FREE PAGE 8

614 11 0
                                    

*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*ANYA BAIWA CE?*

             Na

*AMEERA ADAM*
          

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

   FREE PAGE 8

     Abu ce ta dafata ta ce, "Maryo lafiya kuwa" Maryo lumshe idanu tayi tana jin kanta yana daɗa sara mata ta ce. "Abu wallahi kaina ne yake juya mun ji nake juwa na ɗiba na" Inna Habi ta ce. Sannu Maryo kinji? Bayan shi ko wani abun yana damunki?" Uwar bayi cikin masifa ta ce. "Kai dallah kuyi ku ɗaga ƙafa sai tafe kuke kamar masu tausayin ƙasa haba, banda ma ku baƙin takawa ne kwa tsaya kuna mun tafiyar rangwaɗa wallahi sai kun fanshe wannan rangajin da aikin wahala" Gabaɗaya babu wanda ya kula ta har suka ƙarasa sashen bayi Uwar bayi na zuwa da ƙwalawa  Zainu kira da sauri ta fito cikin girmamawa ta ce. "Gani uwar bayi" a yatsine Uwar bayi ta ce. "Ga baƙin takawa ne ki kaisu ɗakinku" tana gama faɗar haka ta juya ta fice.

     Zainu ce ta musu jagora zuwa cikin ɗakinsu, a gajiye su Inna Habi suka zauna a fakaice suke bin cikin ɗakin da kallo, sauran bayin da ke sanye da kayan bayi sai binsu suke da kallo jin ance baƙin Mai Martaba ne, suna nan zaune Jakadiya ta shigo cikin gidan kamar wacce aka jefo haka  ta tsaya daga bakin ƙofar ɗakin tana binsu da kallo, Inna Habi ce ta russuna ta ce. "Ina wuni Inna" Jakadiya ya mutsa fuska tayi ta ce. "Kar dai kune baƙin takawa?" Murmushi Inna Habi tayi ta ce. "Eh mune" Jakadiya ta taɓe baki ta ce. "Ai naga alama to amma ba Inna sunana ba, ni da kika ganni Jakadiya ce babu wanda bai san matsayina ba a gidan na" Inna Habi ta gyaɗa cikin ladabi ta ce.  "Zamu kiyaye" Maryo tunda ta zaune ta dafe kanta sama-sama take jin maganganunsu kuma har zuwa wannan lokacin bata daina jin maganganun farkon shigowarta masarautar ba, Jakadiya ta gyara tsayiwa tana gyara ɗaurin zaninta ta ce. "Yaya sunanku kun zuba mun na mujiya sai kallona kuke" Inna Habi ta ce. "Ni sunana Habiba wannan kuma Zainabu Abu ga Maryo duka ƴaƴana ne" Jakadiya ta ce. "Yayi kyau zan wuce sai na ƙara zagayowa" Jakadiya na wuce Inna Habi tabi Jakadiya da kallo lokaci ɗaya suka haɗa ido da Abu, ita kuwa Maryo duk budurin da akeyi kanta na ƙasa saboda sarawar da yake mata. Inna Habi ce ta ce. "Maryo lafiya kuwa ko jikin ne?" Maryo ta ce. "Inna wallahi har yanzu kaina sarawa yake ga wata irin hayaniya da nake ji" Inna Habi ta ce. "Kinsan gidan sarakai na'a rabasu da jama'a dole kiji hayaniya" Maryo taja ta jingina da bango tana runtse idonta.

      Bayan kwana su Inna Habi na zaune Mai martba ya aika kiransu da a wannan ranar har sun fara sakin jikinsu da waɗanda suke kwana ɗaki ɗaya, sai dai alhinin rashin da sukayi da ƴan uwansu. Gabaɗaya suka ƙara gurin Mai Martaba a fada yana zaune da shi da Galadinma sai Waziri, Cikin girmamawa suka gaishe sa Sarki Aminullah bayan ya amsa ya ƙara da cewa. "Ya baƙunta" Inna Habi ta amsa da, "Alhamdulillah ranka shi daɗe" Sarki Aminullahi yace. "Masha Allah, maƙasudin kiranku na kira ku ne domin naji tarinku da ainihin garinku da inda zamu je mu sadu da ƴan uwanku, dan mu jajanta musu da rashi ƴan uwa su da sukayi" Inna Habi hawaye ta goge murya na rawa ta ce.

   "Allah ya taimake ka  a yanzu dai maganar da nake maka bani da kowa kaine uwata kaine ubana, Mutumin da ya rasu lokacin da kukayi hatsari Mahaifina ne" Inno ta tsagaita da maganar tana share ƙwallah ta ci gaba da cewa. "Mahaifina ne shi kaɗai ya rage mun kuma shima Allah ya karɓi rayuwarsa." Sarki Aminullah ya ce. "Baki da dangim mahaifi ko mahaifiya" Inna Habi ta ce. "Bansan dangin Mahaifi da mahaifiyata ba, sai dai wata rana Mahaifiyata kafin ta rasu ta taɓa bani labari cewar ita da Mahaifina ƴan ƙasar Agadaz ne wani daliline ya rabosu daga garin sakamakon rashin amincewa da Iyayensu sukayi da aurensu, tun da suka baro garinsu basu ƙara komawa ba wannan dalilin yasan nida ƴan uwana muka tashi bamusan kowa daga danginsu ba, na taɓa aure da ƴaƴa uku sai mijin ya rasu lokacin da ciwon baƙwan dauro yazo yarana suka kamu da ciwon ta sanadin haka na rasa ɗaya daga ciki, sai biyu ne Allah ya barmun su gasu nan har sun fara girma, dangin Mahaifinsu tun bayan rasuwarsa suka gujeni da yake fulanin tashi ne tun daga lokacin bamu ƙara sa kowanne daga cikinsu ba. Daga cikin waɗanda suka rasu akwai Mahaifina, Mahaifiya sai ƴan uwana guda biyu wannan shine tarihina." Cikin tausaya Sarki Aminullah yace. "Allah ya jiƙansu ya gafarta musu.'" Inna Habi ta ce. "Amin ya rabbi" Sarki ya ci gaba da cewa. "Zamu ci gaba da riƙe ku a ƙarƙashinmu Allah ya albarkaci rayuwarsu" Gabaɗaya suka amsa da Amin. Maryo tun da ta zauna take ƙurawa Sarki Aminullah ido har sai da shi kansa ya lura da irin kallon da Maryo take masa, mamaki ne ya kamashi saboda yasan duk cikin talakawa da fadawansa da sauran masu sarauta da suke ƙarƙashinsa basa iya haɗa ƙwayar idonsu da nashi, sai gashi ya haɗa idanu da Maryo yafi a irga amma ta kasa ɗauke ƙwayar idonta a kansa, Waziri da Galadima ba ƙaramin mamaki sukayi da ganin haka, har sai da Sarki Aminullah ya kalli Inna Habi yace. "Ya sunan yaran naki" Inna Habi ta ce. "Wannan Zainabu ce muna kiranta da Abu ita kuma wannan Maryama ce muna kiranta da Maryo" Inna Habi ta ƙarasa faɗa tana nuna Maryo da har lokacin ƙwayar idonta na kan Mai Martaba, Muryar Sarki Aminullah ce ta katseta ta sunyar da kai ƙasa taji yace. "Allah yayi musu albarka, zaku iya tafiya" Cikin ladabi suka russuna suna godiya gai Mai Martaba sanannan suka fice.

    Tun kafin su fice daga farfajiyar Sarki Aminullah Maryo ta tirje a gurin ta ce. "Inna wallahi nasan wannan Sarkin kuma ko jiya a tsakiyar dare sai da ya zo gurina yace inbishi mu tafi..." da sauri Inna Habi ta sa hannu ta toshewa Maryo baki tana waigawa gefe da gefe muryan cen ƙasa ta ce. "Ke Maryo ahir na ƙarajin makamanciyar wannan maganar sai ranki ya ɓaci, so kike wani yaji ya kai ƙararmu a koremu bayan Allah ya rufa mana asiri? Idan aka koremu ina muka kama ki rufa mana koda wasa karna ƙara jin  haka" A dai-dai wannan lolacin Fulani Maryama ta ƙaraso cikin soron da alama wucewa zata yi, binsu tayi da kallo daga ƙasa har sama har ta wuce su taga babu wanda ya tanka mata sai ma  binta suke yi da kallo. A wulaƙance Fulani Maryama ta dawo ta ce. "Ku ƴaƴan gidan uban waye, waye Ubanku a garin nan da me kuke taƙama da har zanzo wuce wa baku gaisheni ba"  da sauri Baiwar dake biye da ita a baya ta ce. "Ƙarya kuke ƴaƴan talakawa Fulani Maryama tafi ƙarfin wargi" Jiki na rawa Inna Habi da Abu suka tsugunna suka fara kwasar gaisuwa, Maryo ido ta ƙurawa Fulani Maryama babu ƙiftawa, a hankali Fulani Maryama ta fara takowa har gaban Maryo tana yi mata wani irin kallo mai wuyar fasaltuwa.

KUYI HAƘURI DA SHORT TYPING BANYI EDITING BA KUNSAN ƳAU WEEKEND OGA NA GIDA😉

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

ANYA BAIWA CE?Where stories live. Discover now