan harshen sa ta wani ɓangaren kuma kamar ruwan teku ya sha
Nan take suka mike dukkan su shi kuma a firgice ya fara nuna kyauren dakin yana sumbatu se fadi yake
"I sauri Shamsu ka kiramin bayin da suka fita yanzun nan".
Da haramar sa kuwa Yarima Shamsu yayi waje cikin dakin shaqatawar Yariman amma babu su babu alamun su, babu kuma Jakadiyar Sarki.
Nan yayi can waje harabar sashen still babu su babu alamun su sema Bilkisu da ya hango ita da Samira suna nufowa sashen Yariman.

Shi ko sai ya koma ya sanar dashi akan be gansu ba su kuma su Suleiman har lokacin tambayar sa suke akan meya faru.
Kapin yace komi suka ji Sallamar su Gimbiya Bilkisu da Samira
Suna shigowa Bilkisu ta fada kan sa tana fadin
"Madallah Yayana nayi matukar farin ciki da ganin ka haka, naje gidan su Samira ina haramar dawowa ake sanar dani rashin lafiyar ka shine hankalinmu ya tashi nida Samira muka taho pa" ta karashe tana kallon Samirar da ta shagala da kallon sa bata ma san wainar da ake toyawa ba.

Shi ko cewa yayi "dan Allah Ni ki sake ni Bilkisu ke bakya taba girma ne? Ko so kike ki karasa ni ne"?
Shamsu ne ya keçe da dariyar mugunta yana kallon Bilkisun tare da fadin
"Ai wallahi maganin ki, kina gani na kika shareni ki kayi gurinsa gashi nan ai, mutumin da ba'a masa gwanin ta"? Ya karashe yana mata dariya Ita kuwa ta tsaya tana hura hanci se kallon Hayatu take da Sulaiman amma basu ce mata komai ba, nan ta maida hankalinta kan Samira tare da bubbuga ta
Se a sannan Samira ta dawo hankalin ta, ta gaida su suka amsa baya ma Sulaiman da yake mata kallon mamaki na kallon Yariman da yaga tana yi, sam Samira baza ta taɓa canzawa ba

"Ya Yarima kai ka jefar da wannan kopin haka? Fadamin a garin yaya? Ko de Ya Shamsu ne ya ture maka ya fadi? Bilkisu ta sake tambayar Yarima Idriss
Se a sannan abinda ya wakana ya sake dawo masa, aransa yana tunanin gobe gobe in Allah ya yadda ze sa Jakadiyar Sarki ta nemo masa yarinyar ya hukunta ta, ze mata hukuncin da ko sunan sa aka kira nan gaba se ta suma, da wannan tunanin ya dubi Bilkisu yace mata
"Kinga ƙanwa ta nazo tashi tsaye kawai na ture a bisa kuskure ba Yarima Shamsu bane" ya fada yana kallon Shamsun da se harara yake ta aika mata ita kuwa tana mishi gwaliyo.
Bayan sun gama cin abincin yace su bashi wuri ya huta, badan komi ya fadi hakan ba se dan surutun da Bilkisu da shamsu suke yi ne, gabaki daya sun sa masa ciwon kai
Ya Ilahi
Bayan fitar su ne Sulaiman yake cemasa akan yau anan ze kwana gudun kar jikin sa ya kara tashi

Su Hafsa kuwa seda suka yi tafiya me nisa da zummar su wuce makarantar bayin se kuma suka canza shawarar wucewa dakin su kawai tunda lokaci yaja, kila ma suna zuwa su tarar an tashi.
Hafsa kuwa zuciyarta ba abinda take banda bugawa can kuma ta saki murmushin mugunta, Murja ce ta tambaye ta dalilin yin murmushin nata, can dai tayi niyyar fada mata se kuma ta fasa saboda tasan idan har Murja ta sani toh shikenan watan yin baccin ta ya kare a ranar.
Can sun kusa isa Bangaren bayin Murja take ce mata
"Ke baki ga yanda Megida Sulaiman yake kallon ki bane"? Nace kode kode??😆
"Uwar 'kode' ɗin" fadin Hafsa kenan tana sakin tsaki. Niko na zaare ido na
Murja kuwa me zata yi in ba dariya ba.
Suna isa suka cinye sauran tuwon da suka rage kowa yabi lapiyar gado
A gurin Hafsa kuwa ba haka bane dan bacci cewa yayi be san ta ba se tunanin wanne kalan hukuncin Yarima ze mata take, can taji Sallamar su Lantana, sun shigo suna ta mita akan wani bafade wai yana san Shafa'atu, abun de abun dariya amma haka Hafsa ta gimtse kanta
Bata san sanda barawon yazo ya sace ta ba.

_______________

BOKA KAFOOR ne zaune a cikin katoton kogon sa wanda tsabar duhu zaka dauka kamar a cikin kabari mutum yake, gaban sa wani katon abu ne kaman drum, sede wannan ba drum bane dan abin kamar kwalba haka yake, cikin abun kuwa wasu unimaginary abu ne a ciki kamar Mami Water se shawagi suke a cikin kwalbar

Tadi suke yi cikin nishadi shida aljanun sa masu yi masa aiki suna basa labarin wata baiwar Allah da ta gagare su amma sun yi maganin ta

Se gani yayi kasa yana girgiza bisa ga dukkan alamu wani ne daga cikin mabiyansa yake neman iso a gurin sa, nan wata halitta ta ɓaco cikin kogon cikin baƙaƙen kaya
Halittar dai gata nan kamar bil adama kamar kuma aljanun amma dai mace ce tabbas.
Shin wacece wannan halittar?🤔

Let's meet in the next Chappy
Fadrees Bello
Chat me on Whatsapp Via 09020588802

Yariman Hafsa.Where stories live. Discover now