BONUS PAGE

1.2K 25 14
                                    

*ANYA BAIWA CE?*
     
    PAGE 19

                   BONUS✋🏻😂🤚🏻

    Kamar yadda Sarki Aminullah ya zubawa sabon Bawan nan ido haka shima ya zuba masa idanu yana yi yana zagaye kaskon wutar kamar yadda abokin takararsa yake yi, Zagaya wutar suka fara yi suna yi suna ɗiban yashin gurin suna murzawa a hannunsu da jikinsu, idanun jama'ar gurin gabaɗaya ya koma kansu dan ganin wanda zai fara tsokano wutar tunda ita kanta wutar ita kaɗai ma neman abokin lasarta take yi, Haro ne ya gyara tsayuwarsa ya damƙi ƙasa ya watsawa wutar aikuwa kamar wanda ya watsa mata Fetir haka ta kuma tashi sama tana cin bal bal bal kamar zata fara lasarsu tun basu basu taɓa ta ba.

  Daga Haro har Sabon Bawan ja sukayi da baya kowa na ayyana ta yadda zai fara ɓullowa lamarin wutar, saboda sihirinta ya wuce tunanin me tunani. Daga cen gefe Mai Martaba Aminullah ne ya yi murmushi yana kallan Aminansa biyu, Sarkin Adamawa Dr Musa Ɗan bahaushe ya kalli Amininsa yace. "Wa kake ganin zai iya cin wannan nasarar?" Sarki Aminullah ya yi murmushi yace. "Alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba. Dan nasan waye Haro ka ga kuwa ruwa ba sa'an kwando bane." Sarki Musa yace. "Amma ba'a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare" Sarki Aminullah ya yi wani irin murmushi sannan yace. "Duk faɗin gurin nan kana gani babu wanda ya yarda ya shiga gasa da Haro, saboda wanda ya taka wuta, idan ya ga toka sai ya yi nesa da ita. Su kansu sun waye Haro wancen yaron ma da alama baƙo ne dan na lura da yanayinsa." Sarkin Nupe Sarki Abdullahi murmushi shima ya yi yace. "Yanzu fa duk harsashe ne kawai muke yi amma tuni Ubangiji ya zaɓi me yin nasara." Gabaɗaya suka amsa masa sannan suka mayar da kallansu wajen su Haro.

    Kallan kallo aka shiga yi da tsakanin Haro da Sabon Bawan sannan Haro ya yi kukan kura ta nufi wutar gadan-gadan, shima daga ɓangarensa Sabon Bawan cikin ƙwarin gwiwa ya nufi gurin nan take suka fara artabu da wannan wutar dake cikin kasko, duk lokacin da jikin Haro dana Sabon bawan ya haɗu sai kaji ya bada wani irin sauti kamar haɗuwar takubban da ake tsaka da azababben yaƙi. Sannu a hankali rigunan jikinsu suka fara ƙonewa suna bajewa cikin toka ya zamana daga su sai wandunan ƙarfe. Al'amarin da ya ƙara jan hankulan al'ummar da ke gurin, kowa ya yi shiru banda sautin kokawarsu babu abinda yake tashi agurin. Wasan ne ya fara ɗaukan zafi saboda yadda wandunan jikinsu tuni suka amsa tayin turirin zafin da wutar take yi musu, ganin wankin hula na hiyyar kaisu dare yasa Haro ya ƙara bada azama wajen ganin ya juya akalar wutar zuwa ga wannan Sabon Bawa, kamar wacce ya sanar da ita  wutar haka ta juyar akalarta zuwa gareshi har ta fara ƙoƙarin kaishi ga halaka, ganin haka ba ƙaramin faranta ran mutanen da ke gurin ya yi ba saboda kowa fatansa bai wuce ace Haro ya yi nasara ba.

    Sabon Bawan na ganin haka ya miƙe a zabure yana motsa bakinsa nan take wutar ta juya ga Haro har ta kwantar shi ƙasa, miƙewa ya yi tsaye yana murmushin nasara sai dai babu walawala  a fuskokin mutanen da ke gurin, ganin wutar ta tasamma halaka Haro yasa ya ƙarasa gurin ya kashe ta a lokacin tuni Haro ya fita hayyacinsa.Daga cen gefe Sarkin ƙira ne ya fito yana tafi haɗe da girgiza gwangwani mai ɗaure da wuri a hannunsa, yana zuwa ya kama hannun Sabon Bawan ya ɗaga sama tare da ɗaura masa wata ƙatuwar laya a damtsen hannunsa. Amma wani abin mamaki yana ɗaura layar sai ta suɓuce ta faɗo ƙasa ya gwada haka ya fi a irga, gabaɗaya mutanen gurin ido suka zubo musu suna kallon abin da yake faruwa. Da sauri wasu manyan Bayi suka ɗauke Haro da yake cikin wani irin yanayi. Sarkin Maƙera ya kalli Sabon bawa da mamaki shima shi yake kallo yana yi masa shu'umin murmushi. Sabon Bawan ƙasa ya yi da murya yace. "Ni da kake gani nafi ƙarfin siddabarunku ya kama ni" yana gama faɗa zubawa layar ido nan take ta hau ƙuncewa da kanta sai ga wasu irin ƙananun allurai da karyayyun reza haɗe da wani irin rubutu a ciki. Mutanen da ke zagaye basu san me yake faruwa ba a tsammaninsu Sarkin Ƙira wani abu na girmamawa yake masa dan haka aka ga sun haɗa kai guri ɗaya. Sabon bawan ya kalli Sarkin Ƙira yace. "Idan zaka gina ramin mugunta gina shi gajere dan bakasan wanda zai faɗa ciki ba, daga yanzu idan zaka shuka mugunta kasan wanda zaka aikatawa." Kunya ce ta kama Sarƙin ƙira yana shirin tsugunnawa ya roƙeshi ya ruƙo hannunsa ɗaya yace. "Idan kayi haka sauran jama'a zasu fahimci halin da ake ciki gwara ma mu bar lamarin a tsakaninmu, amma da sharaɗi guda ɗaya" bakin Sarkin ƙira har rawa yake yace. "Me nene sharaɗin a yanzu na aikata maka" Murmushi Sabon Bawan ya yi ya huro iska akan tafin hannunsa nan take sai ga Sarƙin ƙira tsaye tare da Haro yana yi masa bayani kafin shigar su Haro da Sabon Bawan filin gasa.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 01, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ANYA BAIWA CE?Where stories live. Discover now