PAGE 3

786 16 0
                                    

*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*ANYA BAIWA CE?*

             Na

*AMEERA ADAM*
          

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

FREE PAGE 3

       Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, " Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za'ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? "

      Boka ya ce, " Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan " ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa.

        Zanen  wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga ƙasan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu, ta farko ya fara nuna mata yace, " Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata, Ƴar Sarkin jinsin Fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa ce, tunda take bata taɓa taka doron ƙasa ba "

        Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faɗa, ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa, " Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat Ƴar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron ƙasa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru, acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf (A.S) ita kuma tunda ta ke bata taɓa nutsawa ƙarƙashin ƙasa ba a matsayinta na jinsin aljanu, kuma ita Kalimsiyat mace ce mara haƙuri mai faɗan gaske, kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci, kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne, sai dai banbancin nahiya da zamani.
     Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aƙarshen zamanin nan, sunanta Rayzuta ita ta haɗa dukkan abubuwan da waɗancen suke dashi harma da wanda suka rasa, ƴar baiwa ce me ɗauke da ɓoyayyun al'amura, ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba."

      Yana rufe baki cikin azarɓaɓi Fulani Maryama ta ce, " To itama ta ukun nasu Aljanar ce? kuma meye alaƙar su da junan su? Kuma meye alaƙarta da gidan masarautarmu? "

      " Maryama kenan azarɓaɓin me kike yi? Ai duk gaggauwar asara ta jira samu, kuma duk gaggawar unguwar zoma ta jira a haihu, mai kike ci ne na baka na zuba inkinyi haƙuri sannu-sannu bata hana zuwa sai dai adaɗe ba'a je ba "

     Murmushin tayi sannan ta bashi amsa da, " Hmmm Marduska ai Ranar biyan buƙata rai ba'a bakin komai yake ba, na ƙagu na ji matsayin Yarinyar da ka ce da kuma ya alaƙarsu ta ke? "

    Marduska ya cigaba da cewa, " Har zuwa wannan zancen da nake miki ruhin su  na nan ya wanzu a dora ƙasa, sai dai babu inda zasu ya da zango sai akan cikon ta ukunsu, kuma ba kowa bace cikon ta ukunsu sai Yarinyar da nace miki karki sakankance har ta shigo Masarautar ku, har yanxu mudubin tsafi na ya gagara gano mun mutum ce ko kuma itama tana cikin jinsin Aljan, sai dai bincike ya nuna akwai wani ɓoyayyen al'amar dake bibiyar jinin zuri'ar sarki Aminullahi "

       Damuwa ce ƙarara a fuskar Fulani Maryama ta kuma jefo masa tambaya, " Ita yarinyar ba dama ka nuna mun hoton fuskarta yanda zan gane kamaninta? "

     Mudubinsa ya janyo ya fara wasu surutai yana watsa masa wani ruwa mai yauƙi, wata irin ƙara suka ji ta tsagewar mudubin har sai da suka tsorata, cikin damuwa Bokan ya ce, " Gaskiya gaba ɗaya aikin da kika zo dashi akwai damuwa da tashin hankali, haka kawai banci nanin ba nanin zata ci ni, na dakata akan binciken Yarinyar nan saboda ceton rayuwa ta "

ANYA BAIWA CE?Όπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα